Manyan ƴan siyasa da aka bincika a Najeriya bayan hawan Tinubu

...

Asalin hoton, FB/Multiple

    • Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
    • Aiko rahoto daga, BBC Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Zargin ƴan siyasa da suka taɓa riƙe muƙaman gwamnati a Najeriya da aikata almundahana ba sabon abu ba ne a fagen siyasar ƙasar.

A mafi yawan lokuta akan fara zarge-zargen ne a lokacin da ‘yan siyasar ke kan mulki, sai dai a mafi yawan lokaci bincike na tasowa ne bayan sun sauka.

A baya-bayan nan ‘yan adawa a Najeriya na zargin gwamnati da yin amfani da hukumomin yaki da rashawa wajen tsoratar da su ko yi musu barazana, kamar yadda tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya fada a wata tattaunawa da BBC.

Tun bayan hawan Shugaban Bola Tinubu kan mulki an ci gaba da yin irin wannan bincike, sai dai duk da cewa akwai ‘yan jam’iyyun adawa da dama a cikin wadanda aka bincika, amma akwai kuma ‘yan siyasa na jam’iyya mai mulki.

BBC ta duba wasu daga cikin wadannam ‘yan siyasa da aka zarga da almundahana tun bayan hawan Tinubu kan mulki.

Abubakar Malami

Abubakar Malami

Asalin hoton, Malami

Abubakar Malami shi ne tsohon babban lauyan gwamnati kuma ministan shari'a a ƙarƙashin gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, ya kasance babban ɗan siyasar ɓangaren adawa da ke fuskantar zargin aikata rashawa a baya bayan nan.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar EFCC ta zargi Malami da laifukan da suka haɗa da amfani da muƙami ba bisa ƙa'ida da kuma safarar haramtattun kuɗade.

EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume 16 a kan Malami da ɗansa da kuma mai ɗakinsa, Hajiya Asabe Bashir, masu alaƙa da halasta kuɗaɗen haram da kuma mallakar kadarori da darajarsu ta haura naira biliyan 8.7.

Kuma bayan kotu ta bayar da belinsa bisa wannan tuhumar, daga baya an sake kama shi inda hukumomin ƙasar ke tuhumar sa da ayyukan tallafa wa ta'addanci inda har yanzu yake riƙe a hannun hukuma.

Malami, wanda ake kallo a matsayin jigo a tafiyar ƴan adawar shugaba Bola Tinubu a Najeriya, ya yi watsi da zarge-zargen inda ya alaƙanta abin da yake fuskanta daga hukumomin ƙasar da bi-ta-da-ƙullin siyasa.

Aminu Waziri Tambuwal

Aminu Waziri Tambuwal

Asalin hoton, Aminu Waziri Tambuwal Media Office

A watan augustan 2025, hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal zuwa hedikwatarta da ke Abuja.m domin ya amsa tambayoyi kan zarge-zargen fitar da maƙudan kuɗaɗe da suka kai Naira biliyan 189, wanda aka bayyana cewa yin hakan ya saɓawa dokar yaƙi da halasta kuɗaɗen haram, ta shekarar 2022.

Hukumar ta yi zargin cewa an cire wafannan kuɗaɗe ne a lokacin da ya ke gwamna, kuma masu bincike sun bayyana hakan a matsayin yi wa dokokin kuɗin ƙasa karan tsaye.

Duk da cewa zargin da hukumar EFCC ta yi wa Tambuwal bai kai ga gurfanar da shi a gaban kotu ba, kamun da aka yi masa ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar, musamman tsakanin ƴan hamayya, kamar su Atiku Abubakar da Peter Obi, waɗanda ke zargin hakan na da alaƙa da rawar da yake takawa a tafiyar ƴan jama'iyyar haɗaka ta ADC.

Nasiru El-Rufai

Nasiru El-Rufai

Asalin hoton, El Rufa'i/X

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun barinsa kujerar gwamnan jihar Kaduna a Shekarar 2023, da kuma ficewarsa daga jam'iyyar APC, Nasiru El-Rufai ya fuskanci zarge - zarge daga gwamnatin da ta gaje shi kan aikita laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa duk da dai ba a kai ga kama shi ko tuhumarsa a hukumance ba.

A cikin ƴan kwanakin nan dai El-Rufa'i ya tsananta sukar da yake yi wa gwamnatin shugaban Najeriya Bola Tinubu da kuma jam'iyyar APC mai mulki, wadda a ƙarƙashinta ne ya yi gwamnan jihar Kaduna na shekara takwas.

A wata tattaunawa da BBC, El-Rufa'i ya ce duk da cewa ba a riga an kama shi ba, amma an kama na kusa da shi, kuma yana tunanin za a iya zuwa kansa nan ba da jimawa ba.

"An kama mutum wajen guda huɗu waɗanda muka yi aiki da su a Kaduna, saboda haka ni ma lokaci ne, ni ma za a neme ni," in ji shi

Tsohon gwamnan dai ya zargi jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar da yi wa ƴan siyasar adawa barazana da kamu inda ya ce hakan ne ke tilastawa wasu ƴan siyasar sauya sheƙa zuwa jam'iyyar.

Sule Lamido

Sule Lamido

Asalin hoton, Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya fuskanci doguwar shari'a da hukumar EFCC kan zargin almundahanar sama da naira biliyan 1.3 da kuma sauran tuhume-tuhume tun bayan barin mulkinsa a 2015.

A baya an taba tsare shi tare da ƴaƴansa Aminu da Mustapha, inda aka gudanar da bincike kan zargin karkatar da kuɗaden gwamnatin Jihar ta hanyar amfani da kamfanonin iyalinsa.

Ko a ƙarshen shekarar 2012 jami'an hukumar EFCC sun kama ɗaya daga cikin ƴaƴan tsohon gwamnan, Aminu Sule inda aka yi zargin yana shirin fita ƙasar waje da maƙuden kuɗaɗe.

A shekarun baya dai tsohon gwamnan wanda jigo ne a jami'iyyar hamayya ta PDP ya zargi gwamnatin APC a ƙarƙashin marigayi Muhammadu Buhari da karkata hankalinta wurin yaƙin da ta ke yi da cin hanci da rashawa kan jami'an gwamnatin PDP wadda ta yi shekara 16 tana mulki a Nijeriya.

Ƴaƴan jam'iyyar APC da su ma suke fuskantar bincike

Yahaya Bello

A halin da ake ciki yanzu hukumar EFCC na ci gaba da tuhumar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello a gaban kotu bisa zargin karkatar da kuɗi har Naira biliyan 80.2, inda ake ci gaba da shari'ar a kotu.

ashekarar 2024, Jami'an hukumar EFCC sun taɓa mamaye gidan Bello wanda ya yi wa'adi biyu a matsayin gwamnan jihar Kogi, a yunƙurin kama shi, to amma sai aka yi zargin cewa gwamnan jihar wanda ya gaje shi, Usman Ododo ya je gidan domin tseratar da shi zuwa gidansa, kamar yadda kafafen yaɗa labarab ƙasar suka ruwaito.

Daga baya dai Bello ya gurfana a gaban kotu a ƙarshen 2024, inda aka tsare shi tare da hana shi beli.

A watan Janairun 2026 shugaban hukumar EFCC ya tabbatar cewa shari'ar na ci gaba da gudana a kotu, kuma sun himmatu wajen tabbatar da cewa an kai ga cimma nasara.

Hadi Sirika

Hadi Sirika, shi ne tsohon ministan sufurin jiragen sama a lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari.

Sirika dai ya shahara ne kan batun kamfanin NIgeria Air da ya ƙaddamar a lokacin da ana saura ƴan kwanaki kaɗan wa'adin gwamnatinsu ya ƙare.

Cecekucen da ya biyo bayan lamarin ya sa gwamnatin Tinubu ta soke kwantaragin kafa kamfanin.

Yanzu haka hukumar EFCC ta gurfanar da Sirika a kotu game da batun kafa kamfanin jirgin mallakar gwmnatin Najeriya.

Ta zarge shi da yin amfani da ofishinsa wajen yi wa ɗiyarsa Fatima da mijinta Jalal Hamma alfarmomi ta hanyar ba su aikin bayar da shawarwari a kamfanin Nigeria Air, da kuma ba su kwangilar gina wani ɓangare na filin jirgi a Katsina.

Kotu ta bayar da belin tsohon ministan kan naira miliyan 100 kuma har yanzu batun na gaban kotu.