Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 17/11/2025

Wannan shafi ne da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 17/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Aliyu Ja'afar da Abdullahi Bello Diginza

  1. Jamus na shirin ɗage haramcin sayar wa Isra'ila da makamai

    Netanyahu

    Asalin hoton, AFP

    Jamus na shirin dage haramcin da ta sanya a baya na fitar da makamai zuwa Isra'ila wadanda za a iya amfani da su a Zirin Gaza.

    A watan Agusta ne aka sanar da dakatar da fitar da wasu makamai, a lokacin da sojojin Isra'ila suka zafafa hare haren da suke yi a birnin Gaza.

    Gwamnatin Jamus ta ce ta janye matakin ne saboda yarjejeniyar da aka cimma da kuma bada damar shigar da kayan agajin da ake yi.

    Jamus ce ƙasa ta biyu a duniya cikin ƙasashen da suka fi fitar da makamai zuwa Isra'ila baya ga Amurka.

  2. Rufewa

    Jama'a a nan muka kawo karshen wannan shafin na labaran kai-tsaye na wannan rana ta Litinin.

    Sai kuma gobe idan Allah Ya nuna mana.

    Da fata kun ji dadin kasancewa tare da mu.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  3. An fara bincike Vinted kan fitar da hotunan ɓatsa

    Vintage

    Asalin hoton, Getty Images

    An soma gudanar da binciken dandalin yanar gizon nan ta Vinted mai sayar da kayan sawa a Faransa, bayan da ya saka wata talla bisa kuskure da ke nuna hotunan batsa ta hanyar jagorantar masu bibiya zuwa wata kafar da ke tallata wadannan bidiyo da hotunan.

    Abokan huldar dandalin sun bayyana cewa idan suka danna likau na kafar domin zaben kayan ninkaya, ya kan kai su wadannan wurare.

    Kamfanin da asalinsa na kasar Lituwaniya ne ba shi da tsarin tantance shekarun abokan hulda, abin da hakan ke sa yara kanana ke da damar bin kafar domin shiga bangarorin da za su kai su wurin kallom hutunan abubuwan batsa.

    To sai dai kamfanin na Vinted ya ce lamari ne da ba za a lamunta ba kuma nan take ya cire duk wasu tallace-tallace masu alaka da hakan.

  4. Shugabar Tanzania ta naɗa ƴarta da surikinta ministoci a ƙasar

    Tanzania

    Asalin hoton, Reuters

    Shugabar ƙasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta fitar sa sababbin ministocin ƙasar, inda ta sanar da sanar da ƙirƙirar sabuwar ma'aikatar matasa, sannan ta ƙara yawan ma'aikatun ƙasar daga 26 zuwa 27 a sabuwar gwamnatin.

    Daga cikin ministocin akwai sababbin fuskoki, da tsofaffin ƴan siyasar ƙasar, ciki har da tsofaffin ministoci bakwai, sannan ba ta mayar da tsohon mataimakin firaministan ƙasar kuma ministan makamashi, Dotto Biteko da tsohon shugaban majalisar ƙasar, Tulia Ackson ba.

    Sai dai hankali ya fi komawa ne kan naɗa ƴar shugabar ƙasar, Wanu Hafidh a matsayin mataimakiyar ministar ilimi, sannan ta naɗa surikinta, Mohamed Mchegerwa a matsayin ministan lafiya a cikin sababbin ministocin.

    Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugabar ƙasar ta kafa kwamitin bincike domin gano musabbin zanga-zangar bayan zaɓe da aka yi a ƙasar.

    Jam'iyyun hamayya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun zargi jami'an tsaron ƙasar da kashe ɗaruruwan mutane, sannan suka ɓoye gawarwakinsu.

    Sai dai har zuwa yanzu hukumomin ƙasar ba su fitar da alƙaluman waɗanda suka mutu ba.

    Samia Suluhu Hassan dai ta lashe zaɓen ƙasar ne da kashi 98 na ƙuri'ar ƙasar.

  5. Iyalan waɗanda aka kashe a zanga-zangar Bangladesh sun yi maraba da hukuncin Sheikh Hasina

    Hasina

    Asalin hoton, Reuters

    Iyalai da 'yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata.

    An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba 'yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga, inda aka yanke mata hukuncin a bayan idonta.

    Gwamnatin Bangaledash ta bukaci Indiya da ta tusa keyar Hasina da ke gudun hijira a can domin ta fuskanci hukuncin.

    Wakiliyar BBC ta ce; Hukumomin Indiya na cewa suna ci gaba da bibiyar lamarin tsakanin Sheikh Hasina da mahukuntan Bangaledash kuma hakan na nufin Indiya na neman wata hanyar diflomasiyya akan lamarin.

  6. Uwargidan gwamnan Sokoto ta tallafa wa mata da suka haifi ƴan uku a jihar

    Uwargidan gwamnan jihar Sokoto

    Asalin hoton, Uwargidan gwamnan jihar Sokoto

    Uwargidan Gwanman Jihar Sokoto, Dr. Fatima Ahmad Aliyu, ta kaddamar da shirin tallafin abinci da kuɗi ga matan da suka haifi ƴan uku a kananan hukumomi 19 na jihar.

    Kowace uwa ta samu buhunan shinkafa da gero guda biyar, tare da tallafin kuɗi na naira miliyan daya domin rage nauyin kula da jarirain.

    Dr. Fatima Ahmad Aliyu ta ce shirin na nuna kulawa ne ga iyaye masu fuskantar ƙalubalen kashe kuɗi da nauyin rainon yaran ƴan ukku.

    Wakilai daga dukkan kananan hukumomin sun halarci bikin, inda aka ba iyayen yaran da aka yi wa rajista kayan tallafin.

    Da take jawabi a wajen taron rabo, uwargidan gwamnan ta ce wannan somi-taɓi ne, inda ta ce za ta ci gaba da gudanar da tallafi ire-iren wannan lokaci bayan lokaci.

    Uwargidan gwamnan jihar Sokoto

    Asalin hoton, Uwargidan gwamnan jihar Sokoto

  7. Sace ɗalibai mata a Kebbi gazawar gwamnati ce - Amnesty

    Amnesty International Nigeria

    Asalin hoton, Amnesty International Nigeria

    Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da garkuwa da mata sama da 25 da aka yi a makarantar sakandare ta mata da ke garin Maga a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ƙungiyar ta bayyana da abin ban mamaki.

    Ƙungiyar ta ce sace matan na ƙara nuna gazawar gwamnatin Najeriya wajen kare rayukan al'ummar ƙasar da dukiyoyinsu.

    "Bincikenmu ya gano cewa an sace matan ne bayan ƴanbindiga sun kutsa makarantar da misalin ƙarfe 5 na safiya, inda suka kashe mai gadi, da mataimakin shugaban makaranta, sannan suka tilasta wani ya nuna ɗakin kwanan ɗalibai mata, inda suka yi awon gaba da ɗaliban."

    Ƙungiyar ta ce wannan sace ɗaliban na nuna cewa "gwamnatin Tinubu ba ta da wani tsari ingantacce na kawo ƙarshen ta'addancin ƴanbindiga da suka ɗauki shekaru suna yi aika-aika a ƙasar, domin wannan na nuna cewa dukan matakan da gwamnatin ta ɗauka ba sa aiki domin ba a sa haifar da ɗa mai ido," kamar yadda ƙungiyar ta bayyana a wata sanarwa.

    Amnesty ta buƙaci gwamnatin ta ɗauki matakin gaggawa wajen ceto ɗaliban, sannan ta buƙaci hukumomi a ƙasar su gudanar da bincike domin ganowa tare da kare yawaitar sace-sacen mutane a jihar, wanda a cewarta yake barazana ga ilimi.

  8. Magoya bayan A.A Zaura sun buƙaci ya tsaya takarar gwamnan Kano

    Abdussalam Abdulkarim Zaura - AA Zaura

    Asalin hoton, Abdussalam Abdulkarim Zaura - AA Zaura/Facebook

    Magoya bayan tsohon ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya, Abdussalam Abdulkarim Zaura, wanda aka fi sani da A.A Zaura sun gudanar da taro, inda suka bayyana shi a matsayin wanda suke so ya fito takarar gwamnan jihar a zaɓen shekarar 2027.

    Magoya bayan ɗan siyasar sun gudanar da taron ne a ƙarƙashin jagorancin Iliyasu Hassan Gwazaye, inda suka gudanar da taruka a sassa daban-daban na jihar, sanye da riguna da huluna ɗauke da hotunan A.A Zaura.

    Lamarin ya ɗauki hankali ne ganin A.A Zaura ya tsaya takarar sanata ne a zaɓen shekarar 2023 a jam'iyyar APC, amma a yanzu magoya bayansa suke bayyana cewa shi ya fi cancanta ya zama gwamnan jihar mai ɗimbin jama'a.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da siyasa ke ci gaba da zafi jam'iyyar APC a jihar Kano game da wanda zai tsaya takarar gwamnan jihar, inda magoya bayan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin da na tsohon ɗan takarar gwamnan jihar, Yusuf Gawuna suke ta ƙoƙarin tallata gwanayensu, suna masu cewa nasu ne ya fi dacewa.

  9. 'Aƙalla fursunonin Falasɗinawa 100 ne suka rasu a Isra'ila'

    Fursuna

    Asalin hoton, Reuters

    Wata fitacciyar kungiyar fafutukar kare hakkin dan Adam a Isra'ila ta ce fiye da Falasdinawa dari ne suka rasa rayukansu wadanda ake tsare da su tun daga 7 ga watan Octoban 2023.

    Kungiyar ta ce fiye da rabin wadanda suka mutun na tsare ne a hannun sojoji, sauran kuma na gidajen yari daban-daban.

    Ta kuma ta'llaka mutuwar mutanen bisa dalilan azabtarwa saboda raunukan da aka samu a jikinsu na nuna hakarkarin wasunsu a karye.

    Sai dai mai magana da yawun wani gidan yarin Isra'ila ya musanta wadannan zarge-zarge, tare da cewa hukumomin Isra'ila na kiyaye doka a yayin da ake tsare da fursunoni.

  10. Jami'an tsaro a Nijar sun kama wasu da ake zargi da safarar man fetir ga ƴanbindiga

    ORTN

    Asalin hoton, ORTN

    Wani samame da rundunar tsaron Nijar ta Garde Nationale ta gudanar ya bata damar kama wasu mutane shida da ake zargi da safarar man fetur ga kungiyoyi masu ɗauke da makamai.

    An kama mutane shida da ake zargi ne a wani ɓangare na ayyukan da rundunar ta ƙaddamar cikin ƴan kwanakin nan domin yaki da ta’addanci da safarar man fetur da ake yi wa ƙungiyoyi masu tayar da ƙayar baya.

    Jamhuriyar Nijar dai na fuskantar barazanar tsaro daga mayaƙa masu riƙe da bindiga, a daidai lokacin da ƙasar ke ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin mulkin soji.

  11. Zalensky ya ƙulla yarjejeniyar tsaron sararin samaniya da Faransa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi nasarar cimma wata muhimiyyar yarjejeniya da za ta ba shi damar samun na'urorin kare sararin samaniya daga kasar Faransa.

    Mista Zalenski da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron sun gana a wata tashar jirgin sama da ke kusa da birnin Paris, inda suka rattaba hannu akan yarjejeniyar sayen daruruwan jiragen saman yaƙi samufurin Rafale, da na'urorin harba makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuki.

    Shugabannin biyu sun kai ziyara a wani wuri da ake sa ran za a samar da wani sansanin rundunar soji ta ƙasashe daban daban da ake ganin ita ce za ta yi yunkurin tabbatar da tsagaita wuta tsakanin Ukraine da Rasha.

    Wakilin BBC ya ce duk da an soma shirin samar da hedkwatar tsaron, amma a zahiri akwai sojoji daga kasashen Faransa da Birtaiya da sauran su, da ke nazarin abin da zai faru a baya idan har an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kasashen biyu, ciki har da irin matakan da za a ci gaba da dauka nan gaba.

  12. 'Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama da take tsare da su'

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata fitacciyar kungiyar fafutukar kare hakkin dan Adam a Isra'ila ta ce fiye da Falasdinawa dari ne suka rasa rayukansu wadanda ake tsare da su tun daga 7 ga watan Octoban 2023.

    Kungiyar ta ce fiye da rabin wadanda suka mutun na tsare ne a hannun sojoji, sauran kuma na gidajen yari daban-daban.

    Ta kuma ta'llaka mutuwar mutanen bisa dalilan azabtarwa saboda raunukan da aka samu a jikinsu na nuna hakarkarin wasunsu a karye.

    Sai dai mai magana da yawun wani gidan yarin Isra'ila ya musanta wadannan zarge-zarge, tare da cewa hukumomin Isra'ila na kiyaye doka a yayin da ake tsare da fursunoni.

  13. Ministan Afirka ta Kudu ya zargi Isra'ila da ƙoƙarin raba Falasɗinawa da ƙasarsu

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan Maikatar harkokin wajen Afirka ta Kudu ya zargi Isra'ila da kokarin raba Falasdinawa daga kasarsu.

    Wadannan kalama na na zuwa ne bayan da aka karkatar da akalar wani jirgin saman fasinja zuwa Johanesburg dauke da Falasdinawa 153 da kuma tun farko ya nufi kudancin birnin Eilat na Isra'ila ne.

    Wata kungiyar bayar da agaji dai ce ta tsara tafiyar, kuma Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce ba ta da masaniyar kome akan lamarin sai a ranar Alhamis da suka sauka.

    Ministan harkokin wajen Afrika ta Kudun Ronald Lamola, ya ce matakin na da nasaba da wata boyayyar manufar neman share Falasdinawa ne daga Gaza.

  14. ISWAP ta kashe kwamandan sojan Najeriya a Borno

    Mayaƙan ƙungiyar ISWAP da ke kai hare-hare a jihar Borno sun kashe wani kwamandan sojin saman Najeriya, bayan samun damar katse bayanan wurin da sojojin suke a tsakanin Damboa da Biyu da jihar.

    Jaridar PR Nigeria ta rawaito cewa sojan shi ne kwamandan da ke jagorantar rundunar da ta kai wa sojojin haɗin gwiwa na CJTF ɗauki waɗanda ƙungiyar ta yi wa kwantan ɓauna.

    Da farko dai sai da kwamandan wanda aka ɓoye sunansa ya wallafa wani bidiyo inda yake sanar da manyansa irin nasarar da suke samu. Sai dai rahotanni sun ce ƴan ƙungiyar sun bibiyi wurin da kwamandan yake sannan suka katse sadarwar, inda kuma suka samu suka kama shi sannan suka kashe shi bayan yi masa tambayoyi.

    Kwandan dai na jagorantar rundunar da ke kai ɗauki ga wasu dakarun Najeriya da suka yi ɓatan hanya abin da ya janyo mayaƙan na ISWAP suka yi musu kwantan ɓauna.

  15. Yadda ƴanbindiga suka sace ɗalibai mata a Kebbi

    kofar makaranta

    Asalin hoton, MUSTAPHA IBRAHIM/BBC

    Hukumomi a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da harin da wasu ƴan bindiga suka kai a Makarantar Sakandiren Ƴanmata da ke garin Maga, inda suka kashe aƙalla ma'aikaci ɗaya da sace ɗalibai.

    Lamarin ya faru ne da asubahin Litinin lokacin da ɗaliban ke shirin tashi sallar asuba.

    Bayanai sun ce maharan sun far wa makarantar ɗauke da muggan makamai inda suka yi ta harbi kafin daga bisani su tafi da ɗalibai, waɗanda ba a riga an tantance adadinsu ba.

    Wannan ne hari na baya-baya da irin waɗannan ƴan bindiga suka riƙa kaiwa a makarantu suna sace ɗalibai a jihohi daban-daban na ƙasar, musamman yankin arewacin ƙasar mai fama da ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

    Karanta cikakken labarin a nan

  16. Hauhawar farashi ta ragu a watan Oktoba - NBS

    kayayyaki a kasuwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce Hauhawar farashin kayyayaki a ƙasar ta ragu zuwa kashi 16.05 cikin 100 a watan Oktoban 2025.

    Cikin rahoton wata wata da hukumar ke fitarwa, ta ce hauhawar farashin ta ragu ne da kashi 1.97 idan aka kwatanta da kashi 18.02 da aka samu a watan Satumba.

  17. Jamus za ta ci gaba da sayar wa Isra'ila makamai

    Ƙasar Jamus ta ce tana shirin cire kaidojin da ta sanya kan fitar da makamai zuwa Isra'ila waɗanda za a iya amfani da su a Zirin Gaza.

    A watan Agusta ne aka sanar da dakatar da fitar da wasu makamai, a lokacin da sojojin Isra'ila suka zafafa hare haren da suke yi a birnin Gaza.

    Gwamnatin Jamus ta ce ta janye matakin ne saboda yarjejeniyar da aka cimma da kuma shigar da kayan agajin da ake yi.

    Jamus ce ƙasa ta biyu a cikin ƙasashen da suka fi fitar da makamai zuwa Isra'ila baya ga Amurka.

  18. Ƙungiyar Fulani ta buƙaci Trump ya cire sunanta daga cikin masu 'gallaza wa Kiristoci'

    Makiyayi

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata ƙungiyar Fulani makiyaya a Najeriya ta soki shawarar da aka gabatar a majalisar dokokin Amurka na kiran a sanya mata takunkumi saboda 'gallaza wa Kiristoci'.

    Ƙungiyar Miyetti Allah (Macban) ta ce ba ta taɓa goyon bayan wani nau'i na aikata laifi ko zalunci ba.

    ''Cikin mutunci Macban ke kiran a sake waiwayar shawarar da aka gabatar ta HR 860 domin a cire duk inda aka ambaci Macban. Muna so mu bayyana ƙarara cewa Macban ba ta goyon baya, ko lamunta ko tallafawa, ko kare aikata wani laifi,' A cewar shugaban ƙungiyar Baba Ngelzarma.

    ''Ƙungiyar Macban ba ƙungiyar ƴan bindiga ba ce, kuma ba ta taɓa zama haka ba. Da kakkausar murya mu ke Allah wadai da harin ƴan bindiga, da satar shanu, da garkuwa da mutane ko wani laifin.''

    Ngelzarma ya faɗi hakan ne bayan ƴan majalisar wakilai Christopher Smith da Bill Huizenga sun gabatar da shawarar a majalisar dokokin Amurka bayan shugaban Trump ya ayyana Najeriya a matsayin 'ƙasar da ake da damuwa a kanta' kan zargin hana walwalar addini.

    Shawarar da aka gabatar na neman a ƙwace kadarori da hana biza ga ƙungiyoyin Macban da Miyetti Allah Kautal Hore da wasu ƙungiyoyin Fulani, da ɗaiɗaikun mutane da ke aiki a jihohin Benue da Filato, waɗanda ke fama da rikicin makiyaya da manoma.

  19. Faransa ta amince ta sayar wa Ukraine makamai

    Shugaba Macron da Zelensky su na gaisawa

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi nasarar cimma wata muhimiyyar yarjejeniya da za ta bashi damar samun na'urorin kare sararin samaniya daga Faransa.

    Ya sanya hannu kan yarjejeniyar samun gwamman jiragen saman yaƙi, da na'urorin harba makamai masu linzami da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron a wata tashar jirgin sama da ke kusa da Paris.

    Ana kuma sa ran Mista Zelensky zai yi rangadi a wani wuri da ake sa ran za a gina sansanin rundunar soji ta ƙasashe daban daban wadda ake ganin ita ce za ta yi yunkurin tabbatar da tsagaita wuta tsakanin Ukraine da Rasha.

    Tun da farko hukumomi a gabashin Ukraine sun ce wani harin makami mai linzami na Rahsa ya hallaka mutum uku a yankin Kharkiv.

  20. Hatsarin mota ya kashe Indiyawa 45 masu aikin umara a Saudiyya

    Wani hatsari a birnin Riyad na ƙasar Saudiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wani hatsari a birnin Riyad na ƙasar Saudiyya

    Hukumomi a Indiya sun ce ƴan ƙasar 45 masu aikin Umara a Saudiyya sun mutu bayan motar su ta yi hatsari tare da kamawa da wuta.

    Masu aikin ibadar, waɗanda akasarinsu ƴan jihar Telangana ne, na kan hanyar su ta zuwa Madina ne daga Makkah a lokacin da suka yi hatsarin.

    Mutum ɗaya daga cikinsu wanda ya tsira na asibiti cikin mawuyacin hali.

    Hukumomin sun ce hatsarin ya kuma haɗa da wata tankar dakon man fetir, amma ba su yi ƙarin bayani kan hakan ba.

    FiraMinistan Indiya Narendra Modi ya ce ya matuƙar kaɗu, ya kuma miƙa ta'azziyyar sa.