Ferran Torres ya buga wa Barcelona wasa na 200, Barcelona
Ɗan wasan Barcelona, Ferran Tores ya buga karawa ta 200 a ƙungiyar a wasan da suka yi rashin nasara 2-0 a hannun Atletico Madrid a wasan farko zagayen kwata fainal a Champions League ranar Laraba a Camp Nou.
Torres ya koma Barcelona ne a kakar 2021/2022, kuma ya zama muhimmin ɗan wasan ƙungiyar, saboda rawar da yake takawa.
Tun bayan da ya koma Barcelona ɗan asalin Valencia an ci wasa 135 da shi da rashin nasara 24 ya shiga canji sau 41 da cin ƙwallo 60.
Daga cikin wasa 200 da ya buga, 134 a gasar lig, 33 a Champions League, 17 a Copa del Rey da takwas a Europa League, sannan da wasu takwas a Spanish Super Cup.
Mafi taka rawar Ferran Torres a matsayin ɗan Barça ya samu ne ƙarƙashin kocin yanzu Hansi Flick. A kakar da ta gabata, ya ci ƙwallo 19 a wasa 45, sannan a wannan kakar ma ya zura ƙwallo16 a cikin wasa 42 da ya buga ƙarƙashin kocin ɗan kasar Jamus.
A matsayinsa na ɗan wasan Barça, Torres ya lashe kofuna shida: sau biyu na La Liga da uku a Spanish Super Cup, da kuma Copa del Rey ɗaya.