Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 12/06/2024

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonni abubuwan da ke faruwa a sassa daban-daban na duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Babbar jam'iyyar hamayya a Faransa ta tsige shugabanta

    Babbar jamiyyar masu matsakaicin ra'ayin riƙau, wadda ke hamayya a Faransa, ta ce ta tsige shugabanta, bayan da ya bayar da shawarar yin haɗaka da jam'iyyar masu tsananin ra'ayin riƙau, a zaɓen da za a yi a Faransar a karshen wannan watan na Yuni.

    Matakin jagoran, Eric Ciotti ya fusata da dama daga cikin manyan jamiyyar tasu ta Republican, abin da ya kai ga an kaɗa ƙuri'ar tsigeshi.

    Sai dai ya yi watsi da wannan matsayi nasu, tare da jadadda cewa shi ne jagoransu har yanzu.

    Kafin wannan lokaci,Shugaban Emmanuel Macron, ya yi kira ga masu matsakaitan ra'ayi su bashi haɗin-kai wajen kawar da masu tsananin ra'ayin riƙau da ra'ayin kawo sauyi.

    Mista Macron ya kare matakin da ya ɗauka na kira a gudanar da zaɓe cikin gaggawa, bayan masu ra'ayin riƙau sun samu gagarumin rinjaye a zaɓen majalisar Turai da aka gudanar a ranar Lahadi.

  3. Jiragen sojin ruwan Rasha sun yi atisaye a ƙasar Cuba

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu jiragen sojin ruwan Rasha sun isa birnin Havana na Cuba, a wani yanayi da ake ganin ƙoƙarin nuna ƙarfi ne, yayinda ake sake shiga tashin hankali tsakanin Rasha da ƙasashen Yamma kan yaƙin Ukraine.

    Tashar jirgin ruwan na da tazarar kilomita 160 daga tashar jiragen ruwan sojin Amurka da ke florida.

    Jami'an Amurka sun ce suna sa ido da bibbiyar komai sannan hakan ba wani abin barazana ba ne a garesu.

    Jiragen da suka haɗa da ƙaramin jirgin yaƙi da jirgin ƙarƙashin teku mai amfani da makamashin nukiliya, sun gudanar da atisaye a tekun Atlantic har zuwa mashigar tsibirin Caribbean.

  4. Binciken BBC ya gano yadda Iran da UAE ke kai agajin makamai Sudan

    Wani binciken sashen Larabci na BBC ya gano shaidu da ke nuna yadda ɓangarorin da ke rikici da juna a Sudan ke samun makamai daga Iran da kuma Hadaddiyar Daular Labarabawa, duk da takunkumin MDD kan shigar da makamai ƙasar.

    Hotunan bidiyo sun nuna yadda dakarun gwamnatin Sudan ke samun bindigogi daga wajen Iran, da kuma yadda jiragen Iran ke zuwa gaɓar teku a Sudan domin kai musu makamai da kayan yaki.

    Binciken na BBC ya kuma gano hotunan bidiyo da ke tabbatar da cewa ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa na taimakawa dakarun RSF.

    Sai dai Daular Larabawar da gwamnatin Sudan sun musanta wannan zargi.

  5. 'Sabon kuɗin da Emefiele ya sauya ba shi Buhari ya sahale ba'

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon darakta kuɗi na Babban Bankin Najeriya, CBN, Ahmed Bello Umar, ya ce sabon kuɗin da aka sauya wa fasali da tsohon gwamnan Bankin, Godwin Emefiele ya gabatar a ƙarshen shekarar 2022, ba shi ne ainihin sabon fasalin da tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya amince masa ba.

    Yayin da yake bayar da shaida a gaban kotu ranar Talata kan shari'ar da ake yi wa tsohon gwamnan Bankin, tsohon daraktan kuɗin ya ce mista Emefiele bai yi amfani da fasalin da shugaan ƙasar ya amince da shi ba.

    Ya faɗa wa kotun cewa akwai bambanci mai yawan gaske tsakanin fasalin takardun kuɗin da tsohon shugaban ya sahale da kuma wanda Emefiele ya buga.

    A ƙarshen shekarar 2022 ne dai tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari, ya amince da sauya fasalin kuɗin ƙasar, wani abu da ya janyo ce-ce-ku-ce mai tarin yawa a ƙasar.

    Sakamakon yadda gwamnati ta sanya wa'adin daina amfani da tsoffin takardun kuɗin, wani abu da ya jefa al'ummar ƙasar cikin fargabar tafka asara.

    To sai dai bayan shigar da ƙara da wasu gwamnonin ƙasar suka yi, Kotun ƙolin ƙasar ta tsawaita wa'adin da shekara guda, inda daga baya kuma ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da kuɗin har zuwa abin da hali ya yi.

  6. Fiye da mutum 80 sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a DR Kongo

    ...

    Asalin hoton, others

    Fiye da mutum 80 ne suka mutu a lokacin da wani kwale-kwale ya kife a kusa da Kinshasa babban birnin kasar Kongo cikin daren da ya gabata.

    Shugaban ƙasar, Felix Tshisekedi ya ce kwale-kwalen na ɗauke da fiye da mutum 100 a lokacin da lamarin ya auku a kogin Kwa da ke kai ruwa babban kogin Kongo.

    Shugaba Tshisekedi ya buƙaci a gudanar da bincike domin gano musabbanin faruwar lamarin.

    Rahotonnin farko, sun nuna cewa matsalar inji ne ya haddasa hatsarin, lamarin da ya sa jirgin ya rabe a lokacin da bugi gaɓar kogin.

    Wannan shi ne hatsarin kwale-kwale na baya-bayan nan a ƙasar da ke yankin tsakiyar Afirka, inda ake maƙare jiragen ruwa da fasinjojin da suka wuce ƙima.

    Tuƙa kwale-kwale cikin dare abu ne da aka haramta a ƙasar, musamman waɗanda aka ƙera da katako.

  7. Amurka da Ukraine za su ƙulla sabuwar yarjejeniyar tsaro

    Amurka da Ukraine za su sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar tsaro ranar Alhamis a lokacin wata ganawa da shugabannin ƙasashen biyu za su yi a Italiya.

    Shugaba Biden da takwaransa Zelensky za su sanya hannun a gefen taron ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin masana'antu ta G7 da za a yi a birnin Fasano na ƙasar Italiya.

    Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro, Jake Sullivan ya ce Amurka za ta alƙawarta ci gaba da tallafa wa Ukriane har na tsawon dogon zango a yaƙin da take yi da Rasha.

    Sabuwar yarjejeniyar na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta bayyana sanya wa kamfanonin da ke tallafa wa Rasha sabbin takunkumai.

    Ma'aikatar baitul-malin Amurka da ma'aikatar tsaron ƙasar sun sanya takunkumai kan kamfanoni da ɗaiɗaikun mutanen Rasha fiye da 300, ciki har da kamfanin musayar kuɗi na Moscow.

  8. Hajji 2024: Fiye da maniyyata miliyan ɗaya da rabi ne za su sauke farali

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin Saudiyya sun ce fiye da mutum miliyan ɗaya da rabi ne suka isa ƙasar, daga sassan duniya daban-daban domin gudanar da akin hajjin bana.

    Jaridar Saudi Gazzet, ta ruwaito babban daraktan ofishin kula da bayar da biza na ƙasar, na cewa maniyyata miliyan 1,547,295 ne suka isa ƙasar ta sama da kan iyakokin ƙasa da kuma tasoshin jiragen ruwa.

    Ya ƙara da cewa maniyyata miliyan 1,483,312 ne suka shiga ƙasar ta jiragen sama, yayin dan mutum 59,273 suka shiga ƙasar ta kan iyakokin ƙasa, sai kuma maniyyata 4,710 da suka je ta jiragen ruwa.

    A ranar Juma'a 8 ga watan Dhul-Hijja ne za a fara gudanar da aikin Hajji na wannan shekarar.

  9. Gomman mutane sun mutu bayan gobara ta tashi a wani gini a Kuwait

    Kuwait

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Hoton inda gobarar ta tashi

    Ministan cikin gida na Kuwaita ya ce aƙalla mutum 49 ne suka mutu, bayan gobara ta tashi a wani gida a birnin Mangaf da ke ƙasar.

    Gobarar - wadda ta tashi da misalin ƙarfe 6:00 na safe agogon ƙasar - a yanzu an shawo kanta

    Bidiyoyin da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda baƙin hayaƙi ya turnuƙe wani ɓangare na ginin.

    Rahotonni na cewa mafi yawan waɗanda suka mutu, 'yan ƙasashen waje ne da ke aiki a ƙasar, ciki har da Indiyawa masu yawa.

    Mataimakin fimininstan ƙasar, Sheikh Fahad Yusuf al-Sabah ya ɗora alhaƙin gobarar kan waɗanda suka mallaki ginin, yana mai cewa saɓawa ƙa'idar gine-gine ce ta haifar da bala'in.

    "Abin takaici, son kai daga ɓangaren waɗanda suka mallaki ginin ne ya haddasa wannan bala'i,'' kamar yadda Sheikh al-Sabah - wanda kuma shi ne mai riƙon muƙamin ministan cikin gida na ƙasar - ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    "Sun saɓa wa ƙa'ida, kuma wannan shi ne alhakin saɓa ƙa'ida."

  10. Shettima ya buƙaci likitocin Najeriya su taimaka wajen inganta ƙasar

    Mataimakin shugaban Najeriya

    Asalin hoton, Kashim Shettima/X

    Bayanan hoto, Kashim Shettima ya koka kan yadda likitocin ƙasar ke yawan ficewa zuwa ƙasashen ƙetare

    Mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima ya yi kira ga likitocin ƙasar, su riƙa zama a ƙasar, don taimaka wa magance matsalar da ƙasar ke fuskanta ta ƙarancin likitoci.

    Shettima ya yi kiran ne a lokacin da ƙungiyar likitocin ƙasar - ƙarƙashin jagorancin sabon shugabanta, Farfesa Bala Audu - suka kai masa ziyara a ofishinsa ranar Talata.

    Mataimakin shugaban ƙasar ya nuna damuwa kan yadda likitocin ƙasar ke yawan ficewa daga ƙasar domin neman ayyuka a ƙasashen waje.

    A baya-bayan nan dai ana samun yawaitar ficewar likitocin Najeriya daga ƙasar, zuwa ƙasashen wajen domin samun ingantaccen albashi da yanayin aikin mai kyau.

    Sai dai mataimakin shugaban ƙasar, ya jaddada cewa gwamnatinsu na iya bakin ƙoƙarinsu wajen inganta yanayin aikin likitoci a ƙasar, musamman waɗanda suka zaɓi tsayawa su yi aiki a ƙasar.

    “Likitocin Najeriya na cikin zuciyar shugaba Bola Ahmed Tinubu. Akwai abubuwa da dama da ya yi musu tanadi, musamman ga waɗanda suka zaɓi tsayawa su yi aiki a ƙasarsu,'' in ji Shettima.

  11. Hajji 2024: Saudiyya ta ƙaddamar da na'urar amsa fatawa ga maniyyata

    ..

    Asalin hoton, Haramain/X

    Ƙasar Saudiyya ta ƙaddamar da na'urorin amsa fatawa ga masu ibada a masallatan harami.

    Na'urorin za su riƙa amsa tambayoyin da ke da nasaba da shari'a da dokokin addinin musulunci.

    Shafin X na Haramain ya ce an girke na'urori a harabobin masallatan harami domin bayar da fatawa ga maniyyata a lokacin aikin hajjin bana.

    Masu buƙatar fatawa za su kusanci na'urorin domin tambayar abin da ya shige musu duhu, inda su kuma na'urorin za su sada su da wani malami da zai amsa tambayar nan take.

    Na'urorin na karɓar fatawa da amsa ta cikin harsunan duniya 11, kamar yadda shafin Haramain ya bayyana

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. Ana fama da tsananin zafi a Saudiyya yayin da ake shirye-shiryen fara aikin hajji

    .
    Bayanan hoto, Maniyyata

    Yayin da ake shirye-shiryen soma aikin hajji gadan-gadan a ƙasar Saudiyya, ana nuna damuwa kan yadda yanayin zafi ke ƙaruwa a birnin Makka da kewaye inda ake gudanar da ibadar ta hajji.

    Maniyyata

    Hakan na zuwa ne yayin da dubun dubatar Musulmi ke ci gaba da kwarara zuwa birnin mai tsarki gabanin somawar aikace-aikacen hajji a ranar Jumu’a.

    Maniyyata

    Hukumomin ƙasar kan yi tanadin na'urorin da za su taimaka wa maniyyata wajen rage zafin da suke fuskanta.

    Maniyyata

    Fiye da mutum miliyan 1.3 ne za su gabatar da aikin hajji a wannan shekara

  13. Emre Can ya maye gurbin Pavlovic a tawagar Jamus a Euro 2024

  14. Shugaban Senegal ya alƙawarta gina ƙasar, yayin da aka fara tono man fetur

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, A watan Afrilu ne aka zaɓi Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban Senegal

    Shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya ce ƙasar za ta yi amfani da ribar da za ta samu daga cinikin man fetur da aka fara tonowa wajen gina ƙasar.

    Hakan na zuwa ne bayan da ƙasar da ke yammacin Afirka ta fara tono man fetur karon farko a tarihi.

    Fitaccen kamfanin makamashi na Australian ''Woodside'' ya bayyana tono man a matsayin ''ranar tarihi'' kuma wani abun ci gaba ga kamfanin da kuma Senegal.

    Shirin tono man da aka yi wa laƙabi da ''Sangamor'', wanda ya haɗa da iskar gas, na da niyyar tono gangar man fetur 100,000 a kowace rana.

    Ana sa ran shirin zai samar wa Senegal biliyoyin daloli, tare da bunƙasa tattalin arzikinta.

    Babban manajan kamfanin man fetur na ƙasar, Thierno Ly, ya ce ƙasar ta buɗe sabon babi, a lokacin da aka ƙaddamar da tono man ranar Talata.

    Shugaban ƙasar, Bassirou Diomaye Faye - wanda aka zaɓa a watan Afrilu - ya jima yana burin ƙulla yarjejeniyar fara aikin, a wani ɓangare na sauye-sauyen da ya alƙawarta samar wa ƙasar a lokacin yaƙin neman zaɓe.

  15. Ten Hag zai ci gaba da horar da Man United

  16. Ana fargabar yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza tana ƙasa tana dabo

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren harkokin waje na Amurka, Antony Blinken ya sauka a Qatar domin tabbatar da yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar a Gaza da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su wadda a yanzu haka ta ke kasa take dabo tun bayan martanin kungiyar Hamas.

    Rahotanni dai sun ce tun tsakar dare mista Blinken ya farka daga barci yake ta nazarin sakon da Hamas ta miƙa wa Qatar da Egypt masu shiga tsakani.

    Ƙungiyar Hamas dai ta ce a shirye take ta yi maraba da yarjejeniyar to amma ta sa sharadin cewa sai idan Isra'ila ta amince da dakatar da yaƙi baki ɗayansa.

    Gwamnatin Isra'ila dai ba ta mayar da martani ba amma kuma wani jami'in Isra'ilar wanda ba ya son a ambaci sunansa ya ce sauyin da Hamas ke son yi ga yarjejeniyar tamkar watsi da ita ne.

    BBC na daga cikin tawagar ƴan jaridar da ke tafiya da mista Blinken a ziyarar tasa zuwa birnin Doha inda yake ganawa da shugabannin Qatar domin tabbatar da yarjejeniyar ba ta samu cikas ba.

    A ranar Talata dai Mista Blinken da firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu sun ƙara nanata muhimmancin yarjejeniyar duk da cewa Mista Netanyahu bai fito fili ya yi maraba da yarjejeniyar ba wadda shugaban Amurka, Joe Biden ya ce Isra'ilar ce ta fito da ita .

  17. Sauro ya sake ɓulla a nahiyar Turai

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Lafiya ta Tarayyar Turai ta yi gargaɗin cewa cutar zazzaɓin cizon sauro ta Dengue da sauran cututtuka da sauro ke yaɗawa na ƙaruwa sosai a nahiyar.

    Cibiyar Kare yaɗuwar Cututtuka ta Turai ta ce sauyin yanayi na samar da yanayi mai kyau ga ƙwari masu haɗari, kamar nau'in sauron da ke yaɗa cututtukan zazzaɓin Dengue da cutar Zika.

    Yanzu an gano waɗannan a ƙasashe 13 na tarayyar Turai da suka haɗa da Faransa da Spaniya da Girka har zuwa abun da ya kai arewacin Paris.

    Adadin mutanen da ke kamuwa da zazzaɓin na Dengue a Turai ya ninka a bara kaɗai.

    Kazalika an gano nau'in wani sauro wanda shi ne ke yaɗa zazzaɓi a Cyprus.

    Zazzaɓin Dengue cuta ce da macen sauro ke yaɗawa tsakanin al'umma. Hakan ne ya sa ake shawartar masu rayuwa a Turan da su riƙa kawar da ajiyayyen ruwa da kuma riƙa kwana a gidan sauro.

  18. Atiku ya jajanta wa Tinubu

    ..

    Mutumin da shugaba Tinubun ya kayar a zaɓen 2023, Atiku Abubakar na jam'iyyar adawa ta PDP, ya ce yana jajanta wa Bola Tinubu dangane da "zamewar" da ya yi.

    "Ina matukar jajanta wa shugaba Bola Tinubu dangane da ɗan hatsarin da ya samu a lokaci da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti ranar dimokaraɗiyya. Ina fatan lafiyar lau."

    A baya-bayan nan dai an ga yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ke ƙara ƙaimi wajen yin hamayya ta fuskar sukan abubuwan da yake ganin gwamnatin ba ta yi daidai ba.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Tsadar rayuwa: Guinness mai yin giya ya sanar da ficewa daga Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin Guinness mai yin kayan sha ciki har da giya ya sanar da shirinsa na ficewa daga Najeriya saboda matsanancin halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki.

    Kamfanin wanda ya kwashe fiye da shekra 74 yana aiki a Najeriya ya ce zai fice sannan kuma zai sayar da dukkannin hannin jari mallakarsa ga rukunin kamfanoni na Tolaram Group na ƙasar Singapore.

    Jaridar People's Gazette ta rawaito cewa kamfanin na Guinness dai ya yi asarar naira biliyan 61.9 a watan Yulin 2023 da Maris na 2024 bayan hawan Tinubu inda ya rage wa naira daraja.

    Guinness Nigeria Plc, kamfani ne wanda yake cikin jerin sunayen kamfanoni da ke hada-hadar hannayen jari a Najeriya kuma an yi masa rijista a kasar a matsayin kamfanin da ke shigar da giya samfirin Stout daga Dublin.

  20. Yadda Tinubu ya zame a Eagles Square a ƙoƙarinsa na hawa mota