Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 14/07/25

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi da Isiyaku Muhammed da Aisha Aliyu Jaafar da Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Bankwana

    Da wannan ni Umaymah Sani Abdulmumin daga nan sashin hausa na BBC na ke cewa sai gobe da yardan Allah. A kwana lafiya

  2. Sojojin Isra'ila sun kai wa tankokin yaƙin Syria Hari

    Sojin Isra'ila sun kai wa tankokin yakin Siriya hari, wadanda Damascus ta aika don hana rikici tsakanin mayakan addinin Druze da ke bin mazhabar shi'a da Larabawa mazauna karkara 'yan Sunni.

    Mabiya Addinin Druze dubu dari da hamsin da ke zaune a Isra'ila sun dauki alwashin kare kungiyar mabiya Addinin a Siriya.

    Kafar yada labarai ƙasar ta ce akalla mutane 50 sun mutu a rikicin, wanda ya barke ranar Lahadi a birnin Sweida bayan an sace wani dan kasuwa.

    Isra'ila na kallon sabuwar gwamnatin Siriya a matsayin barazana ga tsaronta, kuma ta gargade ta da ta guji jibge dakaru a kudancin damascus.

  3. Jonathan da Akufo-Addo na Ghana sun je ta'azziyar Buhari Landan

    Tsohon shugaba Goodluck Jonathan da Nana Akufo-Addo na Ghana sun ziyarci mataimakin shugaban ƙasa domin ta'aziyar Muhammadu Buhari a Landan.

    Tsoffin shugabannin biyu sun ziyarci mataimakin shugaban ƙasar da iyalansa tare da muƙarabansu kafin a taho da gawar Buhari Najeriya a gobe Talata.

    Kashin Shettima ya je Landan ne tare da manyan jami'an gwamnati da gwamnan Borno da minista Yusuf Tuggar domin kammala duk abin da ya kamata na dauko gawar Buhari zuwa Najeriya.

  4. 'Cinikayya tsakanin Turai da Amurka na iya samun cikas'

    Kwamishinan cinikayya na Tarayyar Turai Maros Sefcovic ya ce cinikayyar da ta kai dala biliyan 84 da ke tsakanin EU da Amurka ka iya samun tasgaro idan tattaunawar da ake yi ta kasa cimma nasara.

    Ya faɗi hakan ne bayan kammala wani taron ministocin cinikayya na ƙasashen Tarayyar Turai inda suka tattauna yadda za su mayar da martani kan barazanar da Trump ya yi na ƙaƙaba musu harajin kashi 30.

    Hukumomi a Brussels sun ce zuwa yanzu an fitar da jerin wasu matakan ramuwar gayya da za a iya ɗauka, sai dai za a jinkirta ƙaddamar da su yayin da ake ci gaba da tattaunawa.

  5. Ra'ayoyin wasu ƴan Najeriya da ke London kan rasuwar Buhari

  6. Tinubu ne zai karɓi gawar Buhari a Katsina

    Shugaban Nigeria Bola Tinubu ne zai tarbi gawar tsohon shugaba Muhammadu Buhari a Katsina, domin yi masa jana'iza a Daura.

    Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ne ya tabbatar da hakan da yammacin yau Litinin a Abuja.

    A cewar ministan, da misalin karfi 12 ranar gobe Talata ake saran gawar marigayi tsohon shugaban ya isa Katsina.

    Sannan za a yiwa shugaban faretin ban girma a filin jirgin saman Katsina, kafin daga bisani a wuce garin Daura da gawarsa.

    Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima yanzu haka na Landan, kuma shi ne zai rako gawar har Katsina.

    Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti na musamman da za su tsara jana'izar da kuma duk wani abu da ake bukata wajen binne shugaban.

  7. Al'umma na dafifin zuwa jana'izar Buhari a Daura

    'Yan'uwa da makusanta da abokan arziƙi na ci gaba da isa Daura, mahaifar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari domin halartar jana’izarsa a gobe Talata.

    Yayin da mahukunta ke cewa suna ɗaukar matakai domin mahalartan da ake sa ran zuwansu ciki har da shugabannin ƙasashe.

    Tsare-tsare sun yi nisa don kawo gawar marigayin inda za a yi masa jana'izar a mahaifarsa Daura.

    Akwai mabanbantan ra'ayoyi game da yadda Marigayi tsohon shugaban Najeriyar ya mulki kasar.

    Amma a cewar Alhaji Yau Umar Gwajo-Gwajo, rashin sanin yadda shugabanci yake ne yasa wasu ke masa wani irin kallo.

    Baya gwamnatin tarayya da ta ayyana gobe Talata, 15 ga watan Yulin shekarar 2025 a matsayin hutu domin jimamin rasuwar tsohon shugaban, sauran jihohi ma sun sanar da hutun kamar jihar Yobe inda gwamnan ya ce al'umma su zauna a masallatai don yi masa addu'o'i.

    Yayin da gwamnatin jihar Katsina ke kiran ga 'yan Najeriya su yi wa marigayin addu'a, a gefe guda kuma suna rokon al'umma su bayar da haɗin-kai ga jami'an tsaro a gobe lokacin da za a yi masa jana'izar a gidansa da ke Daura.

  8. RSF na korar majinyata daga asibitocin Kordofan

    Masu aikin ceto a Sudan sun ce dakarun RSF na korar majinyata daga asibitocin da ke yammacin jihar Kordorfan don mayakansu da suka jikkata su samu kulawa.

    Sun ce dakarun RSF sun yiwa wasu majinyata duka. Rahotannin sun biyo bayan yake-yake a karshen makon da ya gabata a birnin Um Samima, inda bagarorin da basa ga macijin ke ikirarin iko da shi.

    Rikici ya 'kara tsanani a El fasher da ke yammacin yankin Darfur.

    Dakarun RSF sun shafe sama da shekara guda suna kokarin karbe birnin, lamarin da ya sanya 'daruruwan fararen hula tserewa.

    Wakilin BBC ya ce sojoji sun yiwa wasu birane luguden wuta a yankin, an samu lafawa a Khartoum babban birnin 'kasar da gabashin Sudan, rikicin ya koma Kudanci da Yammacin kasar da suka hada da Darfur.

  9. 'Yan Nijar na alhinin rasuwar Buhari

    Mutuwar tsohon shugaban Najeriya Mohamadu Buhari ta dauki hankalin 'yan Nijar da dama.

    Tun bayan samun labarin rasuwar shugaban al'ummar Nijar da dama sun girgiza tare da tuna wasu daga cikin ayyukan da ya yi na karfafa danganta da ma hulda tsakanin kasar Nijar da Najeriya.

    'Yan Nijar ɗin na cewar da a lokacin mulkinsa ne aka yi juyin mulkin ƙasar, babu mamaki da abubuwa ba su surkukuce musu haka ba.

    Galibi dai sun rinka tuna da alkhairan shugaban da abubuwan da ba za su taba manta da marigayi Muhammadu Buhari ba.

    Rasuwar tsohon shugaba Buhari ya zo wa 'yan Najeriya da ƙasashe makwabta da ketare da mamaki yayinda ake cigaba da alhinin rasuwar shugaban.

  10. Zelensky ya gode wa Amurka kan taimakon soji

    Shugaban Ukraine ya miƙa godiyarsa ga Amurka saboda goyon bayanta, gabanin sanarwar da Donald Trump zai yi na bata ƙarin tallafin kayayyakin soji.

    Volodymyr Zelensky ya faɗi hakan ne bayan ganawa da wakilin fadar White House Keith Kellogg a Kyiv.

    Mista Zelensky ya ce sun tattauna kan batun ƙarfafa garkuwar kare sararin samaniyar Ukraine da kuma takunkuman da watakil za a sanyawa Rasha.

    Tun da farko shugaba Trump ya ce Amurka za ta aika wa Kyiv kayyayakin soji na zamani.

    Ana dakon jiran sanarwarsa a hukumace idan an jima.

  11. Tinubu ya kafa kwamitin jana'izar Buhari

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kafa kwamitin da zai jagoranci jana'izar ƙasa da za a yi wa tsohon shugaban ƙasar Muhamamdu Buhari.

    Kwamitin ƙarƙashin jagorancin babban sakaten gwamnatin tarayya, Sanata George Akume zai jagoranci shiryawa tare da tsara yadda za a gudanar da jana'izar tsohon shugaban ƙasar.

    ikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnati, Segun Imohiosen ya fitar ya ce mambobin kwamitin sun haɗa da:

    • Ministan kudi
    • Ministan kasafi da tsare-tsare
    • Ministan Tsaro
    • Ministan yaɗa labarai
    • Ministan ayyuka
    • Ministan cikin gida
    • Ministan Abuja
    • Ministan Gidaje da raya birane
    • Ministan kiwon lafiya
    • Ministar al'adu
    • Bai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha'anin tsaro
    • Bai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsare-tsare
    • Babban mai taimaka wa shugaba kan harkokin siyasa
    • Babban sifeton ƴansanda
    • daraktan hukumar tsaro ta farin kaya
    • Babban hafsan tsaron ƙasar.
  12. Za a binne gawar Buhari a cikin gidansa na Daura - Dikko Radda

    Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda ya bayayna cewa za a binne gawar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a cikin gidansa na Daura.

    Cikin wata hira da BBC, Gwamna Radda ya ce za a kai gawar tsohon shugaban gidan sarkin Daura domin yi masa sallah sannan a mayar da gawar gida domin binne ta.

    ''Mun yi magana da ƴan'uwa da danginsa, kuma abin da shawara ta kaya shi ne za a binne shi cikin gidansa da ke Daura'', in ji shi.

  13. WHO ta amince da wani sabon maganin kariyar kamuwa da HIV

    Hukumar lafiya ta duniya WHO ta amince da wani allura da ake yi sau biyu a shekara mai suna Lenacapavir da ke kariya daga kamuwa da HIV.

    Wannan muhimmin sanarwa na zuwa ne bayan ma'aikatar kula da lafiya ta Amurka ta amince da maganin a watan da ya gabata.

    Maganin wanda ake amfani da shi ta hanyar yin allura, zai maye gurbin maganin da ake sha kullun ko kuma wasu magungunan da ke aiki na gajeren lokaci.

    Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce amincewa da maganin shi ne matakin farko na faɗaɗa samar da shi.

  14. Yadda mutanen Daura ke alhinin rasuwar Muhammadu Buhari

    A ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli ne tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rasu a wani asibiti da ke Landan bayan doguwar jinya.

    Mutanen garin Daura, mahaifar tsohon shugaban ƙasar a jihar Katsina sun bayyana halin da suka shiga bayan samun labarin rasuwar tasa.

  15. Bayani kan jana'izar Muhammadu Buhari

    Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa Shugaban Najeriya, Bola Tinubu da wasu shugabannin ƙasashe biyu za su halarci jana'izar marigayi Muhammadu Buhari a Daura ranar Talata.

  16. Gwamnatin Najeriya ta ayyana hutu ranar Talata domin jimamin Buhari

    Gwamnatin Najeriya ta ayyana gobe Talata, 15 ga watan Yulin shekarar 2025 a matsayin hutu domin jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin cikin gida na ƙasar ta fitar, wanda babban sakataren ma'aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu, inda ta ce wannan ɗoriya ce kan sanar da kwana bakwai na jimamin rasuwar.

    Ministan Harkokin Cikin Gidan ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya yi sanarwar a madadin shugaban ƙasar, Bola Tinubu.

    Ministan ya ce ƙasar ta ayyana hutun ne domin nuna irin girmamawar da gwamnatin ke yi wa tsohon shugaban, da kuma godiya ga hidima da sadauwar da ya yi domin ciyar da ƙasar gaba.

    "Muhammadu Buhari ya mulki Najeriya da gaskiya da amana da kuma matuƙar sadaukarwa musamman wajen haɗin kan Najeriya da cigabanta. Wannan hutun dama ne ga ƴan Najeriya domin tuna irin sadaukarwar da Buhari ya yi."

    Ya yi kira ga ƴan Najeriya su tuna mamacin ta hanyar koyi da shi wajen ɗabbaƙa zaman lafiya da son cigaban ƙasar da aka san marigayin da su.

  17. Wane ne Muhammadu Buhari?

    Tsohon shugaban Najeriya, ɗaya daga cikin ƴansiyasa na ƙasar da aka fi nuna wa ƙauna, ya rasu yana da shekara 82.

    Ɗan siyasa wanda siyasarsa ta sha bamban da ta saura, ya kasance mara son hayaniya kuma mai jajircewa. Buhari ya kasance sahun gaba a cikin shugabanni Najeriya ƙalilan da ake yi wa kallon masu gaskiya.

    Tsohon babban mai taimaka masa kan yaɗa labarai Femi Adesina, ya ce "babu ta yadda za a yi ka alaƙanta Buhari da rashawa".

    Akasarin waɗanda ke ƙaunar Buhari sun yi hakan ne sanadiyyar ɗabi'unsa na gaskiya da son bin doka.

  18. Gwamnonin arewa maso yamma sun ayyana hutu ranar Talata domin rasuwar Buhari

    Ƙungiyar gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana kaɗuwarsu kan rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari wanda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin shekarar 2025 a birnin Landan.

    A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, wanda shugabanta, Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda ya fitar, ya ce Buhari tamkar uba yake a gare su.

    "Muna miƙa ta'aziyarmu ga Shugaban Najeriya Bola Tinubu da iyalai da ƴanuwa da mutanen jihar Katsina da ma ƴan Najeriya baki ɗaya bisa wannan babban rashin da aka yi."

    Gwamnonin sun ce Buhari abin alfaharin yankinsu ne, "wanda ya ƙarar da rasyuwarsa wajen hidima da sadaukar da kansa wajen ciyar da Najeriya gaba."

    "Saboda wannan ne ƙungiyar gwmnonin arewa maso yamma suka amince da ayyana ranar Talata, 5 ga watan Yulin 2025 a matsayin ranar hutu domin jimamin rasuwar mamacin," kamar yadda sanarwar ta nuna.

    Dikko Radda ya ce gawar Buhari za ta isa Katsina a gobe Talata da misalin ƙarfe 12, sannan a gudanar da jana'izar da misalin ƙarfe biyu na rana.

    "Muna kira ga dukkan ƴan Najeriya su yi masa addu'a. Allah ya jiƙansa, sannan muna addu'ar Allah ya ba iyalana da ma dukkan ƴan ƙasar juriyar rashinsa."

  19. Shettima ya yi wa iyalan marigayi Muhammadu Buhari ta'aziyya a Landan

    Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya yi wa wasu daga cikin iyalan marigayi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta'aziyya a birnin Landan.

    Mataimakin shugaban ƙasar ya samu rakiyar shugaban mai'aikatan fadar Gwamnatin Najeriya, Femi Gbajabiamila.

    Kashim Shettima ya isar da gaisuwar ne ga maiɗakin mamacin A'isha Buhari da kuma ɗan'uwansa Mamman Daura.

    Sauran jami'an gwamnati da ke Landan domin rasuwar tsohon shugaban ƙasar su ne ministan harkokin waje Yusuf Tuggar, da Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum.

    Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025 a wani asibiti da ke birnin Landan bayan fama da jinya.

  20. Majalisar dokokin Najeriya ta ɗage zamanta saboda rasuwar Buhari

    Majalisar dokokin Najeriya ta ɗage zamanta zuwa ranar Talata 22 ga watan Yuli na 2025 domin alhinin rasuwar tsohon shugaba Buhari.

    Matakin ɗagewar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da akawun majalisa Kamoru Ogunlana ya fitar a ranar Litinin.

    A cewar sanarwar '' domin martaba tarihinsa da ayyukan da ya yi wa ƙasar, shugabannin majalisun na sanar da alumma da ƴan majalisu ɗage zaman majalisa zuwa mako mai zuwa, kuma ana buƙatar dukka ƴan majalisu su tsara ayyukansu yadda zai basu damar halartar jana'izar marigayin.''