Cututtukan da za a iya ɗauka a wajen kitso ko aski

Kitso

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Kitso ga mata, da kuma aski ga maza, wani abu ne tamkar wajibi - domin tabbatar da tsafta, kiwin lafiya da kuma ado.

Mako-mako ko wata-wata ko kasa da haka, kowa na da lokacin da yake dauka kafin ya je a rangada masa aski ko kuma a rangada mata kitso.

Sai dai wani lokaci idan ba a dauki matakan da suka kamata ba, a garin neman gira sai a rasa ido.

Domin kuwa wadamnam abubuwa biyu, idan har ba a dauki matakan da suka dace ba wajen tabbatar da tsafta da kuma kare lafiya, masana na cewa hanyoyi ne na yada cutuka cikin sauri.

A yawancin lokuta, mutane sun fi damuwa da irin salo ko kyawun da za su fito da shi, ba tare da la'akari da irin kayan aikin da ake amfani da su ba.

Duk da cewa zamani ya zo da kayan aiki na zamani wajen aski ko kitso, to amma hadarinsu wajen yada cutuka kusan iri daya ne da reza, almakashi, mataji ko kuma tsinken tsifa da ake amfani da su tun kaka da kakanni.

Hadarin kamuwa da cutuka a wurin aski ko kitso ya fi kamari ne idan ba a daukar matakan da suka dace wajen tsaftace kayan aiki.

Wasu lokutan ma, ana samun ƙananan raunuka yayin aski ko kitso kamar yanka a fatan kai da sauransu wanda mutane ba su cika lura da shi ba.

Sai dai masana lafiya sun ce waɗannan ƙananan raunuka su ne manyan hanyoyin da cututtuka ke bi su shiga jiki, musamman idan kayan aikin ba su da tsafta.

Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda cututtukan ba sa bayyana nan take. Wasu kan kamu da ƙaiƙayi ko kumburi ko zubar gashi bayan kwanaki ko makonni, ba tare da sun alaƙanta matsalar da wurin aski ko kitso ba kamar yadda Dr. Sani Abubakar, likitan lafiyar al'umma ya bayyana wa BBC.

Dr. Sani ya ce yawancin cututtukan kai da fata da ake gani a asibitoci suna da alaƙa kai tsaye da rashin tsafta a wuraren aski da kitso.

A cewarsa, "duk wani kayan aiki da ke taɓa fata, musamman idan wani ya taba samun rauni da shi na iya zama hanyar shigar cuta."

Likitan ya lissafo cutukan da za a iya ɗauka a wureren aski ko kitso kamar haka.

Amosanin kai da maƙero

Kitso

Asalin hoton, Getty Images

Waɗannan su ne cutukan da aka fi yawan ɗauka a wuraren aski ko kitso.

Dr. Sani ya ce ana ɗaukar su ne idan an yi amfani da abin tsefe gashi ko abin aski da aka riga aka yi amfani da su a kan wani mai ɗauke da amosanin ko kuma maƙero.

"Waɗannan cutukan suna haddasa kaikayi ko fatar kai ta bare, wani lokaci har gashi ya zube," in ji likitan.

Ciwon hanta nau'in B (Hepatitis B)

...

Asalin hoton, Getty Images

A cewar likitan, ciwon hanta na iya yaɗuwa ta hanyar jini.

"Idan aka yi amfani da abin aski da aka riga aka yi amfani da shi a kan wani mai dauke da cutar kuma aka yanke shi, sannan aka yanki wanda ya zo bayan shi, akwai yiwuwar kamuwa da cutar," in ji likitan.

Ciwon hanta nau'in C (Hepatitis C)

...

Asalin hoton, Getty Images

Kamar Hepatitis B, wannan cuta ma tana yaɗuwa ta hanyar jini. Likitan ya jaddada cewa rashin sauya abin aski ko kashe ƙwayoyin cuta ta hanyar tsaftacewa na iya ƙara haɗarin ɗaukar cutar.

Cutar mai karya garkuwar jiki HIV/Aids

Ko da yake ba kasafai take faruwa ba, Dr. Sani ya ce yiwuwar ɗaukar cutar HIV na nan idan an yi amfani da reza ko abin tsaga ko abin aski guda ɗaya kan me cutar kuma aka samu yanka kai sai kum aka yi amfani da kayan aikin a kan wani daban.

Ƙwarƙwata

...

Asalin hoton, Getty Images

Wannan in ji likitan nna yaduwa sosai a wuraren kitso, musamman idan ana amfani da abin tsifa ko mataji ɗaya ko kayan haɗa gashi ba tare da tsaftacewa ba. Yana haddasa matsanancin ƙaiƙayi, musamman ga yara.

Kumbirin fatar kai (Folliculitis)

Dr. Sani ya bayyana cewa wannan cuta kan faru ne idan ƙwayoyin cuta suka shiga fatar gashi bayan aski. Tana haifar da ƙananan kumburi masu ciwo, musamman a bayan kai ko gemu.

Ƙuraje masu ƙaikayi (Scabies)

Likitan ya ce duk da cewa ba ta da alaƙa kai tsaye da aski, likitan ya ce ana iya ɗaukar ta idan aka yi amfani da tawul ko zani ko kayan aiki marasa tsafta a wurin kitso.

Yadda za a kare kai

Kitso

Asalin hoton, Getty Images

Dr. Sani ya ba da shawarwarin da mutane za su iya bi wajen kare kai kamar haka;

  • A riƙa amfani da reza sabuwa ko ta kai kaɗai
  • A tabbatar an tsaftace kayan aski ko kitso ta hanyar jiƙa su cikin ruwan zabi.
  • A guji aski ko kitso idan akwai rauni a kai
  • Iyaye su kula da wurin kitson yara, musamman 'yan mata
  • Haka kuma, mallakar kayan aski ko abin tsifa na kai zai rage haɗarin kamuwa da cututtuka.