Sai anjima!
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Allah ya ba mu alherinsa - mu zama lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke wakana a Najeriya da sassan duniya a ranar 28/12/2025.
Ahmad Tijjani Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Allah ya ba mu alherinsa - mu zama lafiya.
Ƴansanda a Bangladesh sun yi zargin cewa wasu mutum biyu da ake zargi da kashe wani fitaccen shugaban ɗalibai a farkon watan nan, sun tsere zuwa Indiya.
Wasu mutane rufe da fuska sun harbi Sharif Osman Hadi a Dhaka, babban birnin ƙasar, inda daga bisani ya rasa ransa sakamakon raunuka da ya samu. Lamarin ya janyo kazamar zanga-zanga na tsawon kwanaki.
Wani babban jami'in ɗansanda ya ce waɗanda ake zargin sun tsallaka zuwa jihar Meghalaya na Indiya jim kaɗan bayan yin harbin.
Jami'an tsaron kan iyaka na Indiya sun kwatanta hakan a matsayin ƙarya ce kawai.
Dangantaka tsakanin Indiya da Bangladesh na ƙara tsami tun bayan da Firaministar ƙasar da aka tumɓuke Sheikh Hasina ta tsere zuwa Indiya a bara.
Dubban ƴan kabilar Alawi marasa rinjaye ne suka fito zanga-zanga a Siriya bayan kai musu harin bam.
Wani mai sa ido kan yaƙe-yaƙe, ya ce jami'an tsaro sun kashe mutum biyu yayin da suke ƙoƙarin tarwatsa zanga-zangar.
Hukumomi a Siriya sun ce sun daƙile lamarin, ba tare da amsa cewa sun buɗe wuta ba.
Harin na bam kwanaki biyu da suka wuce a Homs ya hallaka mutum takwas. Wannan ne hari na farko tun bayan tumɓuke gwamnatin Bashar al-Assad - wanda shi ma ɗan Alawi ne.
Hukumomi sun bayar da tabbacin cewa za a kare marasa rinjaye, sai dai mutane da dama na kaffa-kaffa da sabuwar gwamnatin ta Siriya.
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya bar Legas a yau Lahadi zuwa Turai don cigaba da hutunsa na karshen shekara.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban zai kuma kai ziyara a hukumance zuwa Abu Dhabi, babban birnin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Shugaban ƙasar ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ne ya gayyaci Tinubu domin halartar wani taro na mako ɗaya kan ɗorewar cigaba na 2026, wanda za a gudanar a farkon Janairun sabuwar shekara.
Kakakin na Tinubu ya ce taron na tsawon mako ɗaya an saba yin sa ne domin haɗa shugabannin gwamnati, ƴan kasuwa da kuma al'umma don tattaunawa a taron.
Sanarwar ta ce shugaban zai koma Najeriya bayan kammala taron.
Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa za ta taƙaita bayar da takardar izinin shiga ƙasarta - biza ga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo saboda kin yarda da ta yi da matakan karɓar bakin haure da kuma 'yan ƙasashen waje masu laifi.
Ma'aikatar harkokin cikn gida ta Birtaniya ta ce ta harzuka da ki da kuma jinkirin da ake samu na tattara sanya hannun mutane - wanda hakan wata hanya ce da ke hana fitar da su daga Birtaniyar.
Wasu ƙasashen biyu na Afirka da Birtaniyar ta yi musu irin wannan barazana - Angola da Namibia sun yarda su karɓi 'yan ƙasashensu.
Matakin ya biyo bayan shirin Birtaniya ne na rage baki da kuma fitar da mutanen da ba su da damar kasancewa a ƙasar.
Fitacciyyar tauraruwar fina-finai kuma mawaƙiya ƴar Faransa, Brigitte Bardot ta rasu, tana da shekara 91.
An haife ta ne a birnin Paris a shekara ta 1934, cikin iyali mai wadata.
Ta yi shahararrun fina-finai da dama waɗanda suka karaɗe sinimomi, ciki har da fim ɗin "And God Created Woman" a 1956, wanda mijinta ya rubuta sannan ya ba da umarni.
Daga baya a cikin rayuwarta, ta bar masana'antar fina-finai inda ta koma mai fafutukar kare hakkin dabbobi.
An kuma sha cin tararta saboda ingiza batun nuna wariyar launin fata.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya miƙa ta'aziyyar rasuwar tauraruwar, inda ya ce rashi na babbar jaruma.
Rundunar ƴansanda a jihar Zamfara ta ce ta daƙile wani yunkurin ƴanbindiga na kai hari a karamar hukumar Maru na jihar a safiyar yau Lahadi.
Wata sanarwa da kakakin ƴansandan jihar DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce sun samu nasarar daƙile yunkurin ne bayan samun bayanan sirri.
"Haɗakar jami'an tsaro ne da ya haɗa ƴansanda, sojoji, rundunar tsaro ta al'umma da kuma ƴan sa-kai suka fafata da maharan, abin da ya tilasta musu tserewa tare da raunuka. Babu wanda ya mutu ko kuma garkuwa da aka yi," in ji sanarwar ƴansandan.
Sai dai, an tsaurara matakan tsaro a karamar hukumar ta Maru da kuma yankuna da ke ƙewaye.
Kwamishinan ƴansandan jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba ya tabbatarwa al'umma cewa a shirye jami'an tsaro suke wajen kare rayuka da kuma dukiyoyinsu, inda ya buƙace su da su ci gaba da bai wa hukumomi haɗin kai.
Wata guguwa mai ƙarfin gaske ta hallaka wasu mutum biyu a Sweden, inda ta kuma janyo tsaiko wajen tafiye-tafiye da ɗaukewar lantarki.
Hukumar lura da yanayi ta ƙasar ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar samun iska mai ƙarfi a sassan arewacin ƙasar da dama yayin da guguwar mai suna Johannes ke ci gaba da ɓarna.
Wani mutum ɗan shekara 50 ya mutu bayan da itace ya faɗi a kansa a kudancin ƙasar, kamar yadda kafafen yaɗa labarai da kuma ƴansandan ƙasar suka ruwaito. Wani kamfani ma ya ce ma'aikacinsa ɗaya ya mutu a lamarin.
An samu ɗaukewar lantarki a dubun-dubatar gidaje a Sweden, Norway da kuma Finland.
A Sweden, sama da gidaje 40,000 ne lamarin na katsewar lantarki ya shafa sannan an dakatar da tafiye-tafiyen jiragen ƙasa, a cewar kamfanin dillancin labarai na Sweden TT.
Haka kuma, an soke tashin jiragen sama da jiragen ƙasa da kuma na ruwa a faɗin ƙasashen arewacin Turai.
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya nuna kaɗuwarsa kan wani hatsarin mota da ya lakume rayukan ƴan jihar bakwai waɗanda suka fito daga karamar hukumar Akko na jihar.
An ruwaito cewa mutanen na kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno lokacin da suka haɗu da ajalinsu.
Gwamna Inuwa Yahaya ya kwatanta hatsarin da mai ciwo da kuma raɗaɗi na rashin da aka yi, ba ga iyalan mutanen kaɗai ba har ma ga ɗaukacin al'ummar Lawanti a karamar hukumar Akko da kuma Gombe baki-ɗaya, kamar yadda sanarwar da darektan yaɗa labarai na gidan gwamnatin jihar, Ismaila Uba Misilli ya fitar ranar Asabar, ta bayyana.
Gwamnan ya ce rasuwar mutanen ya taɓa al'umma sosai, inda ya miƙa ta'azziyarsa ga iyalan mamatan, da kuma addu'ar Allah ya gafarta musu.
An fara kaɗa kuri'a a matakin farko na babban zaɓen ƙasar Myanmar - na farko tun bayan da sojoji suka karɓe mulki kusan shekara biyar da suka wuce.
Lamarin ya ƙara ta'azzara yaƙin basasar ƙasar mai muni.
Wakilin BBC ya ce yanayi ne na kamar ruwa ya ci mutum domin duk wanda ke zaɓe a nan ya san wannan ba wani abu da zai canza kan wanda ke mulkin ƙasar.
Za a yi zaɓen zagayen farko a kusan kashi ɗaya bisa huɗu na ƙasar , sannan kuma a yi wasu zagaye biyu a wata mai zuwa.
Gwamnatin sojin ta bayyana zaɓen a matsayin wata hanya ta mayar da ƙasar turbar zaman lafiya.
Amma masu suka sun bayyana zaɓen wanda aka tsaurara matakai, a matsayin - ungulu da kanzabo, wanda zai share wa sojojin hanyar kara dawwama a mulki da sunan farar hula.
Gwamnatin mulkin soji ta Nijar ta zartar da wata doka da ta ba ta ikon shigar da mutane aikin soji domin yaƙar ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi, da suka kame wasu sassan ƙasar.
Dokar ta kuma bai wa gwamnatin damar karɓe kaya ko wani aiki domin taimaka wa sojojin.
Nijar kamar makwabtanta Mali da Burkina faso na karkashin mulkin soji - ƙasashe uku da suka fice daga ƙungiyar ECOWAS suka kafa ta su ƙungiyar, amma har yanzu sun ƙasa shawo kan matsalar tsaronsu.
Dokar ta ce dole ne 'yan ƙasa su amsa kira da zarar an buƙace su su yi hakan domin kare ƙasarsu.
Ƙasar ta Nijar na fama da hare-hare na ƙungiyoyin da ke da alaƙa da al-Qaeda da IS shekara goma da suka wuce.
A Najeriya, ana can ana kokarin tantance irin ta'adin da fashewar wasu bamabamai biyu da aka dasa a kan hanyar Dansadau zuwa Gusau a jihar Zamfara, suka yi.
Bayanan da aka fara samu sun nuna cewa mutum goma sha daya suka rasu a fashewar, amma hukumomi sun ce yawan bai wuce mutum bakwai ba.
Ana dai zargin wannan wani salon harin ramuwar gayya ne 'yan bindiga suka kaddamar, game da kisan da 'yan sa-kai suka yi wa wasu 'yan bindiga da mukarrabansa a makon jiya a yankin.
Yanzu haka dai ana can cikin jimami da zaman jugum, da kuma dakon tantance matafiyan da ko dai suka jikkata ko ma suka rasu sakamakon fashewar
Latsa nan don karanta cikakken labarin....
Yawan mutanen da ake zartar wa da hukuncin kisa a Iran a shekarar nan na neman ninƙa yawan na bara har sau biyu.
Ƙungiyar rajin kare hakkin dan'adam ta Iran wadda ke da mazauni a Norway ta shaida wa BBC cewa ta tabbatar da ƙarin zartar da wannan haddi har 1,500 zuwa farkon watan nan na Disamba, inda aka zartar da wasu da dama tun ma kafin wannan lokacin.
A shekarar da ta gabata ta ce ta iya tantance zartar da haddin har 975.
Ana samun ƙaruwar waɗanda ake zartar wa hukuncin kisan tun bayan zanga-zangar gama-gari da aka yi a karshen 2022.
Kusan kashi 90 cikin ɗari na hukuncin kisan ko dai na kisan kai ne ko kuma laifi na miyagun ƙwayoyi.
Masu bibiyar BBC Hausa barkan mu da warhaka.
Ku kasance da mu a wannan shafi domin samun labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.