Ƙasashen Afirka biyu tal da suka mallaki jirgin yaƙin zamani na F-16

Asalin hoton, Getty Images
Bayanai sun nuna cewa ƙasashe biyu ne kacal a Afirka suke da jiragen yaƙi na zamani na F-16, wanda jirgi ne da ke cikin waɗanda suka fi ƙarfi da inganci a wajen yaƙi.
Sai dai mallakar wannan jirgin yana danganta ne da alaƙa da kuma yarjejeniya tsakanin ƙasar da ke buƙatar jirgin da gwamnatin Amurka, wadda ita ce take ƙera shi.
Masar tana da jirgin, wanda kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito ta mallaka a shekarar 2015 bayan gwamnatin Amurka ta fara kai jiragen na F-16 guda 8 zuwa ƙasar a daidai lokacin da ƙasashen biyu suka fara gyara alaƙa.
Sun fara gyara alaƙa ne bayan hamɓarar da gwamnatin Mohamed Mursi, sannan kuma Abdel Fattah al-Sisi ya karɓi ragamar mulki, wanda ya yi ta yunƙurin gyara alaƙa da Amurka.
Wata ƙasar da take da jirgin na F-16 ita ce ƙasar Morocco, wadda a shekarar 2007 gwamnatin ƙasar ta shiga yarjejeniya da gwamnatin Amurka a zamanin mulkin George W. Bush domin mallakar jirgin yaƙin na F-16 guda 24 a kan kuɗi dala biliyan 2.4.
Bayan kimanin shekara 10, a shekarar 2019 Morocco ta sake shiga wata yarjejeniyar da Amurka domin mallakar wasu jiragen na F-16 da kuma gyara tsofaffin da ta saya a baya a kan kuɗi dala biliyan 4.

Asalin hoton, Getty Images
Yanayin ƙarfin jirgin F-16
An tsara jiragen na F-16 ne su zama ƙanana ƴan shafal-shafal domin guje wa nauyi, kuma su samu sauƙin aiki a fagen daga.
Amma da aka samu cigaban kimiyya da fasaha, da kuma yadda buƙatuwar sojoji ta canja, ciki har da buƙatar kai hare-hare a can ƙasa da jiragen ruwa da tattara bayanan sirri, sai ya zama akwai buƙata inganta jiragen.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Zuwa shekarar 2015, jiragen F-16 ne waɗanda aka fi amfanin da su wajen yaƙi a duniya, inda ake tunanin har zuwa yanzu akwai jiragen sama da guda 2,000 da ake amfani da su a duniya.
Jirgin na da tsayin mita 15, sannan fuka-fukansa sun kai tsayin mita 9.45, kuma yana da gudun kusan nunki biyu sama da na ƙara.
Jirgin na ɗauke da bindiga mai girman 20mm da ke ɗaukar makamai masu linzami a fuka-fukansa, mai jimillar nauyin kilogiram 10,000.
Jiragen na F-16 sun samu karɓuwa ne ba kawai domin yanayinsu ba, har da ma gyare-gyaren da aka yi bayan darasin da aka ɗauka daga yaƙin Vietnam.
A ƙarni na 21, jirgin F-16 ya zama wani jirgi da ke iya ƙaddamar da hari zuwa can ƙasa, aikin da asali ba ya cikin abin da aka tsara zai yi a farkon ƙera shi a shekarun 1970.
Sannan yadda jirgin yake iya shigewa cikin kowane irin yanayi ya yi aikinsa ya sa ya zama abin sha'awa, wanda hakan ya sa sojojin saman ƙasashen da dama ke sha'awar amfani da shi.
A cewar Robinson, ana kiran jirgin da Viper ne saboda nuna shi da aka yi a shirin talabijin na Battlestar Galactica da aka yi a tsakankanin 1970, inda jirgin ƙirƙirarren labarin Colonial Viper yake kama da jirgin na F-16.
Waɗanne irin jiragen yaƙi Najeriya ta mallaka?
Wasu alƙaluma game da rundunar sojin saman Najeriya kan yawan jiragen yaƙin da rundunar ke da su ya zuwa 2025 sun nuna cewa Najeriya na da jiragen yaƙi 142 waɗanda lafiyayyu ne sannan suna zaman ko-ta-kwana.
Shafin da ke bayyana ƙarfin sojin saman ƙasashen duniya na WDMMA ya zayyana yadda ake amfani da jiragen inda 35 daga cikin 142 suka kasance na zuwa filin daga da 80 da ake kai ɗauki da su da kuma 27 na atisaye.
Bayanin ya ce jiragen yaƙin Najeriya sun haɗa da:
Alpha Jet A/E: ƙirar Faransa - 12
F-7NI: ƙirar China - 11
JF-17A: ƙirar Pakistan hadin gwiwa da China - 3
A-29B Super Tucano: Daga Amurka - 12
Jirgin soji mai saukar ungulu - 51
Jirgin soji na jigila - 20
Jirgin soji na bayar da horo - 27
Jiragen sojin aiki na musamman - 9
Jiragen yaƙi da aka yi oda - 56










