Paul Biya: Shugaban ƙasa da ya fi tsufa a duniya zai nemi wa'adin mulki na takwas

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban Kamaru mai shekara 92, Paul Biya ya ce zai tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a ranar 12 ga watan Oktoba.

Matakinsa na tsayawa takara a karo na takwas ya biyo bayan ɗaukar lokaci da aka yi ana cikin halin rashin tabbas game da takarar tasa.

Paul Biya wanda shi ne shugaban ƙasa da ya fi tsufa ko yawan shekaru a duniya ya shafe shekaru fiye da 40 a karagar mulki.

Shugaba Paul Biya ya ce ya yanke shawarar tsayawa takara ne bayan kiraye-kirayen hakan da ake ta yi masa a ciki da wajen ƙasar.

A cikin wata sanarwa, Mr Biya ya yabawa abin da ya kira nasarar tabbatar da tsaro da walwalar jama'ar Kamaru a tsawon shekaru, yayin da ya amsa cewa har yanzu akwai buƙatar ƙara ƙaimi wajen magance ƙalubalan ƙasar.

Mr. Biya wanda ake yi wa kallon shugaba mai taka-tsantsan ya zura ido ba tare da cewa komai ba a yayin da ake tattauna damar da yake da ita ta sake tsayawa takara a tsakanin gwamnatinsa da kuma jam'iyyarsa.

Duk da cewa a yanzu ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara, zai iya fuskantar ƙalubale daga yankin arewa mai yawan ƙuri'u, inda wasu abokan siyasarsa na baya suka raba gari da jam'iyya mai mulki ta CPDM.

Damuwa a kan ƙoshin lafiyarsa

Babu shakka sanarwar da ya yi ta ƙara neman takara za ta farfaɗo da muhawara kan ƙoshin lafiyar shugaba Biya. Da wuya dai ake ganinsa a wuraren taro, inda ya ke tura wa domin a wakilce shi, mafi yawa ofishin shugaban ma'aikatansa ke aiwatar da irin wannan aiki. Wani ofishi da ake ganin ya bai wa ƙarfin iko sosai.

A watan Oktoban bara ya koma Kamaru, bayan shafe kwanaki 42 baya nan, lamarin da ya janyo jita-jita a kan wajen da yake. Gwamnatinsa ta yi iƙirarin cewa yana nan lafiya, amma ta haramta duk wata tattaunawa game da lafiyarsa, inda ta ce batu ne na tsaron ƙasa.

A 2008 ne shugaba Biya ya soke tanadin ko wa'adi nawa mutum zai iya yi a shugabancin Kamaru, lamarin da ya ba shi damar sake tsayawa takara kuma ya lashe zaɓen 2018 da kashi 71.28 cikin 100 na jimillar ƙuri'ar da aka kaɗa, duk da cewa ƴan adawa sun yi zargin tafka maguɗi.

Sauran masu neman takara

Bayan shugaba Biya, ƴan adawa da dama sun bayyana aniyar su ta tsayawa takara a zaɓen mai zuwa, a cikin su harda wanda ya zo na biyu a zaɓen 2018 Maurice Kamto

na jam'iyyar Cameroon Renaissance Movement da Joshua Osih na jam'iyyar Social

Democratic Front, da lauya Akere Muna da kuma Cabral Libii na jam'iyyar Cameroon Party for National Reconciliation.