Mai tsaron ragar tawagar Italiya, Gianluigi Donnarumma, ya ce yana jin zafi sosai kan rahotannin da ke cewa ƴan wasa sun nemi a ba su lada idan sun samu tikitin shiga gasar FIFA World Cup ta bana.
Italiya, wadda ta taba lashe kofin duniya sau hudu, ta kasa samun gurbin zuwa gasar karo na uku a jere bayan da ta sha kashi da ci 4-1 a bugun fenariti a hannun Bosnia and Herzegovina a wasan cike gurbi a watan da ya gabata.
“A matsayina na kyaftin, ban taɓa zuwa neman ko euro guda daga hukumar ƙwallon kafar kasar ba,” in ji Donnarumma a hirar da ya yi da Sky Sports Italia.
“Abin da ake yi a kullum shi ne, idan an samu tikitin shiga wata gasa, ana bai wa ƴan wasa kyauta ne kamar yadda aka saba.”
Rashin samun tikitin shiga gasar kofin duniya ya sa shugaban hukumar ƙwallon kafar kasar, Gabriele Gravina, ya yi murabus sakamakon matsin lamba, yayin da tsohon mai tsaron raga Gianluigi Buffon ya sauka daga mukaminsa na shugaban tawagar.
Haka kuma kocin tawagar, Gennaro Gattuso, ya bar aikinsa.