Wakiliyar MDD ta isa birnin Goma na Jamhuriyar Dimokraɗiyar Kongo

Asalin hoton, Getty Images
Mai riƙon muƙamin shugabancin shirin daidaita lamurra na Majalisar ɗinkin duniya a Jamhuriyar dimokraɗiyyar Kongo ta isa birnin Goma da ke gabashin ƙasar, wanda ke hannun ƴan tawaye.
Majalisar ɗinkin duniyar ta ce isar Vivian van de Perre filin jirgin saman Goma, wani mataki ne mai muhimmanci, bayan shafe lokaci mai tsawo jiragen sama ba sa samun damar shiga sararin samaniyar yankin.
Wakilin BBC ya rawaito cewa Vivian na fatan saukar ta a filin jirgin zai bayar da damar sake buɗe shi sannu a hankali, domin ya amfani mutanen yankin.
Ƴan tawayen M23 masu samun goyon bayan Rwanda sun dakatar da ayyuka a filin jirgin saman a watan Janairun bara, bayan ƙwace ikon yankin arewacin Kivu mai cike da albarkatun ƙasa, a wani hari da suka kai da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.
Majalisar ɗinkin duniya ta ce ziyarar na da nufin tallafawa shirye shiryen tabbatar da tsagaita wuta, bayan yarjejeniyar zaman lafiya da Rwanda da Congo suka sanya wa hannu a Washington.



















