Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Garnacho ya yi watsi da batun komawa Al Nassr, Bayern na son Trossard
Ɗanwasan Manchester United Alejandro Garnacho ya yi watsi da batun komawa ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya yayin da ɗanwasan asalin Argentina mai shekara 21 ya fi son komawa Turai. (Telegraph)
Bayern Munich za ta karkatar da hankalinta kan ɗanwasan Arsenal da Belgium Leandro Trossard mai shekara 30 idan haƙarsu ba ta cimma ruwa ba a sayen ɗanwasa Luis Diaz mai buga wa Liverpool ƙwallo. (Bild - in German)
Ɗanwasan Brighton Evan Ferguson ya amince ya koma Roma, yayin da kulob ɗin na Italiya ke tattaunawa kan farashin ɗanwasan mai shekara 20. (Gianluca di Marzio - in Italian)
West Ham ta amince ta ƙulla yarjejeniya da ɗanwasan Slavia Prague El Hadji Malick Diouf mai shekara 20 wanda ɗan asalin Senegal ne. (Footmercato - in French)
Nottingham Forest za ta fuskanci gogayya daga ƙungiyoyin Turai kan sayen ɗanwasan PSV Johan Bakayoko. Ɗanwasan mai shekara 22 ya kasance babban zaɓin ƙungiyar don maye gurbin Anthony Elanga wanda ya koma Newcastle a makon da ya gabata. (Nottinghamshire Live)
Wakilan ɗanwasan RB Leipzig Benjamin Sesko mai shekara 22 sun tuntuɓi Liverpool kan sha'awarsu ta sayen ɗanwasan asalin Slovenia sakamakon matakin Arsenal na mayar da hankali kan ƙoƙarin ɗaukan ɗanwasan Sporting Lisbon Viktor Gyokeres. (TBR Football)
Manchester United na ci gaba da neman gola sai dai ana ganin sauran ɓangarori da ƙungiyar ta fi ba da fifiko, ɗanwasan Kamaru Andre Onana mai shekara 29, na shirin ci gaba da zama a matsayin zaɓin farko. (i paper)
Everton ta bi sahun Roma a zawarcin ɗanwasan RC Lens Neil El Aynaoui duk da cewa ɗanwasan na ƙasar Morocco mai shekara 24 ya furta amincewa da ƙulla yarjejeniya da kulob ɗin na Serie A. (Teamtalk)
Ana sa ran golan Brest Marco Bizot mai shekara 34 zai ƙulla yarjejeniya da Aston Villa kuma zai je Birtaniya domin kammala yarjejeniyar. (L'Equipe - in French)
Rangers na ƙara ƙaimi a sayen ɗanwasan Crystal Palace Jesurun Rak-Sakyi mai shekara 22 a matsayin aro sai dai ƙungiyar na fuskantar gogayya daga wasu ƙungiyoyi da dama. (Football Insider)