Shugabar ƙasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta fitar sa sababbin ministocin ƙasar, inda ta sanar da sanar da ƙirƙirar sabuwar ma'aikatar matasa, sannan ta ƙara yawan ma'aikatun ƙasar daga 26 zuwa 27 a sabuwar gwamnatin.
Daga cikin ministocin akwai sababbin fuskoki, da tsofaffin ƴan siyasar ƙasar, ciki har da tsofaffin ministoci bakwai, sannan ba ta mayar da tsohon mataimakin firaministan ƙasar kuma ministan makamashi, Dotto Biteko da tsohon shugaban majalisar ƙasar, Tulia Ackson ba.
Sai dai hankali ya fi komawa ne kan naɗa ƴar shugabar ƙasar, Wanu Hafidh a matsayin mataimakiyar ministar ilimi, sannan ta naɗa surikinta, Mohamed Mchegerwa a matsayin ministan lafiya a cikin sababbin ministocin.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugabar ƙasar ta kafa kwamitin bincike domin gano musabbin zanga-zangar bayan zaɓe da aka yi a ƙasar.
Jam'iyyun hamayya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun zargi jami'an tsaron ƙasar da kashe ɗaruruwan mutane, sannan suka ɓoye gawarwakinsu.
Sai dai har zuwa yanzu hukumomin ƙasar ba su fitar da alƙaluman waɗanda suka mutu ba.
Samia Suluhu Hassan dai ta lashe zaɓen ƙasar ne da kashi 98 na ƙuri'ar ƙasar.