KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa na 7 zuwa 11 ga watan Afrilun 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Talata 7, zuwa Asabar 11 ga watan Afrilun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Abdu, Haruna Kakangi

  1. Wa ye kan gaba a tsaron raga a tsakanin Raya da Neuer?, Masu tsaron raga a Champions League

    An buga Champions League zagayen kwata fainal wasan farko a Champions League ranar Talata inda Real Madrid ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Bayern Munick, Arsenal ta je ta ci Sporting 1-0.

    Abin da ya ja hankali shi ne rawar da mai tsaron ragar Bayern Munich ya taka, Maneul Neuer da na Arsenal David Raya - hakan ya sa ake cece-kuce kan wane mai tsaron raga ne ba kamarsa a Turai a bana.

    Rawar da Manuel Neuer ya taka ta taimaka wa Bayern Munich ta samu nasara a kan Real Madrid, kuma hakan ya jawo tattaunawa sosai a jaridun Jamus suna kira da a sake dawo da shi cikin tawagar ƙasar Jamus duk da cewa yana da shekaru 40 ya kuma yi ritaya.

    Wannan lamari ya buɗe sabon muhawara kan wanda ya fi kowa iya tsaron raga a duniya a halin yanzu—musamman ganin cewa gasar FIFA World Cup na gabatowa.

    Manuel Neuer

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Man City za ta ci gaba da matsa lamba ga Arsenal a Premier, Premier League

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City za ta koma buga gasar Premier League a wannan karshen mako, yayin da burinsu bai wuce lashe kofin ba, bayan kusan wata guda ba su buga wasannin lig ba.

    Wannan hutu ya biyo bayan wasan kasa da kasa International break da bikin lashe Carabao Cup da fitar da Liverpool daga FA Cup na kakar nan.

    Hakan ya sa City ba ta buga wasan Premier League ba tun daga kunnen doki 1-1 da West Ham a ranar 14 ga Maris. Yanzu kuma hankalin su ya koma wasan da za su yi da Chelsea a ranar Lahadi.

    Kungiyar Pep Guardiola na ƙoƙarin ƙara matsa lamba ga Arsenal da ke jagorantar teburin gasar da maki tara tsakani, duk da cewa Arsenal ta buga wasa 31 City kuwa 30 ta yi, kuma har Gunners za ta je Etihad domin buga wasa nan gaba a wannan watan.

    A bangaren lafiyar 'yan wasa, John Stones da Ruben Dias suna cikin rashin tabbas kan wasan da City za ta je Stamford Bridge.

  3. Paris Saint-Germain v Liverpool, Filin wasa: Parc des Princes

    Ousmane Dembele da Mohammed Salah

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ousmane Dembele na PSG da Mohammed Salah na Liverpool

    A karawa shida na baya-bayan nan tsakanin PSG da Licerpool kowannensu ta yi nasara sau uku.

    Paris Saint-Germain da Liverpool sun kara sau 58 a baya, inda PSG ta yi nasara sau 34 yayin da Liverpool ta yi nasara sau 24.

    Yayin da Liverpool za ta je baƙunci yau Laraba a birnin Paris, ana ganin ya kamata Liverpool ta yi gyare-gyare bayan fadi-tashin da ta riƙa fama da shi a wannan kakar wasanni.

    A kakar da ta gabata, PSG ce ta yi waje da Liverpool a matakin yan 16, inda ta yi gaba har ta lashe kofin na zakarun Turai.

  4. Mataimakin kociyan United ya ce burinsu ya wuce samun shiga Champions League kaɗai, Champions League

    Micheal Carrick

    Asalin hoton, Getty Images

    Mataimakin kocin Manchester United, Steve Holland, ya bayyana cewa ƙungiyar na da burin fiye da kawai samun gurbin shiga gasar UEFA Champions League a baɗi, yayin da kakar wasar bana ke dab da ƙarewa.

    United ta koma matsayi na uku tun bayan da Michael Carrick ya karɓi ragamar horarwa a watan Janairu daga Ruben Amorim, kuma saura wasa bakwai suka rage mata, tana kan hanyar dawowa gasar Turai a baɗi, bayan da ba ita a wasannin bana.

    Holland ya ce: “A matsayin wannan ƙungiya, dole ne mu yi ƙoƙarin kammala kakar a kusa da saman teburi gwargwadon iko. Ko da yake ba mu san yadda hakan zai yiwu ba, amma wannan shi ne burin mu.''

    Ya ƙara da cewa mun fi mayar da hankali kan cin wasanni maimakon damuwa da abin da ke faruwa a ƙasan teburi, amma ya amince cewa samun gurbin Champions League zai zama nasara mai kyau.

    Fatan United na shiga Champions League ya ƙara ƙarfi bayan da Arsenal ta doke Sporting Lisbon da ci 1-0 a wasan farko a quarter-final, wanda ya tabbatar da cewa Premier League za ta samu aƙalla ƙungiya biyar a gasar ta kakar mai zuwa.

    Kafin ƙarshen mako, United ta bai wa Chelsea tazarar maki bakwai tsakaninta wadda take ta shidan teburi.

    United ta yi sansanin atisaye a wajen Dublin, inda ta yi amfani da hutu na kwanaki 24 tun daga tsakanin wasan da ta tashi 2-2 da Bournemouth da kuma wasan da za ta yi da Leeds United.

    Wannan tsawon lokaci tsakanin wasannin ya faru ne saboda hutun wasannin ƙasa da kuma ficewar United daga gasannin kofuna da wuri.

    Holland ya ce wannan hutu ya ba su damar sake haɗa kan ƴan wasa domin kammala kakar ba da kwari gwiwa.

  5. Arsenal za ta lashe Champions League - Havertz, Champions League

    Kai Havertz

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Arsenal, Kai Havertz, ya bayyana cewa akwai wani abu na musamman da zai iya faruwa a ƙungiyar, bayan abokin wasansa David Raya ya ce suna da tabbacin kashi 100% za su iya lashe UEFA Champions League a bana.

    Havertz ne ya ci ƙwallon nasara a wasan da Arsenal ta doke Sporting Lisbon da ci 1-0 a Portugal, wanda ya ba su babbar dama kafin wasa na biyu a Emirates a mako mai zuwa.

    Bayan rashin nasara biyu a jere a karon farko a kakar wasa, Arsenal ta shiga wannan wasa cikin matsin lamba, amma wannan nasara da ta samu a Portugal ta ƙara mata ƙwarin gwiwa.

    Manchester City ta doke Arsenal ta lashe Carabao Cup, sannan Southampton ta fitar da Arsenal daga FA Cup na kakar nan.

    Havertz ya ce: “Mun buƙaci wannan nasara saboda mun yi takaici kan doke mu wasa biyu a jere. Yanzu lokaci ne na ci gaba da kasancewa a kan ganiya da sa kwazo da kuma haɗin kai.”

    Ya ƙara da cewa dukkan ƴan wasa da ma’aikata da magoya baya suna tare da mu, domin cimma wani abu na musamman a wannan kakar.

    Nasarar Arsenal ta samo asali ne daga gogewar mai tsaron gida David Raya, wanda ya hana ƙwallaye da dama shiga ragar Arsenal.

    Duk da cewa an ajiye shi a wasu wasannin baya, ya dawo ya nuna kwarewarsa sosai. Raya ya riga ya yi wasa 22 ba tare da ƙwallo ya shiga raga ba a fafatawa 41 a wannan kakar – abin da ya zarce sauran masu tsaron gida a manyan lig-lig na Turai.

    Ya kuma bayyana cewa Arsenal na da imanin cewa za su iya kaiwa wasan kusa da na ƙarshe da kuma lashe gasar.

    A karshen mako Arsenal za ta koma gasar Premier League inda za ta karɓi baƙuncin Bournemouth, yayin da Manchester City za ta kara da Chelsea.

  6. De Zerbi ya je Tottenham tare mataimaka biyu, Tottenham

    De Zerbi

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabon kocin Tottenham, Roberto De Zerbi, ya koma sabuwar ƙungiyarsa tare da wasu ma’aikata biyu.

    Ƙungiyar ta sanar ranar Laraba cewa Marcattilio Marcattilii da Marcello Quinto za su yi aiki a Tottenham, inda na farko zai zama kocin motsa jiki, yayin da na biyun zai kula da ci gaban ƴan wasa wato ingancinsu.

    Marcattilii ya daɗe yana aiki tare da De Zerbi tun daga lokacin da suka fara aiki a ƙungiyar Foggia a shekarar 2015.

    Shi kuma Quinto ya sake haɗuwa da De Zerbi a Tottenham bayan sun taba aiki tare a Brighton da kuma Marseille.

    Sai dai sauran wasu ma’aikata guda biyar da De Zerbi ya yi aiki da su a baya ba su bi shi zuwa Tottenham ba, ciki har da mataimakinsa da suka dade Andrea Maldera.

    Tottenham ta tabbatar da cewa mataimakin koci Bruno Saltor zai ci gaba da aiki tare da Andreas Georgson, Cameron Campbell da Fabian Otte.

    Haka kuma, Dean Brill da Stuart Lewis za su ci gaba da taimakawa ƙungiyar kamar yadda suke yi a baya.

    An yi ta rade-radin cewa tsohon ɗan wasan AC Milan, Alessandro Nesta, da tsohon ɗan wasan Totenham, Sandro za su shiga cikin ma’aikatan De Zerbi.

    Wasan farko da De Zerbi zai jagoranta a Tottenham shi ne karawar da za su yi da Sunderland a ranar Lahadi a Premier League.

  7. Ana sa ran Summerville zai wasa ranar Juma'a bayan jinyar wata ɗaya, West Ham

    West Ham

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran ɗan wasan West Ham United, Crysencio Summerville, zai dawo fili domin muhimmin wasan da za ta yi da Wolverhampton Wanderers a daren Juma’a a gasar Premier League, wanda zai taimaka wajen yanke makomar su a kokarin kada su faɗi daga gasar.

    Summerville, ɗan ƙasar Holland mai shekaru 24, ya yi sama da wata guda baya wasa sakamakon raunin ƙafar maraƙi da ya ji a wasan FA Cup da suka doke Brentford.

    Kafin wannan rauni, shi ne ke jan ragamar ƙoƙarin West Ham na tsira daga faduwa daga Premier League, inda ya zura ƙwallo bakwai a wasa goma.

    Haka kuma, ana sa ran ƴan wasa kamar Konstantinos Mavropanos, Jean-Clair Todibo da Callum Wilson za su dawo fagen daga, bayan da ba su buga FA Cup da suka sha kashi a bugun fanareti a hannun Leeds United.

    Aaron Wan-Bissaka ma yana dab da dawowa cikin ƙungiyar, wanda bai koma Ingila da wuri ba sakamakon buga wa DR Congo wasa, wacce ta yi murnar samun tikitin shiga gasar FIFA World Cup.

    Kungiyar ba ta ji daɗin rashin halartarsa ba, kuma tana iya kai ƙara ga FIFA, amma kocin ya ce ba zai shiga cikakken bayani ba, yana mai cewa: “Sun yi babban abu a Congo, kuma yanzu ya dawo cikin koshin lafiya.”

  8. Santos ya ce ya mayar da hankali kan yadda Chelsea za ta koma kan ganiya, Chelsea

    Chelsea

    Asalin hoton, Getty Images

    Andrey Santos, ya ce ya ajiye burinsa na buga Gasar Kofin Duniya a gefe domin ya mayar da hankali kan burin Chelsea ta koma kan ganiya kan karshen kakar nan.

    Ɗan kasar Brazil ya kasance ɗaya daga cikin ƴan wasan Chelsea bakwai da suka zura kwallaye a FA Cup zagaye kwata fainal da suka lallasa Port Vale da ci 7-0 a Stamford Bridge ranar Asabar, inda suka samu tikitin buga wasan kusa da na karshe da za su fafafata da Leeds United a Wembley.

    Amma kafin nan, Chelsea za ta fuskanci kalubale mai tsauri a hannun Manchester City da Manchester United a Premier League, yayin da suke ƙoƙarin neman tikitin shiga Champions League na baɗi, yayi da saura wasa bakwai suka rage mata a karkare kakar nan.

    Matashin mai shekara 21 na matuƙar fatan samun damar buga karawa a filin Wembley mai tarihi a ranar 25 ga Afrilu.

    Tuni aka sauya wasan Chelsea da Brighton a Premier League, saboda karawar kusa da na karshe a FA Cup, yanzu za a buga shi a ranar 21 ga Afrilu, kwanaki biyar kafin ranar da aka fara tsara shi.

  9. ''Bayern ta kara samun ƙwarin gwiwa bayan cin Real Madrid'', Champions League

    Harry Kane

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Bayern Munich, Vincent Kompany, ya ce ƙungiyarsa ta kara samun kwarin gwiwa, bayan da ta doke Real Madrid da ci 2-1 a wasan farko a quarter-final a gasar UEFA Champions League ranar Talata.

    Bayern ba ta yi rashin nasara ba a wasa 14 da ta buga a dukkan fafatawa, yayin da take kan gaba a kare kambun Bundesliga. Haka kuma tana da damar kaiwa wasan kusa da na ƙarshe a Champions League karo na biyu a jere idan ta samu sakamako mai kyau a wasa na biyu ranar 15 ga Afrilu.

    Kompany ya ce: “Abu mafi muhimmanci a gare mu shi ne mu ci gaba da wannan kwazon. Za su ba mu wahala sosai, domin su ma ƙungiya ce da za ta iya yin abin mamaki.”

    Ya kamata mu lura cewa karo na ƙarshe da Bayern ta doke Real Madrid shi ne a 2017, inda ta ci 2-1 a Madrid, amma daga baya Real ta yi nasara bayan ƙarin lokaci.

    Tun daga 2012, Bayern ba ta taɓa doke Real Madrid a wasa biyu ba gida da waje a lokacin da ta kai su a wasan kusa da na ƙarshe ta hanyar bugun fanareti.

    Kompany ya ƙara da cewa suna girmama Real Madrid sosai, amma kuma suna da cikakken kwarin gwiwa saboda yadda suka kan ganiya a kwanan nan.

    Ya jaddada cewa ƙungiyarsa tana da burin samun sakamako mai kyau tare da nuna ƙarfi a wannan muhimmin lokaci a gasar.

  10. Barcelona v Atletico Madrid, Filin wasa: Camp Nou

    Lamine Yamal na Barcelona da Ademola Lookman na Atletico Madrid

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Lamine Yamal na Barcelona da Ademola Lookman na Atletico Madrid

    Barcelona da Atletico Madrid za su kara karo na biyar a gasar Turai, kuma dukkanin karawar tasu a baya ta faru ne a matakin kwata-fainal.

    Sun kara a gasar zakarun Turai ta Champions League a kakar wasa ta 2013-2014 da kuma 2015-16.

    A karawa 79 da ƙungiyoyin suka yi a baya Barcelona ce ta lashe guda 41, Atletico ta lashe 20 sannan aka yi canjaras sau 18.

    Atletico ta yi rashin nasara sau ɗaya ne tal a karawa huɗu na baya da ta yi da Barcelona a gasar Champions League.

  11. AN TASHI WASA: Sporting 0-1 Arsenal, Sporting 0-1 Arsenal

    Shi ke nan, ita ma Arsenal ta yi nasara a waje.

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

  12. AN TASHI WASA: Real Madrid 1-2 Bayern Munich, Real Madrid 1-2 Bayern Munich

    Lafari ya hura usur, an tashi wasa tsakanin Real Madrid da Bayern Munich, inda a ƙarshe masu masaukin baƙi suka sha kashi.

    Sai mun haɗu a karawa ta biyu a Allianz Arena.

  13. Sporting 0-1 Arsenal, Minti 90+1

    Arsenal ta samu jefa ƙwallo ta ƙafar Kai Haverts.

    Gabriel Martinelli ne ya ɗauko ƙwallo mai kyau zuwa cikin da'ira, inda nan take Kai Havert ya take ta sannan ya jefa ta a raga cikin natsuwa.

    Arsenal ba za ta damu ba ko da an tashi canjaras, amma yanzu ga shi ta yi nasara.

    XXX

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Canji: Arsenal ta saka Martinelli da Max Dowman, Sporting 0-0 Arsenal

    Arsenal ta yi canji biyu a lokaci ɗaya inda ta cire Noni Madueke da Leandro Trossard, ta sako Gabriel Martinelli da Max Dowman.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Real Madrid 1-2 Bayern Munich, Minti na 74

    Kylian Mbappe ya zura ƙwallo a ragar Bayern.

    Kylian Mbappe

    Asalin hoton, Getty Images

  16. , Sporting 0-0 Arsenal

    Abin takaici ga Arsenal ganin irin ƙwallo mai kyau da Zubemendi ya zura a raga, amma tabbas Viktor Gyokeres ya yi satan fage.

    Amma hakan zai iya bai wa Arsenal ƙwarin gwiwar cewa za ta iya yin nasara a wasan.

  17. An soke ƙwallon da Arsenal ta ci: Sporting 0-0 Arsenal

    Tabbas, Viktor Gyokeres ya yi satan fage kuma an duba VAR ya tabbatar da hakan. Har yanzu babu ci tsakanin Sporting da Arsenal.

  18. Real Madrid 0-2 Bayern Munich, (Minti na 46)

    Harry Kane

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Harry Kane

    Harry Kane ya zura ƙwallo ta biyu a ragar Real Madrid a minti na farko bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

    Hakan ya faru ne duk kuwa da cewa bai taɓuka wani abin a zo a gani ba kafin zuwa hutun rabin lokaci.

    Kafin a je hutun rabin lokaci ne Luiz Diaz ya zura ƙwallo ta farko a ragar Madrid a minti na 41.

  19. Agyemeng ba zai buga wa Amurka gasar kofin duniya ba, saboda rauni, Fifa World Cup

    Patrick Agyemang

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Amurka, Patrick Agyemang, ya samu raunin da zai hana shi buga gasar FIFA World Cup, kamar yadda ƙungiyarsa ta Ingila Derby County ta bayyana a ranar Talata.

    Ɗan ƙwallon mai shekaru 25 ya samu raunin ne a wasan da Derby ta doke Stoke City da ci 2-0 a gasar Championship ranar Litinin, inda aka fitar da shi daga fili a kan gadon ɗaukar marasa lafiya.

    Ƙungiyar ta ce za ta bai wa Agyemang kulawa daga likitoci da kuma shirin murmurewa mafi inganci har sai ya warke gaba ɗaya.

    Sai dai saboda wannan rauni, an tabbatar cewa ba zai buga World Cup a wannan bazara ba, kuma har yanzu ba a saka lokacin da zai dawo taka leda ba.

    Agyemang ya ci kwallo shida a wasa 14 da ya bugawa Amurka tun bayan fara taka mata leda a bara, kuma ya buga wasan sada zumunta a watan Maris.

    Kocin Amurka, Mauricio Pochettino, zai sanar da sunayen ƴan wasan da za su buga World Cup kafin ranar 30 ga Mayu.

    Amurka, wacce za ta ɗauki nauyin gasar tare da Canada da Mexico, za ta kara da Paraguay da Australia da kuma Turkiya a rukunin na huɗu.

    Za a fara gasar World Cup ne a ranar 11 ga Yuni.

  20. Fifa na kokarin ganin Iran ta buga gasar kofin duniya a bana, Fifa World Cup

    Fifa World Cup

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Iran ta ce ba za ta yanke hukunci kan halartar tawagar ƙasarta a gasar FIFA World Cup ba sai bayan ta samu amsa daga FIFA dangane da bukatar canza wurin wasannin ta.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Iran (FFIRI) na ƙoƙarin a mayar da wasannin rukuni da take ciki daga Amurka zuwa Mexico, saboda dalilan tsaro da suka danganci rikicin siyasa a yankin.

    A watan da ya gabata, FFIRI ta bayyana cewa tana tattaunawa da FIFA kan sauya wurin wasa, yayin da ma’aikatar wasanni ta Iran ta hana tawagar ƙasar da na ƙungiyoyinta zuwa buga wasa a ƙasashen da take kallon abokan gaba.

    Sai dai shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya sanar a makon da ya gabata cewa Iran za ta buga wasanninta kamar yadda aka tsara.

    A halin yanzu, an tsara Iran za ta buga dukkan wasanninta na rukuni a Amurka – inda za ta kara da New Zealand da Belgium a Los Angeles, sannan ta kammala da wasa da Egypt a Seattle.

    A gefe guda, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Iran za ta iya zuwa Amurka domin buga wasa, amma ya nuna damuwa kan tsaron su, duk da cewa daga baya ya bayyana cewa duk wani barazana ba zai fito daga Amurka ba.