Sai da safe
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Juma'a.
Sai gobe da safe za mu zo da wasu rahotonnin a wani shafin daban.
Mu zama lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/12/2025.
Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida, da Umar Mikail
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Juma'a.
Sai gobe da safe za mu zo da wasu rahotonnin a wani shafin daban.
Mu zama lafiya.
Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta haramta kafawa da gudanar da ƙungiyar Hisbah Fisabilillahi da tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ke ƙoƙarin samarwa a ƙarƙashin gidauniyarsa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayar da haramcin cikin wani umarnin gwamna mai taken Executive Order 2025 a yau Juma'a, kamar yadda Kwamashinan Yaɗa Labarai Ibrahim Abdullahi Waiya ya shaida wa manema labarai.
Gwamnatin Kano ta ce yunƙurin kafa ƙungiyar "daidai yake da kafa wata hukumar tsaro da ka iya kawo wa zaman lafiyar al'umma barazana".
Da yake isar da saƙon gwamnan, Waiya ya jaddada cewa hukumar Hisbah da dokar majalisar dokokin Kano ta kafa ce kaɗai hukumar da ke da izinin gudanar da ayyukan da suka shafi Shari'ar Musulunci a jihar.
"Saɓa wa doka ne ga duk wani mutum ko ƙungiya ko rukunin wasu mutane su taru, su tattaro, horar da, ko aika wani mutum da zimmar aiwatar da wani aikin Hisbah ko wata ƙungiya mai kama da haka a jihar," a cewar umarnin.
"Saboda haka, daga yau duk wasu ayyukan Hisbah Fisabilillahi haramtattu ne," a cewar Kwamashina Waiya. "Gwamna ya bai wa 'yansanda umarnin daga yanzu duk wanda aka gani da kakin wannan ƙungiya a kama shi."
Hukumomi a ƙungiyar ƙasashe ta AES na ci gaba da tsare dakarun sojan Najeriya 11 da jirginsu ya yi saukar gaggawa a Burkina Faso, yayin da hukumomi ke cewa suna ci gaba da bincike.
"Muna ƙoƙarin kammala bincike game da abin da ya faru kafin mu ɗauki mataki na gaba," kamar yadda Daoud Aly Mohammedine, ministan tsaro na ƙasar Mali, ya shaida wa BBC.
Mohammedine ya ƙara da cewa: "Mun saka wa makaman tsare sararin samaniyarmu na ƙasashe AES ƙaimi. Yanzu mun tsara su ta yadda za su harbe duk wani jirgi da ya keta alfarmar sararin samaniyarmu."
A ranar Litinin ne jirgin sojan Najeriya C-130 ya yi saukar gaggawa a Bobo-Dioulasso. Wata sanarwa da gamayyar ƙasashen Burkina da Mali da Nijar suka fitar ta ce bincikensu ya nuna jirgin ya keta alfarmar samaniyarsu.
Lamarin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun rashin jituwa tsakanin ƙasashen AES da ƙasashen Ecowas, wadda Najeriya jigo ce a cikinta.
Birtaniya ta haramta wa wasu manyan kwamandojin kungiyar RSF ta Sudan shiga kasar, waɗanda ake zargi sun aikata munanan laifuka a birnin El-Fasher, tare da kwace kadarorinsu.
Mutanen sun haɗa da mataimakin shugaban RSF, Abdul Rahim Hamdan Dagalo, da wasu kwamandoji uku.
Laifukan da ake zargin su da aikatawa sun haɗa da kisan gwamman mutane, da kuma cin zarafi ta hanyar lalata.
Birtaniya ta ce shaidun da aka samu sun tabbatar ana barin mutane da yunwa, wasu kuma a yi musu fyade, wanda abu ne mai matuƙar tayar da hankali, kuma tana duba yiwuwar ƙaƙaba musu ƙarin takunkumai.
Birtaniya ta kuma ce za ta bayar da tallafin dala miliyan 28 domin samar da kayan tallafi, sannan a kare mata da yara, wadanda lamarin ya fi shafa.
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce ta kafa kwamatoci na riƙon ƙwarya da za su kula da shugaancin jam'iyyar a jihohin Enugu da Delta da Rivers - dukkansu a kudancin ƙasar.
Wata sanarwa da ta fitar a yammacin yau Juma'a, PDP ta ce kwamatin gudanarwa ne ya amince da kwamatocin riƙon bisa tanadin sashe na 29(2)(b) na tsarin mulkin jam'iyyar na 2025 da aka yi wa kwaskarima.
Zaɓukan shugabanci a jihohin kudu maso kudu na cikin abubuwan da suka ƙara jawo ruɗani a cikin jam'iyar, inda ɓangaren Ministan Abuja Nyesom Wike ke zargin an yi wa waɗanda suke goya wa baya ƙarfa-ƙarfa bayan sun cei zaɓen ta hanyar soke shi.
"Kwamatocin za su ɗauki ragamar shugabancin jam'iyyar a jihohinsu na tsawon abin da bai wuce kwana 90 ba...ko kuma zuwa lokacin da za a zaɓi sababbin shugabanni," a cewar sanarwar ta PDP.
A ƙarshen watan Nuwamba aka zaɓi sababbin shugabannin jam'iyyar na ƙasa, wadda a yanzu Kabiru Tanimu Turaki ke jagoranta a matsayin shugaba.
Gwamnatin jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya ta tabbatar da mutuwar Mataimakin Gwamna Lawrence Ewhrudjakpo.
Mista Ewhrudjakpo ya rasu ranar Alhamis bayan ya yanke jiki ya faɗi a ofishinsa, inda aka garzaya da shi asibiti a Yenagoa babban birnin jihar.
Kwamashinar yaɗa labarai ta Bayelsa ta bayyana mutuwar a matsayin "mai girgiza zuciya" cikin wata sanarwa.
"Gwmanatin Bayelsa na sanar da rasuwar Mataimakin Gwamna Sanata Lawrence Ewhrudjakpo ranar Alhamis, 11 ga watan Disamba yana da shekara 60 da haihuwa," in ji Kwamashina Ebiuwou Koku-Obiyai.
Ta ƙara da cewa Gwamna Douye Diri ya ayyana makokin kwana uku a jihar, da bayar da umarnin sassauto da tuta a matsayin girmamawa ga mamacin.
Ana sa ran Shugaba Trump zai tattauna da shugabannin Thailand da Cambodia nan ba da jimawa ba, domin ƙoƙarin ƙarfafa yarjejeniyar zaman lafiyar da ya tsara.
Wata biyar da suka gabata ne shugabannin ƙasashen biyu suka amince da yarjejeniyar tsagaita wuta bayan karon farko na kai wa juna hare-hare.
An shiga kwana na biyar kenan na rikicin kan iyaka tsakanin sojojin ɓangarorin biyu, wanda ya yi ajalin mutum akalla 20, da kuma raba mutum kusan 500,000 da muhallansu a ƙasashen biyu.
Kafin tattaunawar tasu ta wayar tarho, ministan harkokin wajen Thailand ya bai wa sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio tabbacin cewa kasarsa a shirye take a samu zaman lafiya a rikicin.
Jamus ta gayyaci jakadan Rasha a Berlin kan abin da ta kira yawaitar abubuwan barazana gare ta, ciki har da gangamin yada labaran bogi
Gwamnatin ƙasar ta kuma zargi Rasha da ayyukan leken asiri, da yunƙurin yi wa ƙasar zagon kasa.
Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta ce ta gano yunkurin yi musu kutse ta intanet sau biyu daga Rasha. Ta ce na farkon an yi shi ne kan na'urorin masu kula da jiragen sama a shekarar da ta gabata.
Na biyun kuma ma'aikatar ta ce an yi yunkurin kawo cikas ga babban zaben watan Fabrairu.
Wakiliyar BBC ta ce ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta ce da gangan Rasha ke yi wa tsaron kasar barazana.
Ƴansanda a Ethiopian sun kama wasu matasa uku da suka shahara a shafin TikTok a bisa zargin amfani da shafin ta hanyoyin da hukumomi suka ce sun saɓa al’adun al’ummar ƙasar.
Wannan na zuwa ne a lokacin da ake ƙorafi kan yadda hukumomi ke ci gaba da ƙoƙarin rufe bakin masu amfani da shafukan sada zumunta.Ƴansanda sun ce suna tsare da Goyghar Kot, da Helile Gibo da kuma Baharudin Mussema a bisa zargin yaɗa saƙonni da hotuna da suka yi hannun riga da al’adu da mutumtakar al’umma.
Hukumomi sun ce biyu daga cikin waɗanda aka kaman sun yi amfani da TikTok wajen yaɗa baɗala kai tsaye.
Kamen na baya-bayan nan ya zo ne kwana shida kacal bayan ƴansanda sun kama wasu fitattu a shafukan sada zumunta har su shida, a bisa abinda hukumomin ƙasar suka kira ayyukan rashin mutumci, saboda sun sanya tufafi masu bayyana tsiraici a yayin wani taron karrama ƴan TikTok a birnin Addis Ababa.
Daga cikin mutanen da aka kama harda Adonay Berhane mai shekara 25, wanda ya shahara wajen tallar kayan ado da kwalliya, kuma mai mabiya aƙalla miliyan hudu a shafukan sada zumunta.
Shi ne kuma aka bai wa kyautar gwarzon ɗan TikTok na 2025 a Ethiopia, a wajen taron da ya janyo dambarwar da suke ciki yanzu.
Akwai kuma Wongelawit Gebre Endrias, wadda aka fi sani da Evan, mai wallafa bidiyon ado da kwalliya a TikTok, da aka kama saboda yadda ta bayyana sanye da kwat, amma babu riga a ciki, kuma ana iya ganin sassan ƙirjinta.
Kama matasan dai ya janyo muhawara mai zafi a shafukan sada zumunta a Ethiopia.Masu goyon bayan su na ganin cewa an tauye ƴancin su na gudanar da rayuwa yadda suke so, yayin da masu suka ke cewa ƴansandan sun yi daidai a ƙoƙarin su na kare al’ada da mutumcin al’ummar ƙasar.
Gwamnatin Ethiopia dai ba ta ce komai ba a kan batun, amma ƴansanda sun ce sun ɗauki matakin ne domin hana su gurɓata tarbiyyar ɗinbin matasan da ke bibiyarsu a TikTok
Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, ya tabbatar da fashewar da ta faru a ranar Laraba a wasu al’ummomi biyu da ke kusa da masarautar Gbaramatu ta jihar Delta mai arziƙin mai.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis da yamma, ya ce har yanzu ba a gano musabbabin fashewar ba, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.
NNPC ba ta bayyana adadin lalacewar da ta faru ko asarar rayuka.
Kamfanin ya ce an ƙaddamar da matakan gaggawa tare da haɗa kai da hukumomin tsaro da shugabannin al’umma domin ɗaukar matakan da suka dace.
“Abu mafi muhimmanci a wannan lokaci shi ne kare rayukan al’ummomin da ke kusa da wurin da kuma kiyaye muhalli,” in ji jami’in hulda da jama’a na NNPC, Andy Odeh.
NNPC ta bayyana cewa an gano raguwar ƙarfi a daya daga cikin manyan bututunta, wanda ke nuna yiwuwar fitar mai, lamarin da ya sa aka fara binciken farko.
Fashewar bututun mai ba sabon abu ba ne a Najeriya, inda kungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ko masu satar mai ke yawan lalata bututun domin sace man fetur.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirin ɗaukar sama da jami’an tsaro 90,000 a wani sabon mataki na ƙarfafa yaki da matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar ƙasar.
A ƙarƙashin wannan tsarin, hukumar ƴansandan Najeriya (NPF) za ta ɗauki ’yan sanda 50,000 ƙarin da za a haɗa da adadin da ake da shi yanzu.
Za a buɗe kafar ɗaukar aikin daga ranar 15 ga wannan wata na Disamban zuwa 25 ga watan Janairun 2026.
Wannan mataki ya biyo bayan wani shiri da gwamnatin ta soma tun farko na ɗaukar jami’an tsaro 30,000, waɗanda suka haɗa da ma’aikatan gidajen gyaran hali, ma’aikatan kula da iyakoki (Immigration), da wasu sassan tsaro daban-daban.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ta ƙara ta’azzara a sassan Najeriya
Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda bisa samunta da laifin kashe mijinta Bilyaminun Bello.
Alƙalan kotun guda huɗu a cikin biyar ne suka tabbatar hukuncin, inda ake yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan watsi da ɗaukaka ƙararta, kamar yadda mai shari'a Moore Adumein ne ya sanar da hukuncin a madadin sauran alƙalan.
Kotun ta ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi rangwame ga Maryam alhalin ana ci gaba da sauraron shari'arta a gaban kotun ɗaukaka ƙara, kamar yadda tashar Channles ta ruwaito.
A ranar 27 ga watan Janairun 2020 ne kotu a Abuja ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin da kashe mijinta Bilyaminu Bello a gidansu na Abuja shekarar 2017.
Najeriya da Cote d'Ivoire sun tura kimanin sojoji 200 zuwa Jamhuriyar Benin, bayan yunkurin juyin mulkin da ya faru a ranar 7 ga Disamba, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.
Ko da yake ECOWAS ba ta bayyana adadin sojojin da ta tura ba, ƙungiyar ta ce Ghana da Saliyo ma za su ba da dakaru a matsayin wani ɓangare na tsarin rundunar tsaron gaggawa da ta tanada.
Da yake jawabi a taron manema labarai a Abuja a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen Benin, Olushegun Adjadi Bakari, ya ce: “A halin yanzu akwai kusan sojoji 200 da suka isa domin taimaka wa rundunar tsaron Benin a matsayin sharar fage domin wanzar da zaman lafiya.”
Ya ƙara da cewa an shawo kan yunkurin juyin mulkin tun kafin neman goyon bayan ECOWAS.
A nasa ɓangaren, ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa haɗin gwiwar difilomasiyya da soji da bayanan sirri tsakanin Najeriya da Benin ne ya taimaka wajen dakile juyin mulkin.
Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje sun nuna cewa shugaban juyin mulkin, Pascal Tigri, tare da abokan aikinsa, sun tsere ne zuwa ƙasar Togo.
Wata babbar kotun tarayya mai zamanta da ke babban birnin tarayya Abuja ta tura tsohon ministan ƙwadago Chris Ngige gidan yarin Kuje.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ce ta gurfanar da tsohon ministan a gaban mai shari’a Mariam Hassan bisa tuhume-tuhume guda takwas da suka danganci cin hanci da rashawa.
Ngige, wanda ya kasance minista a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya isa harabar kotun ne da misalin ƙarfe 8:10 na safiyar yau Juma'a tare da rakiyar jami’an EFCC.
Hukumar ta zargi Ngige da aikata laifukan ne a lokacin da yake minista, musamman a lokacin da yake kula da hukumar bayar da tallafi ta Najeriya wato NSITF.
A tuhuma ta farko, ana zargin cewa daga Satumban 2015 zuwa Mayun 2023, Ngige ya yi amfani da matsayinsa a lokacin wajen bai wa abokansa kwangila ba bisa ƙa’ida.
Sai dai a zaman kotun, tsohon ministan ya musanta laifukan da ake tuhumarsa da su.
Mai shari'a Mariam ta ɗage shari'ar zuwa Litinin domin sauraron buƙatar neman belinsa, sannan ta bayar da umarni a tsare shi a gidan yarin Kuje har zuwa ranar.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya ce har yanzu sojojin Najeriya 11 na maƙale a ƙasar Burkina Faso bayan saukar gaggawa da wani jirgi da suke ciki ya yi a ƙasar.
Rahoton ya ce lamarin ya faru ne tun ranar 8 ga Disamba, lokacin da jirgin ya yi saukar gaggawa a ƙasar inda ƙungiyar ƙasashen Sahel (AES) ta zargi jirgin sojin Najeriya da keta sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izini ba.
A cewar rahoton, shugaban gwamnatin soji ta Mali, Assimi Goïta, ya bayyana saukar jirgin a matsayin matakin da ya saɓa wa ƙa'idojin ƙasashen duniya
Rundunar Sojin Saman Najeriya kuwa ta ce jirgin yana kan hanyarsa ce ta zuwa ƙasar Portugal lokacin da ya samu tangarɗar na'urar da ta tilasta masa yin saukar gaggawa a ƙasar.
Kungiyar AES – ta ƙunshi ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar wadanda suka fice daga ƙungiyar ECOWAS a watan Janairu, bayan takunkuman da aka sanya musu sakamakon juyin mulki a ƙasashensu.
Sun sanar da ficewarsu daga ƙungiyar ne a daidai lokacin da Najeriya ke jagorantar ECOWAS.
Yunkurin tsohon gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, na kafa wata kungiyar Hisbah mai zaman kanta na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, inda wasu daga cikin ’yan siyasa da al’umma ke barazanar kai maganar gaban kotu
Masu sukar tsarin na ganin cewa yunƙurin na iya janyo tashin hankali, duba da yadda ake fassara ikon rundunar Hisbah a Kano a matsayin wanda doka ta tanada.
Tsohon ɗan takarar gwamna, Ibrahim Al-Amin Little, ya kasance cikin masu adawa da shirin, inda ya gargaɗi Ganduje da ya janye wannan batu na kafa Hibah mai zaman kanta.
Ya ce kafa irin wannan ƙungiya zai buɗe ƙofa ga wasu su fara ƙirƙiro nasu, lamarin da zai iya rikitar da harkokin tsaro.
“A matsayina na ƙaninsa, nake ankarar da shi da ba shi shawarar ya janye maganar kafa Hibah mai zaman kanta idan kuwa ba haka ba mu na da niyyar zuwa kotu domin tantance ko yana da hurumin yin haka,” in ji Little.
Ya kara da cewa doka ce ta kafa Hisbah ta yanzu, kuma tana da ikon kamawa da miƙa masu laifi ga hukuma.
Sai dai ɓangaren Ganduje ya musanta zargin cewa tsarin zai iya haifar da fitina, kamar yadda tsohon kwamishinan yaɗa labarai a Kano, Muhammad Garba ya bayyana, yana cewa jama’a ne ba su fahimci abin da ake ƙoƙarin yi ba.
"Ƴan hisban da suka yi aiki a loacin tsohon gwamna Ganduje ne wanda gwamnatin yanzu ta rusa, waɗannan mutanen ne suka zo suka nemi taimakon tsohon gwamna domin su ci gaba da ayyukan agaji da na addini da suka saba,” in ji shi.
Rahotanni sun nuna cewa an riga an fara nema da cike fom na shiga ƙungiyar, tare da taron ƙaddamarwa da ya ja ɗimbin mutane daga kananan hukumomi 44 na jihar, inda suka nuna goyon bayansu ga sabon tsarin da bangaren Ganduje ya fito da shi.
Amurka ta sanya takunkumi a kan wasu jiragen ruwa shida da ta ce suna satar fitar da man Venezuela, haka kuma takunkumin ya shafi karin wasu daidaikun mutane da ke da alaka da Shugaba Nicolas Maduro.
Amurka ta dauki matakin ne kwana daya bayan ta kwace wani jirgin ruwa na dakon mai a gabar tekun Venezuelar. Kuma tuni fadar gwamnatin Amurkar ta ce za ta kwashe man da ke cikin jirgin.
Yayin da yake ci gaba da matsin lamba a kan Shugaba Maduro Trump ya nuna alamun cewa nan gaba kadan Amurka za ta fara kai hari kan mutanen da take zargi na safarar miyagun kwayoyi ta kasa.
Wakiliyar BBC ta ce shugaba na Venezuela ya ce, ainahin burin shugaba Trump shi ne sauyin gwamnati, yana son kawar da shi ne daga mulki
Jam'iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa Sanata Lawrence Ewhrudjakpo.
Da farko an fara raɗe-raɗin cewa ɗan siyasar ya yanke jiki ya faɗi ne a jiya Alhamis, sannan aka kai shi babban asibitin tarayya da ke birnin Yenegoa.
A wata sanarwa da PDP ta fitar, ta ce ta samu labarin mutuwar mataimakin gwamnan ne a ranar Alhamis 11 ga watan Disamba.
"Sanata Ewhrudjakpo jajirtaccen ɗan siyasa ne mai gaskiya wanda yake ƙoƙari wajen bin doka."
An haife hi ne a garin Ofoni da ke ƙaramar hukumar Sagbama ta jihar watan Satumban shekarar 1965, kuma ya rasu ne yana da shekara 60 a duniya.
Shugaba Zelensky na Ukrine ya ce babban abin takaddama tsakaninsa da Amurka shi ne yadda za a kawo karshen yaki da Rasha, shi ne har yanzu kan yadda makomar wani yankin gabashin kasar zai kasance.
Ya ce Amurka ta shirya cewa dakarun Ukraine su janye daga yankin Donetsk, ba tare da tlisata wa Rasha ita ma ta janye ba.
Shugaban ya ce abu na biyu kuma da suke ja-in-ja da shi ne shirin hadaka na tafiyar da tashar nukiliya mai muhimmanci ta Zaporizhzhia - wadda a yanzu Rasha ta mamaye.
Zelensky ya ce mun aikawa tawagar ta Amrka, daftarin da muka sabunta da yarjejeniyar. Shugaba Trump ya jaddda cewa yana duba yuwuwar tura wakili domin ganawa da shugabannin Turai a gobe Asabar amma ya ce zai yi hakan ne kawai idan da yuwuwar cimma yarjejeniya.
Jama'a barkamu da wannan safiya ta ranar Juma'a, barkanmu da sake saduwa a wannan shafin namu na labaran kai-tsaye.
A yau ma za mu ɗaura daga inda muka tsaya a jiya Alhamis wajen kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na Whattsapp da Facebook da X da Instagram domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da ma tafka muhawara.
Ku kasance tare a mu.