Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 29/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 29/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotonni

    Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Asabar, kafin mu zo da wasu rahotonnin gobe da safe.

  2. Hamɓararren shugaban Guinea Embalo ya isa Congo

    Jamhuriyar Congo ta ce hamɓararren shugaban ƙasar Guinea-Bissau, Umaro Sissocco Embaló, ya isa Brazzaville babban birnin ƙasar.

    Wata majiyar gwamnati ta ce ya isa Congon ne a cikin wani jirgi da aka yi shata daga Senegal.

    Sojojin da suka yi wa Mista Embaló juyin mulki a ranar Juma'a sun sake shi ne bayan shiga tsakani da ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas ta yi.

    Ecowas da Tarayyar Afirika sun yi Allah wadai da juyin mulkin, wanda suka ce koma-baya ne ga turbar dimokuraɗiyya.

    Ƙungiyoyin fararen hula sun zargi Embaló da kitsa abin da ya faru domin hana sanar da sakamakon zaɓen da aka yi a ƙasar, wanda suka ce yana tsoron shan kayi.

  3. Fafaroma Leo ya jagoranci ibada a babbar cocin Istanbul

    Fafaroma Leo ya halarci taron ibada a babbar cocin birnin Istanbul na Turkiyya, inda manyan limaman cocin suka tarbe shi.

    Wakiliyar BBC ta ce yana kira ga mabiya ɗarikar Katolikan Turkiyya su samar da yanayin haɗin kai tsakaninsu da Kiristoci da ma mabiya sauran addinai.

    A karon farko, babban limamin Katolikan ya kai ziyara ga Musulman Turkiyya a cikin masallaci.

  4. Ukraine ta kai wa jiragen ruwan Rasha hari

    Wani bidiyo da aka yaɗa ya nuna hare-haren da ake zargin dakarun Ukraine sun kai kan wasu tankokin mai biyu a tekun Bahar Aswad, waɗanda ake zargin na Rasha ne.

    An kai hare-haren ne a jiya Juma'a a wani lamari da kafafen yaɗa labaran Ukraine suka ce aikin haɗin gwiwa ne tsakanin sojin ƙasa da na ruwa. Babu dai rahoton ɓarnar da hare-haren suka yi.

    Tun da farko kamfanonin jigilar mai sun bayar da sanarwar dakatar da ayyukansu saboda harin da suke fama da shi tsakar dare a kan jiragen ruwa.

  5. Tinubu ya nemi tura ƙarin jakadu 32 zuwa ƙasashen waje

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya miƙa wa majalisar dattawa sunayen mutum 32 da yake son turawa a matsayin jakadun ƙasar zuwa ƙasashen waje.

    Wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a yau Asabar ta ce shugaban ya nemi majalisar ta gagaggauta tantancewa da amincewa da mutanen.

    Sunayen sun ƙunshi Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, da Reno Omokri, tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasa na musamman.

    A ranar Alhamis ne Tinubu ya nemi majalisar ta amince da tura jakadu zuwa Amurka da Ingila da Faransa.

    Fiye da shekara biyu kenan da gwamnatin APC ƙarƙashin Tinubu ta yi wa jakadun ƙasar kusan 109 kiranye kuma tun daga lokacin wakilai ne ke tafiyar da ofisoshin jakadancin Najeriya a ƙasashen waje.

  6. A kan cinyata Sheikh Dahiru Bauchi ya ja nimfashinsa na ƙarshe - Matar shehi

    Matar Sheikh Dahiru Bauchi, Hajiya Aisha, ta bayyana wa BBC yadda malamin ya yi numfashinsa na ƙarshe yana kwance a cinyarta.

    Sayyida Alayka kamar yadda mijinta ke kiranta, ta kuma bayyana rayuwar soyayya tsakaninsu irin wadda ba ku saba ji ba.

  7. Bikin karɓar mulki aka yi a Guinea-Bissau ba juyin mulki ba - Jonathan

    Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya siffanta juyin mulkin da aka yi a ƙasar Guinea-Bissau a matsayin "bikin karɓar mulki", ba na ƙwace mulki da ƙarfi ba.

    Jonathan ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai ranar Juma'a jim kaɗan bayan ya sauka a Abuja daga ƙasar da ya je sa ido kan zaɓen shugaban ƙasa.

    Ya ce lamarin da ya ƙunshi karɓe mulki a hannun Shugaba Umaro Mbalo, wanda yake takara a zaɓen, baƙon abu ne da ba a saba gani ba.

    "Ba zan kira abin da ya faru a Guinea-Bissau a matsayin juyin mulki ba," in ji shi. "Sai dai na ce bikin karɓar mulki ne saboda dalilai biyu.

    "Shugaba Mbalo ne ya sanar da juyin mulkin da kansa. Daga baya sojoji suka yi bayani cewa su ne ke da iko duk da cewa tuni Mbalo ya sanar da hakan, wanda baƙon abu ne.

    "Mbalo ya ci gaba da amfani da wayarsa a lokacin da juyin mulkin ke faruwa yana sanar da kafofin yaɗa labarai na duniya cewa an tsare shi. Daga baya kuma sai ga shi ya fice daga ƙasar."

  8. An kama wasu ƴan Afirka ta Kudu bisa yunƙurin zuwa Rasha don shiga yaƙin Ukraine

    Ƴansandan Afirka ta Kudu sun kama wasu mutum huɗu bisa zarginsu da yunƙurin tafiya Rasha domin shiga yaƙin da ƙasar ke yi da Ukraine

    Kakakin ƴansandan ƙasar ya ce an kama mutanen ne a babban filin jirgin sama na birnin Johannesburg, yayin da suke shirin hawa jirgi zuwa UAE kafin su wuce Rasha.

    Masu bincike sun ce wata mata ƴar Afirka ta Kudu ce ta shirya musu tafiyar da kuma yadda za a ɗauke su aikin soja a Rasha don shiga yaƙin.

    Ƴansandan sun ce za a gurfanar da mutanen a gaban kotu ranar Litinin, bisa zargin saɓa dokar shiga sojin wata ƙasar.

    Kamen na zuwa ne bayan da ƴargidan tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma ta yi murabus daga majalisar dokokin ƙasar, saboda zargin ta da taimaka wa wasu ƴanƙasar 17 zama sojojin hayar Rasha da suka shiga yaƙin Ukraine.

  9. Za a rufe sararin samaniyar Venezuela da kewaye - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce za a rufe ɗaukacin sararin samaniyar Venezuela da kewaye

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya gargaɗi duka kamfanonin jiragen sama da dillalan ƙwaya da masu safarar bil'adama.

    Tuni dai Amurka ta girke ƙaton jirgin dakon kayan yaƙi mafi girma a duniya a gaɓar ruwan ƙasar, tare da jibge dakaru 15,000 da za su iya ƙaddamar da hari cikin Venezuela.

    Amurka ta ce tana son yaƙar safarar ƙwayoyi a ƙasar.

    To amma gwamnatin Venezuela na kallon matakin a matsayin yunƙurin hambarar da Shugaba Nicolás Maduro, wanda madugun hamayyar ƙasar da ma wasu ƙasashen duniya suka ƙi amincewa da nasararsa a zaɓen shekarar da ta gabata.

  10. Ƙungiyoyin farar hula a Guinea-Bissau sun zargi shugaban ƙasar da kitsa juyin mulki

    Ana ci gaba da samun bayanai masu cin karo da juna game da juyin mulkin Guine-Bissau.

    Ƙungiyoyin fararen hula masu yawa a ƙasar sun zargi Shugaba, Umaro Sissoco Embaló da ''kitsa juyin mulkin'' ta hanyar taimakon sojojin ƙasar.

    Ƙungiyoyin sun ce ya yi hakan ne domin hana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen da ake tunanin ya sha kaye.

    Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, wanda ya jagoranci tawagar Ecowas domin sanya idanu a zaɓen, ya ce an kitsa juyin mulkin da gangan da nufin rutsa dimokraɗiyya.

    Mista Embaló bai ce komai ba game da waɗannan zarge-zarge.

    An bayyana labarin juyin mulki ne dai a lokacin da ake tsaka da tattara sakamakon zaɓen.

  11. Gwamnan Kano ya guji siyasantar da matsalar tsaron jiharmu - Barau

    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibril ya buƙaci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya guji siyasantar da matsalolin tsaron da jihar ke fuskanta, a maimakon haka ya mayar da hankali wajen magance ɗimbin matsalolin da ya ce na damun Kano.

    Cikin wata sanarwa da Sanata Barau ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, ya ce yana martani ne kan zargin da ya ce gwamnatin Kano ta yi masa na yin wasu kalamai da ka iya ta'azzara matsalar tsaron jihar.

    Sanarwar ta musanta iƙirarin gwamnatin, inda ta ƙalubalanci gwamnatin Kano ta bayyana sautin murya na inda Sanatan ya yi kalaman.

    Sanata Barau ya ce matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta ciki har da hare-haren ƴanbindiga a Kano a baya-bayan nan, na buƙatar haɗin kan kowa da aiki tare domin maganceta.

    "Abin mamaki ne yadda gwamnatin jihar Kano ke siyasantar da tsaro ta hanyar ƙirƙirar ƙarairayi domin ɓata wa mataimakin shugaban majalisar dattawa suna'', in ji sanarwar.

    ''Babu inda Sanata Barau ya furta wasu kalamai da ke zagon-ƙasa ga sha'anin tsaro a ƙasar nan, a maimakon haka ma a kullum yana kan gaba wajen samar da hanyoyin magance matsalar'', kamar yada sanarwar ta yi ƙarin haske.

  12. Sheikh Dahiru Bauchi ya auri ƴaƴan Sheikh Inyass har guda biyu

    A wata hira da BBC a baya marigayin ya ce, baya ga kasancewa almajirin Sheikh Ibrahim Inyass, akwai ƙarin dangantaka mai ƙarfi a tsakaninsu.

    Ya ce: ''Alhamdulillah baya ga zama almajirin Sheikh Ibrahim na kuma zama khadiminsa, kana na zama surukinsa, don na auri 'ya'yansa har sau biyu, na auri ɗaya bayan ta rasu ya sake bani auren ɗaya.''

    Kana malamin ya ce baya ga haka, yana ƙauna tare da mutunta malamai a ko ina suke, musamman malaman Tijjaniyya.

    ''Babu abin da ke faranta min rai irin na ga Musulunci ya bunƙasa, in ga darikar Tijjaniyya ta bunƙasa,'' in ji malamin.

  13. ADC ce kawai za ta ceto Najeriya - Atiku

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya ce jam'iyyar ADC ce kawai za ta iya ceto Najeriya daga halin da take ciki na matsalar tsaro da tattalin arziki.

    Yayin da yake jawabi a wurin taron ƙaddamar ofishin jam'iyyar a jihar Taraba a ranar Asabar, Atiku ya ce ya shiga jam'iyyun APC da PDP a baya kuma ya fahimci ba za su iya fitar da Najeriya daga halin da take ciki ba.

    A cikin makon nan ne dai tsohon ɗan takakarar shugaban ƙasar ya yanki katinsa na ADC, lamarin da ke alamta shigarsa jam'iyyar a hukumance.

    Atiku Abubakar ya kuma yi kira ga mutanen Taraba su fito su shiga jam'iyyar ta ADC, idan har suna son ''ceto tsaro da tattalin arzikin Najeriya''.

    ”Ina kira ga mata da matasa, su fahimci cewa muna yin wannan domin inganta makomarsu'', in ji Atiku.

  14. Mun rabu da mahaifinmu lafiya - Ƴaƴan Sheikh Dahiru Bauchi

    Yayin da ake ci gaba da alhinin rasuwar fitaccen malamin addinin musulucin nan na Najeriya, Sheikh Dahiru Bauchi, ƴaƴansa sun bayyana godiyarsu ga mutanen da suka halarci jana'izarsa.

    ''Alhamdulillahi mun rabu da mahifinmu lafiya, kuma muna fatan Allah ya sada shi da masoyinsa'', in ji Maryam wadda ta bayyana cikin sassanyar murya cike da alhini.

  15. Hare-haren Rashe sun jefa mutum 600,000 cikin rashin lantarki a Ukraine

    Jami'an Ukraine sun ce fiye da mutum 600,000 ne suka faɗa cikin halin rashin wutar lantarki bayan harin a Rasha ta kai ƙasar cikin daren da ya gabata.

    Ma'aikatar makamashin ƙasar ta ce fiye da mutum 500,000 cikin wannan adadi na zaune ne a Kyiv, babban birnin ƙasar.

    Ma'aikatar ta ce hare-haren sun faɗa ne kan tasoshin samar da lantarki na ƙasar da ke birnin da sauran yankunan ƙasar.

    Rahotonni sun ce kimanin makamai masu linzami 36 da jirage marasa matuƙa kusan 600 ne suka kai hare-hare a faɗin ƙasar, inda aka samu labarin mutuwar mutum uku da jikkata gommai.

    Rasha ta zafafa hare-hare kan wuraren fararen hula da tasoshin makamashi a Ukraine, duk kuwa ƙoƙarin Amurka na ganin an kawo ƙarshen yaƙin.

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta kai hare-hare kan cibiyar samar da makamai da tasoshin makamashin ƙasar.

  16. Kalli dandazon jama'a a lokacin jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

    Dubun dubatar al'umma ne suka halarci jana'izar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Dahiru Bauchi, da aka gudanar jiya.

    Ɗimbim mutane daga cikin da wajen Najeriya ne suka halarci jana'izar

  17. Hukumomin Katsina sun karɓo mutum 37 daga hannun ƴanbindiga bayan sulhu

    Hukumomin jihar Katsina sun sanar da karɓo wasu mutum 37 daga hannun ƴanbindiga bayan sulhu da aka yi tsakanin hukumomin jihar da ƴanbindigar.

    Mutanen sun ƙunshi maza 18 da mata 17 da ƙananan yara

    Hon. Abdurahman Ahmad Kandarawa shi ne ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Bakori a majalisar dokokin jihar, ya kuma shaida wa BBC cewa a yanzu babu sauran wani mutumin ƙaramar hukumar da ke hannun ƴanbindigar.

    Mutanen sun shafe fiye da wata guda a hannun masu garkuwa da mutanen.

    Ya ƙara da cewa karɓo mutanen na cikin ɓangaren yarjajeniyar zaman lafiyar da aka cimma a yankin, ba wai kudin fansa aka biya ba.

    Ɗan majalisar ya kuma yaba wa sulhun da ka yi da ƴanbindiga a yankin, yana mai cewa tun bayan cimma sulhun, ba a sake samun rahoton sace wani mutumin yankin ba.

  18. Firaministan Senegal ya soki juyin mulkin Guinea-Bissau

    Firaministan Senegel Ousmane Sanko ya bayyana juyin mulkin da aka yi a Guiene-Bissau a matsayin abin da bai dace ba.

    Mista Sanko ya buƙaci a ci gaba da bayar da damar tattara sakamakon zaɓe domin bayyana wanda ya yi nasara a zaɓen.

    Yayin da yake jawabi ga majalisar dokokin ƙasar a birnin Dhakar, Mista Sanko ya ce dole hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana wanda ya yi nasara a zaɓen.

    Tun kafin bayyana zaɓen shugaban ƙasar Omaru Sissico-Embalo ya tsere daga ƙasar, inda ya ce sojoji sun ƙwace mulkin ƙasar.

  19. Tsakaninmu da mutane sai godiya - Ƴaƴan Sheikh Dahiru Bauchi

    Yayin da ake ci gaba da alhinin rasuwar fitaccen malamin addinin musulucin nan na Najeriya, Sheikh Dahiru Bauchi, ƴaƴansa sun bayyana godiyarsu ga mutanen da suka halarci jana'izarsa.

    Yayin wata hira da ƴarsa, Maryam Dahiru Bauchi ta shaida wa BBC cewa babu abin da za su ce game da rasuwar mahaifinta sai godiyar Allah.

    ''Alhamdulillahi mun rabu da mahifinmu lafiya, kuma muna fatan Allah ya sada shi da masoyinsa'', in ji Maryam wadda ta bayyana cikin sassanyar murya cike da alhini.

    Maryam Dahiru Bauchi ta kuma gode wa ɗimbin al'ummar da suka halarci jana'izar mahaifin nata.

    ''Ba abin da za mu ce wa mutane sai godiya, da fatan Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya'', in ji ta.

    Dubun dubatar mutane ne daga ciki da wajen Najeriya ne suka halarci jana'izar fitaccen malamin addinin Musuluncin da ka gudanar a birnin Bauchi.

  20. AU ta dakatar da Guinea-Bissau bayan juyin mulki

    Ƙungiyar Tarayyar Afirka, AU ta sanar da dakatar da ƙasar Guinea-Bissau daga zama mamba a ƙungiyar bayan hamɓarar da shugaban ƙasar, Umaro Sissico-Embalo da sojoji suka yi.

    Shugaban Ƙungiyar Mahamoud Youssouf ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Juma'a.

    Matakin na AU na zuwa ne sa'o'i bayan ƙungiyar ECOWAS, ta dakatar da ƙasar saboda juyin mulkin.

    Ecowas ta ɗauki matakin dakatar da ƙasar ne a wani taro da ta gudanar a ranar Alhamis.

    Sojoji sun yi juyin mulki a ƙasar ne yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.