Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa na 7 zuwa 11 ga watan Afrilun 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Talata 7, zuwa Asabar 11 ga watan Afrilun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Abdu, Haruna Kakangi

  1. Robertson zai bar Liverpool a karshen kakar bana, Liverpool

    Andy Robertson zai bar Liverpool FC a ƙarshen kakar wasa bana, bayan kwantiraginsa ya ƙare, kamar yadda ƙungiyar ta sanar.

    Robertson mai shekaru 32 ya koma Liverpool daga Hull City a shekarar 2017 kan kuɗi fam miliyan 8, kuma ya lashe kofunan Premier League biyu da UEFA Champions League Merseyside.

    Robertson ɗaya ne daga cikin ƴan wasan da Tottenham ke son siya a a watan Janairu, amma ba su kai ga cimma matsaya ba.

    Sai dai Liverpool ta kasa kammala cinikin ne saboda ba ta iya dawo da Kostas Tsimikas daga aron da yake yi a AS Roma ba.

    A wannan kakar, damar Robertson ta buga wa Liverpool wasanni ta ragu karkashin kocin Arne Slot, musamman bayan zuwan ɗan wasa Milos Kerkez wanda ya koma Liverpool daga AFC Bournemouth kan kwantiragi fam miliyan 40.

    Ya buga wasa 373 a Liverpool kuma ya lashe jimillar kofuna tara yayin da yake taka leda a Anfield.

  2. Kudus ya samu koma baya a jinyar da yake yi, Tottenham

    Ɗan wasan Tottenham Hotspur, Mohammed Kudus, ya samu koma baya a jinya da yake yi, akwai yiyuwar ya gama buga kakar wasan bana, in ji rahotannin Press Association.

    Kudus bai yi wasa ba tun daga ranar 4 ga Janairu sakamakon raunin da ya ji, tun farko an yi tsammanin zai koma atisaye a lokacin hutun wasannin ƙasa Maris.

    Sai dai sabon kocin Spurs, Roberto De Zerbi, ya samu mummunan labari, domin yanzu Kudus ba zai buga wasa bakwai da suka ragewa ƙungiyar ba, wanda ake cewa sai an kara yi masa tiyata.

    Ghana za ta buga gasar FIFA World Cup ta bana, kuma tana rukuni daya da ya haɗa da Ingila, don haka tsohon dan wasan West Ham United na fuskantar yadda zai warke da wuri domin ganin ya samu damar buga gasar a Amurka.

    Kudus ya buga wasa 26 a Tottenham tun bayan komawarsa daga West Ham kan kuɗi kusan fam miliyan 55 a watan Yuli, kuma ya fara wasa tara a jere kafin ya samu raunin farko a wasan da suka kara da Sunderland a ranar 4 ga Janairu.

  3. AC Milan da Inter da za su yi atisaye a Australia a karshen kakar nan, Wasannin sada zumunta

    AC Milan da Inter Milan da Juventus sun bayyana cewa za su buga jerin wasannin sada zumunci domin atisayen tunkakar kakar baɗi da za su buga a cikin watan Agusta a filin Perth a Australia, bayan da aka soke shirin gudanar da gasar lig ta Italiya a wata kasar a ƙarshen shekarar da ta gabata.

    Serie A ta tattaunawa kan shirya wasa tsakanin AC Milan da Como a Perth a watan Fabrairu, amma ta soke shirin a watan Disamba sakamakon wasu sharudda da hukumar ƙwallon kafar Asian ta gindaya.

    Da an gudanar da wasan da ya zama karo na farko da aka buga babbar gasar Italiya a wajen ƙasar.

    AC Milan za ta kara da Inter Milan a ranar 5 ga Agusta. Bayan haka Inter za ta fuskanci Juventus bayan kwana uku tsakani, sannan Juventus za ta kara da kungiyar Serie B ta Palermo a ranar 11 ga Agusta.

  4. Scotland za ta buga wasan sada zumunta da Bolivia a Amurka, Fifa World Cup 2026

    Tawagar ƙwallon kafa ta Scotland ta tabbatar da cewa za ta buga wasan sada zumunci da Bolivia a New Jersey a ranar Asabar 6 ga Yuni, wanda zai zama wasan karshe da za ta yi kafin gasar FIFA World Cup ta wannan bazara.

    Za a nuna wasan kai tsaye a tashar BBC, kuma za a fara da karfe 21:00 na dare (BST).

    Bolivia ta kasa samun tikitin shiga gasar bayan ta sha kashi 2-1 a hannun Iraq a karawar cike gurbi a birnin Guadalupe a Mexico a makon da ya gabata.

    Tawagar Steve Clarke ta Scotland ta sha kashi 1-0 a wasan sada zumunci da Japan da kuma Ivory Coast a wannan watan.

    Sai dai har yanzu suna da karin damarmaki biyu na inganta tawagar kafin wasan farko a gasar World Cup da Haiti a ranar 14 ga Yuni a Massachusetts a Amurka. Za su fara da karɓar bakuncin Curacao a wasan sada zumunta a Hampden Park a ranar 30 ga Mayu, sannan su kara da Bolivia a filin Sports Illustrated Stadium.

    Peru da Venezuela wadanda suma suka kasa tsallakewa zuwa gasar an tsara yin wasan sada zumunta da Scoctland, wadda ta zaɓi fuskantar Bolivia daga baya

    Hakan ya kawo karshen jerin wasannin sada zumunci da Scotland za ta buga da tawagogi daga yankuna iri daya da na abokan hamayyarta a rukuni na uku, wato Brazil da Morocco da kuma Haiti.

  5. Real Madrid za ta kara da Girona, bayan rashin nasara biyu a jere, Ggasar La Liga

    Real Madrid za ta karɓi baƙuncin Girona a ranar Juma’a, yayin da take ƙoƙarin ganin ta kamo Barcelona ta kuma lashe kofin La Liga.

    Real Madrid za ta shiga wasan ne bayan ta sha kashi 2-1 a gida a hannun Bayern Munich a wasan farko a zagayen kwata fainal a UEFA Champions League ranar Talata, da kuma rashin nasara 2-1 da ta yi a hannun Mallorca a karshen makon da ya gabata, wanda ya bar ta maki bakwai tsakani da Barcelona ta ɗaya a kan teburi, yayin da wasa takwas kacal suka rage.

    Kociyan Real Madrid, Alvaro Arbeloa ya ce za su ci gaba da matsa lamba har zuwa karshen kakar nan.

    Sai dai kocin ya shaida wa manema labarai cewa dole ne a dakatar da duk wani buri na Turai na ɗan lokaci, domin a maida hankali gaba ɗaya kan La Liga.

    Arbeloa ya jaddada cewa ba zai yi sauya-sauye a cikin ƴan wasansa ba duk da wasan Turai da ke tafe - ya ce abin da ke gabansu shi ne samun maki uku a kan Girona.

  6. Tottenham tana tsaka mai wuya a Premier League ta bana, Premier League

    An bukaci manyan ƴan wasan Tottenham Hotspur da su yi koyi da Archie Gray idan har ƙungiyar na son kauce wa daga faduwa a gasar firimiya karo na farko cikin shekaru 49.

    Spurs na matsayi na 17 a teburin Premier League bayan wasa 13 ba tare da samun nasara ba, kuma da karawa bakwai kacal suka rage mata, ta kuma ɗauki Roberto De Zerbi domin kokarin tsira ita daga faduwa daga Premier Lague.

    A cikin kakar bana mai cike da takaici, Gray ya kasance ɗaya daga cikin ƴan wasan da suka fi haskakawa, kuma David Howells — wanda ya taimaka wa Tottenham wajen kauce wa faduwa daga gasar a 1994 da 1997 — ya yi imanin cewa dole ne sauran ƴan wasan su bi sawun matashin mai shekaru 20 kafin wasan da za su je su kara da Sunderland a ranar Lahadi.

  7. Man United za ta yi atisaye a Finland da Norway da Sweden a kashen kakar bana, Wasannin sada zumunta

    Manchester United za ta buga jerin wasannin a ƙasar Finland da Norway da kuma Sweden idan an kammala kakar bana.

    Baya ga wasan da za ta yi da Leeds United a birnin Dublin a ranar 12 ga Agusta, ƙungiyar Red Devils ta kuma tabbatar da cewa za ta yi wasa hudu masu ƙyau.

    Za ta fara ne da karawa da Wrexham a birnin Helsinki a filin Olympic Stadium Helsinki a ranar 18 ga Yuli, sannan ta kara da Rosenborg a filin Lerkendal Stadium a ranar 24 ga Yuli.

    A ranar 1 ga Agusta a birnin Stockholm, United za ta yi wasa da Atletico Madrid a gasar Snapdragon Cup a filin Strawberry Arena, sannan bayan mako guda za ta kara da Paris Saint-Germain a birnin Gothenburg.

    Daraktan harkokin kwallon kafa na United, Jason Wilcox, ya shaida wa shafin kungiyar cewa:

    “Bayan sanar da wasanmu da Leeds a Dublin, muna farin cikin tabbatar da karin wasa hudu don shirin tunkarar kakar baɗi.

  8. Donnarumma na jin zafin rahoton sun nemi ladan wasan shiga kofin duniya, Fifa World Cup

    Mai tsaron ragar tawagar Italiya, Gianluigi Donnarumma, ya ce yana jin zafi sosai kan rahotannin da ke cewa ƴan wasa sun nemi a ba su lada idan sun samu tikitin shiga gasar FIFA World Cup ta bana.

    Italiya, wadda ta taba lashe kofin duniya sau hudu, ta kasa samun gurbin zuwa gasar karo na uku a jere bayan da ta sha kashi da ci 4-1 a bugun fenariti a hannun Bosnia and Herzegovina a wasan cike gurbi a watan da ya gabata.

    “A matsayina na kyaftin, ban taɓa zuwa neman ko euro guda daga hukumar ƙwallon kafar kasar ba,” in ji Donnarumma a hirar da ya yi da Sky Sports Italia.

    “Abin da ake yi a kullum shi ne, idan an samu tikitin shiga wata gasa, ana bai wa ƴan wasa kyauta ne kamar yadda aka saba.”

    Rashin samun tikitin shiga gasar kofin duniya ya sa shugaban hukumar ƙwallon kafar kasar, Gabriele Gravina, ya yi murabus sakamakon matsin lamba, yayin da tsohon mai tsaron raga Gianluigi Buffon ya sauka daga mukaminsa na shugaban tawagar.

    Haka kuma kocin tawagar, Gennaro Gattuso, ya bar aikinsa.

  9. Maguire na fatan Tuchel zai gayyace shi gasar kofin duniya 2026, Fifa World Cup 2026

    Harry Maguire na Manchester United na fatan za a saka shi cikin jerin ƴan wasa 26 da Thomas Tuchel zai je da tawagar Ingila, domin buga gasar cin kofin dunuya a bana.

    Ɗan wasan mai shekaru 33 ya ce har yanzu yana daga cikin fitattun masu tsaron baya a duniya duk da shekarunsa da suka ja.

    An bai wa Maguire goron gayyata a watan da ya gabata a wasannin sada zumunci tsakanin Ingila da Uruguay da kuma na Japan, wanda hakan ya zama dawowarsa ta farko cikin tawagar tun bayan shekarar 2024.

    Maguire na fuskantar kalubale wajen samu gurbi a tawagar daga ƴan wasa da suka haɗa da Ezri Konsa da Marc Guehi da John Stones da kuma Trevoh Chalobah. Sai dai ya bayyana cewa yana matuƙar son ya buga gasar, wadda za ta gudana daga 11 ga Yuni zuwa 19 ga Yuli.

    A kwanan nan, Maguire ya sabunta kwantiraginsa da United, wanda zai ci gaba da taka leda a Old Trafford har zuwa karshen kakar 2027, tare da damar ƙarin shekara guda.

    Tawagar Ingila na cikin rukuni a gasar kofin duniya da ya haɗa da Croatia da Ghana da kuma Panama. Za ta fara karawa da Croatia a ranar 17 ga watan Yuni a birnin Dallas.

  10. Ferran Torres ya buga wa Barcelona wasa na 200, Barcelona

    Ɗan wasan Barcelona, Ferran Tores ya buga karawa ta 200 a ƙungiyar a wasan da suka yi rashin nasara 2-0 a hannun Atletico Madrid a wasan farko zagayen kwata fainal a Champions League ranar Laraba a Camp Nou.

    Torres ya koma Barcelona ne a kakar 2021/2022, kuma ya zama muhimmin ɗan wasan ƙungiyar, saboda rawar da yake takawa.

    Tun bayan da ya koma Barcelona ɗan asalin Valencia an ci wasa 135 da shi da rashin nasara 24 ya shiga canji sau 41 da cin ƙwallo 60.

    Daga cikin wasa 200 da ya buga, 134 a gasar lig, 33 a Champions League, 17 a Copa del Rey da takwas a Europa League, sannan da wasu takwas a Spanish Super Cup.

    Mafi taka rawar Ferran Torres a matsayin ɗan Barça ya samu ne ƙarƙashin kocin yanzu Hansi Flick. A kakar da ta gabata, ya ci ƙwallo 19 a wasa 45, sannan a wannan kakar ma ya zura ƙwallo16 a cikin wasa 42 da ya buga ƙarƙashin kocin ɗan kasar Jamus.

    A matsayinsa na ɗan wasan Barça, Torres ya lashe kofuna shida: sau biyu na La Liga da uku a Spanish Super Cup, da kuma Copa del Rey ɗaya.

  11. AN TASHI WASA, Barcelona 0-2 Atletico Madrid

    Aikin gama ya gama!

    Atletico ta bi Barcelona ta doke har cikin tsakiyar gidanta Camp Nou, karon farko tun 2006.

    Sau biyu Atletico na yin waje da Barcelona a karawarsu biyu ta kifa ɗaya ƙwale a baya.

    Ga shi yanzu suna son su yi na uku.

  12. AN TASHI WASA, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Shi ke nan! PSG ta yi nasara a kan Liverpool hankali kwance.

    In ban da Allah ya kiyaye da ƙwallayen da za a ɗura wa Liverpool sai sun fi haka.

    Hari uku kacal Liverpool ta kai a yau, kuma cikin ukun babu wani mai kyau.

    Wannan ne karon farko da ta gaza kai farmakin cin ƙwallo a wasan Champions League tun bayan karawarta da Atalanta a Nuwamban 2020.

  13. VAR: BABU FENARITI, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Gaskiya yau Ibrahim Konate yana da sa'a.

    Duk da cewa Ibrahim Konate ya ɗan taɓa shi kaɗan amma bai kai a bayar da fenariti ba.

    Saboda haka babu fenariti.

  14. VAR na duba yiwuwar fenariti ga PSG, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Nuno Mendes ya sheƙo a guje da ƙwallo ta gefen hagu, ana tunanin Ibrahim Konate ya ture shi har ƙasa.

    Ana duba bidiyon VAR domin tantance gaskiya.

  15. An kusa tashi wasa!, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    An shiga minti uku na ƙarshe.

  16. , Barcelona 0-2 Atletico Madrid

    Yamal ya burge!

    Lamine Yamal ya shiga ya fita ta tsakankanin defendun Atletico amma a ƙarshe ƙwallon ta ƙwace masa.

    Kash!

  17. Ana ta canje-canjen ƴan wasa, Barcelona 0-2 Atletico Madrid

    Atletico Madris ta maye gurbi Guiliano Simeone da Nicolas Gonzalez, Thiago Almanda kuma ya maye gurbin Antoine Griezmann.

  18. ƘWALLO A RAGA: Barcelona 0-2 Atletico Madrid, Minti na 70

    Alexander Sorloth ya zura ƙwallo ta biyu a ragar Barca.

    Gaskiya Atletico sun shanye matsi sosai daga Barcelona bayan dawowa hutun rabin lokaci, amma lallai sun yi amfani da damarsu.

  19. VAR: BABU FENARITI, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Lafari Jose Maria Sanchez Martinez ya soke fenaritin da ya bayar da kuma katin gargaɗi da ya bai wa Ibrahim Konate.

    Ko haka zai bai wa Liverpool ƙwarin gwiwa?

  20. VAR, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Lafari ya je duba bidiyo domin tantance gaskiya