Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 29/05/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir, Aisha Babangida da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Najeriya ta kammala jigilar maniyyatan aikin Hajjin 2025 zuwa Saudiyya

    NAHCON

    Asalin hoton, NAHCON

    Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya.

    Shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya tabbatar da hakan kafin tashin sa daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja zuwa Saudiyya, inda ya ce aikin nasu ya gudana cikin nasara.

    Ya ce maniyyata 41,568 ne aka yi jigila zuwa ƙasa mai tsaki a cikin sahu 105 na iragen sama.

    Ya sha alwashin cewa hukumar za ta ci gaba da aikin kula da alhazan a Saudiyya da kuma tabbatar da dawowar su gida lafiya a ƙarshen ibadar su.

  2. Rayuwar ƴan Najeriya na ƙara inganta - Tinubu

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, STATE HOUSE NG

    Bayanan hoto, Bola Tinubu

    Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ta kama hanyar inganta kuma lokacin matsi ya wuce.

    A jawabinsa na cika shekara biyu da karɓar ragamar mulki, Tinubu ya amince cewa tsare-tsarensa na kawo gyara sun janyo matsi kuma bai raina haƙuri da kuma uzurin da ƴan Najeriya suka nuna masa ba.

    "A yau ina alfahari cewa sauye-sauyen mu a fannin tattalin arziki suna aiki. Mun kama hanyar samar da ƙasa mai ƙarfin tatalin arziki,'' in ji shi.

    A ranar da aka rantsar da shi a cikin watan Mayun 2023, shugaba Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur da aka daɗe ana cece ku-ce a kai, lamarin da ya janyo tsadar rayuwa a ƙasar.

    Tinubu ya ce: “Duk da tsadar rayuwa da muka faɗa, mun samu ci gaba sosai. Hauhawar farashi ta fara raguwa musamman a kan farashin shinkafa da sauran kayayyaki.''

    Alƙaluman da hukumomi suka fitar sun nuna cewa hauhawar farashi ya ƙaru zuwa kashi 24 cikin ɗari a watan da ya gabata, idan aka alaƙanta da kashi 22 da ake ciki a lokacin da Tinubu ya karɓi mulki.

    A haka ma an samu raguwa ne idan aka kwatanta da kashi 34 da aka samu a shekarar da ta gabata, lamarin da ya janyo zanga-zanga a sassan ƙasar har ta kai ga asarar rayuka.

  3. Faransa za ta haramta shan sigari a kusa da yara

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Faransa za ta haramta shan taba sigari a wuraren da yara ke zuwa.

    Ministar lafiya, Catherine Vautrin ta ce haramcin zai fara aiki ne daga ranar ɗaya ga watan Yuli kuma wuraren da dokar za ta shafa sun haɗa da gaɓar teku da wuraren shaƙatawa da shaguna da gefen makaranu da kuma filayen wasanni.

    Vautrin ta ce "Dole ne a haramta shan taba a wuraren da yara suke,'''

    "Ba zai yiwu ba ƴancin wani na shan taba ya shafi ƴancin ƙananan yara na shaƙar iska mai lafiya.'' In ji Vautri

    Ta ce haramcin ba zai shafi mashaya da sauran ba, wajen da yara ba su zuwa.

    Vautrin ta yi bayanin cewa karya dokar zai janyo wa mutum biyan tarar €135.

  4. An kama mutane 41 kan zargin kashe DPO a Kano

    CSP Baba Ali

    Asalin hoton, FB/Abdullahi Haruna Kiyawa

    Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta ce ta kama mutane 41 da ake zargi da hannu a kisan baturen ƴansanda na Rano, CSP Baba Ali.

    Kwamishinan ƴansanda a jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce kisan jami'in nasu babban abin takaici da tashin hankali ne.

    Kisan jami'in ya janyo suka daga ɓangarori da dama, musamman a lokacin da bidiyon mummunan al'amarin ya riƙa yawo a shafukan sada zumunta.

    A cikin sanarwar da rundunar, reshen jihar Kano ta fitar a yau Alhamis, kwamishinan ƴansandan ya ce rundunar tana yin duk abin da ya dace domin ganin an gurfanar da masu hannu a kisan jami'in nata da kuma tabbatar da cewa sun fuskanci hukunci daidai da abin da suka aikata.

    Rundunar ta kuma buƙaci jama'a su ci gaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum, yayin da jami'an rundunar ke ci gaba da aikin zaƙulo masu hannu a kisan da ma sauran laifuka domin su fuskanci hukunci.

  5. Ambaliya ta kashe sama da mutum 20 a jihar Neja

    BAGO

    Asalin hoton, Facebok/Mohammed Umaru Bago

    Hukumomi a jihar Neja da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 21 sanadiyyar wata mummunar ambaliyar ruwa a ƙaramar hukumar Mokwa.

    Haka nan sun ce ya zuwa yanzu akwai aƙalla mutum 10 da ba a san inda suke ba.

    Shugaban hukumar bayar a agajin gaggawa ta jihar, Ibrahim Hussaini ya ce lamarin ya kuma lalata aƙalla gidaje 50 a ƙauyukan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa na ƙaramar hukumar Mokwa, bayan shafe sa'oi ana zabga ruwan sama mai ƙarfi.

    Yanzu haka masu aikin ceto na ci gaba da aikin neman mutanen da ambaliyar ta rutsa da su.

    Wani da abin ya faru a idonsa ya ce ruwa ya mamaye unguwannin a cikin dare bayan mamakon ruwan da aka shatata.

  6. Gwamnatin Sokoto ta bayar da kwangilar sake gina madatsar ruwa ta Lugu

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu

    Asalin hoton, Sokoto State Government

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu

    Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da kwangilar sake gina madatasar ruwan ta Lugu da ke ƙaramar hukumar Wurno a jihar, wadda za ta laƙume naira biliyan 32.4.

    Gwamnan jihar Ahmed Aliyu wanda ya sanya wa kwangilar hannu, ya bayyana cewa madatsar za ta yi matuƙar taimakawa wajen bunƙasa fannin noman rani idan aka kammala ta, bayan da ta rufta a shekarar 2010.

    "Wannan gagarumin aikin ba yana nufin sake gina madatsar ruwan kawai ba - har ma muna sake dawo da wata muhimmiyar fata, da inganta rayuwa tare da bunƙasa ɓangarorin tattalin arziƙi da ke neman tallafi tsawon shekaru," in ji gwamnan.

    Gwamnatin Sokoto ta ɗauko aikin sake gina madatasar ruwan ne tare da haɗin gwiwar Bankin Duniya, kuma aikin zai haɗa da sake gina bangwayen madatsar masu faɗin kilomita 7.1 da sake gina hanyoyin mota da suka haɗa muhimman wuraren da ake noman rani a Wurno, da farfaɗo da filayen noman ranin masu faɗin kadada 1,200 da kuma samar da ma'ajiyar ruwa mai ɗaukar ruwa cubic miliyan 64 da sauran su.

    Madatasar ruwan ta Lugu dai na da muhimmanci a ɓangarorin noma da kiyon kifi da samar da ruwan sha da aikin yi ga al'ummar yankunan.

  7. An zaɓi Sidi Ould a matsayin sabon shugaban Bankin Afirka

    Sidi Ould Tah

    Asalin hoton, X/AFDB_Group

    Bayanan hoto, Sidi Ould Tah

    An zaɓi tsohon Ministan raya tattalin arziki na Maurtaniya, Sidi Ould Tah a matsayin shugaban Bankin raya ƙasashen Afirka.

    Ya kama aiki ne daidai loacin da bankin ke fuskantar barazanar hasarar dala miliyan dubu biyar daga tallafin da ƙasar Amurka ke bayarwa domin tallafa wa ƙasashen Afirka masu ƙaramin ƙarfi.

    A jawabinsa bayan karɓar muƙamin, ya ce zai yi ƙoƙarin tabbatar da an dama da su ɓangaren ciniki da sauran ƙasashen duniya.

    Ya kuma yi fatan yawan jama'a da nahiyar Afirka ke da shi zai taimaka mata wajen buƙasa tattalin arzikinta.

    Sabon shugaban ya karɓi muƙamin daga hannun tsohon shugaban bankin ɗan Najeriya, Akinwumi Adesina.

  8. Isra'ila ta amince da shawarar tsagaita wuta a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta ce Isra'ila ta amince da tayin tsagaita wuta da Amurkan ta gabatar mata game da rikicin Gaza.

    Sakatariyar yaɗa labaran fadar White House, Karoline Leavitt, ta shaida wa manema labarai cewa Washington tana jiran martani daga ƙungiyar Hamas.

    Wakilin BBC ya ce da alama ƙungiyar ta karkata ga ƙin amincewa da tayin yarjejeniyar.

    Ya ce wani babban jami'in Falasɗinawa ya shaida mashi cewa sabuwar yarjejeniyar ta fifita buƙatun Isra'ila, musamman a game da kawo ƙarshen yaƙin.

    Rahoton farko ya nuna cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya goyi bayan yarjejeniyar, amma ya jaddada cewa dakarunsa za su ci gaba da zama a Gaza har sai an sako dukkan Isra'ilawan da ake tsare da su.

    Mr Netanyahu ya zargi gidan talabijin ɗin Isra'ila da naɗar tattaunawar da ya yi cikin ofishinsa, a cikin sirri.

  9. Ƙungiyar HURIWA ta yi alawadai da buƙatar Tinubu na karɓo bashin dala biliyan 21.5

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar kare hakin ɗan'adama ta HURIWA ta yi akawadai da neman izinin cin bashi da shugabn ƙasar Najeriya, Ahmed Bola Tinubu ya nema daga majalasar dokoki.

    Dala bilyan 21.5 ,shugaban ƙasar ya nemi izini da ya karɓo bashi daga waje da kuma wasu kuɗin naira bilyan dari 758 a cikin gida.

    Haka zalika, bayan ƙungiyar ta HURIWA ,ƙungiyar SERAP ma daga nata ɓangare ta yi kira ga majalasar dokokin ƙasar da ta yi watsi da wannan buƙata ta karɓo bashi na dala bilyan 24 da shugaban ya nema.

  10. Kotu ta yanke wa wani ɗan tsibbu hukuncin kisa ta rataya bisa laifin kisan almajirinsa

    An yanke wa ɗan tsubbun hukuncin kisa ta hanyar rataya

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a jihar Osun ta yanke wa wani malamin tsibbu mai suna Kabiru Ibrahim hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samun shi da laifin kashe wani abokin hulɗarsa mai suna Lukman Adeleke.

    Kotun mai zaman a garin Iwo dai ta yanke masa hukuncin ne bayan samun shi da laifukan hada baki, da kisan kai da kuma sata.

    Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun Justice Lateef Adegoke ya ce masu shigar da ƙara sun tabbatar da hujjojin da ke nuna cewa malamin ya aikata kisa da kuma sata.

    Saboda haka Justice Adegoke ya yanke ma sa hukuncin ɗaurin shekaru bakwai kan sata da kuma kisa ta hanyar rataya saboda kisan kisan kai.

    Wata sanarwa daga ma’aikatar sharia ta jihar Osun ta ce lauyoyin gwamnati sun shaida wa kotun cewa Kabiru Ibrahim, malamin marigayi Adeleke ne kuma ya fada masa shirin da yake na sayen wani fili ne, sai malamin ya ce masa ya zo da kudin da dare a yi musu addu’a kafin ya je ya biya filin.

    Iyalin wanda aka kashen sun ce Adeleke ya yi ɓatan dabo bayan tafiya wurin malamin don yi ma sa addu’a abin da ya sa suka kai ƙara wajen ‘yansanda.

    Sanarwar ta ce a yayin tambayoyin da ‘yansanda suka yi wa malamin tsibbun ne ya yi ikrarin cewa ya kashe mutumin.

    Daga nan kuma ya kai jami’ai wani wuri inda aka ga gawar Adeleke cikin wani buhu a gefen babbar hanyar Ilesa zuwa Akure.

  11. Mutane sun ɓalle ɗakin ajiyar abinci a Gaza saboda yunwa - WFP

    Gaza

    Asalin hoton, EYAD BABA/AFP

    Hukumar abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya, WFP ta ce "wani gungun masu fama da yunwa" ya ɓalle tare da afka wa ɗakin ajiyar kayan abinci a tsakiyar Gaza.

    An rawaito cewa mutum biyu sun mutu sannan da dama sun jikkata kuma har yanzu hukumar ta ce tana tattara alƙaluma.

    Hotuna sun nuna dubban mutane a lokacin da suke afaka wa ɗakin ajiyar abincin mai suna Al-Ghafari a Deir Al-Balah, inda suka yi awon gaba da buhunan filawa da katan-katan na abinci a daidai lokacin da gunjin bindiga ke tashi.

    Ba a samu tabbacin daga ina ne harbin bindigar yake ba.

    Hukumar ta WFP ta ce matsalar jinƙai a Gaza ta janyo jama'a sun fita daga hayyacinsu bayan kimanin watanni uku da Isra'ila ta hana shigar da kayan jinƙai Gaza, kafin a sassauta a makon da ya gabata.

    Footage showed thousands of people breaking into the Al-Ghafari warehouse in Deir Al-Balah and taking bags of flour and cartons of food as gunshots rang out. It was not immediately clearwhere the gunshots came from or who fired them.

  12. Iran na binciken ɓatan wasu ƴan Indiya uku a cikin ƙasarta

    ...

    Asalin hoton, Family members of the men

    Ofishin Jakadancin Iran da ke Indiya ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan batun ɓatan wasu 'yan asalin Indiya guda uku da suka ɓace a birnin Tehran tun farkon wannan watan.

    Mutanen, dukkansu daga jihar Punjab da ke arewacin Indiya, sun fara ya da zango a Iran a ranar 1 ga Mayu, kafin su ƙarasa Australia, inda aka yi musu alkawarin samun ayyuka da albashi masu tsoka.

    Iyayensu da danginsu sun yi zargin cewa an yi garkuwa da su ne tun isowarsu Iran, kuma suna bukatar fansa har na rupees miliyan biyar (kimanin dala 63,000 ko fam 47,000).

    A ranar Alhamis, ofishin jakadancin Iran ya wallafa a shafin X cewa zai dinga sanar da hukumomin Indiya duk wani cigaba da ake samu a binciken tare da yin gargadi kan haɗarin bin haramtattun hanyoyi wajen shiga ci-rani

    Wannan sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da ofishin jakadancin Indiya a Iran ya ce ya "ɗauki wannan al’amarin da muhimmanci" tare da buƙatar a gaggauta gano inda 'yan Indiyan suke da tabbatar da lafiyarsu.

    Da dama daga cikin 'yan Indiya, musamman daga jihar Punjab, na yawan yin ƙaura zuwa ƙasashe masu da suka ci gaba domin neman aiki da rayuwa mafi inganci.

  13. Ambaliya ta kashe mutane da dama a Jihar Neja

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon wata mummunar ambaliya da ta afku a garin Mokwa, hedikwatar karamar hukumar Mokwa da ke jihar Neja.

    Mazauna yankin sun bayyana cewa ambaliyar ta katse hanyar da ke hade Arewa da Kudancin Najeriya ta hanyar Mokwa, lamarin da ya jefa matafiya cikin kunci.

    Kodayake cikakken bayani bai fito ba tukuna, wasu mazauna yankin sun ce kimanin mutane 50 ne suka rasa rayukansu a musibar.

    Har yanzu ana neman wasu mazauna yankin ciki har da mata da ƙananan yara da suka bace. An kuma ruwaito cewa gidaje da dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira sun nutse sakamakon ambaliyar.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ambaliyar ta samo asali ne daga ruwan sama mai ƙarfi da aka yi tsawon sa’o’i da dama a daren Laraba, wanda ya yi sanadin nutsewar gidaje da hallaka rayukan mutane yayin da suke bacci.

    Jaridar ta ce daraktan a hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dr. Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

    Ya ce har yanzu hukumar na ci gaba da tattara bayanai kan girman ɓarnar da ambaliyar ta haddasa, kuma za ta fitar da cikakken rahoto da zarar an kammala bincike.

  14. Shahararen marubucin adabin Afrika Ngũgĩ wa Thiong'o ya mutu

    ...

    Asalin hoton, Ngugi wa Thiong'o

    Ngũgĩ wa Thiong'o, wanda ya rasu yana da shekara 87, yana daga cikin manyan shahararrun marubutan Afirka na zamani — marubuci wanda duk da zaman gidan yari da ya taɓa yi, hakan bai ya hana shi rubuce-rubuce ba.

    Ayyukansa sun shafe kusan shekaru sittin suna bayyana sauyin da ƙasarsa Kenya ta fuskanta daga mulkin mallaka har ya zuwa tsarin dimokuraɗiyya.

    Sau da dama Ngũgĩ ya kasance cikin jerin waɗanda ake hasashen za su lashe kyautar Adabi ta Nobel, amma hakan ba ta taɓa tabbata ba, lamarin da ke damun masoyansa a ko da yaushe.

    Har ila yau, shi ne marubucin da ya yi fafutukar ganin ana ci gaba da rubuce-rubuce tare da karanta su a cikin harsunan Afirka na asali.

    An haifi Ngũgĩ a shekarar 1938 da sunan James Thiong’o Ngũgĩ, a lokacin da Kenya ke ƙarƙashin mulkin mallakar Birtaniya. Ya taso a garin Limuru cikin iyalai manoma.

    Duk da iyayensa talakawa ne amma sun yi ƙoƙarin tabbatar da ya samu ilmi inda suka yi ɗawainiyar biya masa kuɗin wata makaranta da ake kira Alliance, wadda ke ƙarƙashin ikon Turawan Birtaniya a lokacin.

  15. Gwamnatin Tinubu ba ta tausayin Ƴan Najeriya - Atiku Abubakar

    ...

    Asalin hoton, Atiku Abubakar/X

    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kakkausar murya, yana mai cewa cikin shekara biyu kacal, gwamnatin ta nuna gazawa, kuma gwamnati ce wadda ba ta tare da jama'a sannan maras jin tausayin talakawa fiye da kowacce gwamnati tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana cewa jam'iyyar adawa ba za ta yi shiru ba yayin da halin rayuwa ke ƙara tsananta ga ‘yan kasa tare da yawaitar almubazzaranci daga bangaren gwamnati.

    Atiku ya ce babu wata gwamnati da ta taɓa jefa al’umma cikin irin wannan ƙunci ba tare da la’akari da gaskiya da rikon amana da jagoranci nagari ba.

    “Wannan gwamnati ta Tinubu ba wai kawai ta ƙara talauci a fadin ƙasar ba ne, har ma ta kafa sabbin tarihi wajen almubazzaranci da kuɗaɗen jama’a.”

    Ya ƙara da cewa a daidai lokacin da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa, jami’an gwamnati suna rayuwa cikin walwala da amincewa da kasafin kuɗi da ke amfana kawai ga attajirai yayin da talakawa ke ci gaba da shan wahala.

    “Abin taƙaici ne yadda Najeriya ba wai kawai ta kasance ƙasa da ke fama da matsanacin talauci a duniya ba, yanzu haka ta zama ƙasar da ke da yawan yara masu fama da rashin abinci fiye da kowacce ƙasa a Afirka, hatta fiye da Sudan — ƙasar da ke fama da yaƙi.” in ji Atiku.

    Ya ce bisa rahoton Global Hunger Index na 2024, Najeriya na daga cikin ƙasashen da suka fi fama da yunwa da rashin abinci, inda take matsayi na 18 a duniya.

    Ya ƙara da cewa duk wani tsarin gwamnati da aka ɗauka a ƙarƙashin wannan mulki ya fi cutar da talakawa fiye da komai, yayin da masu kuɗi ke ci gaba da morewa.

    Atiku ya ce abin da ya fi tayar da hankali shi ne yawan bashin da gwamnatin ke ci gaba da karɓa.

    "A lokacin da Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023, jimillar bashin ƙasar ya tsaya kan naira tiriliyan 49. Amma cikin shekaru biyu kacal da fara mulki, ya karu zuwa tiriliyan 144 yayin da kuma ake shirin karɓar ƙarin bashi daga ƙasashen waje wanda zai iya kai bashin ƙasar zuwa tiriliyan 183.”

    Atiku ya ce su a matsayin su na jam'iyyar adawa da masu kishin kasa, ba za su zuba ido ba su kalli abubuwan da ke faruwa ba su ci gaba.

  16. Manyan abubuwa guda biyu ƙarƙashin Tinubu da suka sauya Najeriya - Idris

    Yayin da shugaba Tinubu na Najeriya ke cika shekaru biyu na mulkinsa, ministan labarai na ƙasar, Mohammed Idris ya nemi ƴan Najeriya su ƙara haƙuri dangane da wahalhalun da suka sha domin a cewarsa al'amura za su yi sauƙi nan gaba.

    Ministan ya ce lallai akwai wasu sassan da ke son gyara, amma kuma ya lissafa abubuwa guda biyu da ya ce sun sauya Najeriya.

  17. Fiye da mutum 10,000 sun mutu ƙarƙashin mulkinTinubu - Amnesty International

    ...

    Asalin hoton, Tinubu/X

    Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan nan ya nuna cewa, cikin shekaru biyu da gwamnatin Tinubu ta hau mulki, an kashe aƙalla mutum 10,217 a hare-haren da 'yan bindiga suka kai a jihohi daban-daban.

    Jihohin sun haɗa da Benue da Edo da Katsina da Kebbi da Plateau da Sokoto da Zamfara.

    Jihar Benue ce ke da mafi yawan adadin mutanen da aka kashe – inda ya kai har mutum 6,896, sai Jihar Plateau da mutum 2,630.

    Amnesty International, wadda ta fitar da wannan rahoto a cikar shekaru biyu na shugaban Najeriya, Bola Tinubu kan ƙaragar mulki ta zargi gwamnatinsa da gazawa wajen kare rayukan 'yan kasa da kuma gurfanar da waɗanda ke da hannu a aikata laifuka duk da alkawurran da gwamnatin ta sha yi na inganta tsaro.

    Rahoton ya kuma bayyana cewa "an raba ɗaruruwan ƙauyuka da muhallansu musamman a Zamfara da Benue da Plateau, inda dubban mutane suka rasa matsugunansu."

    "Hare-haren sun kuma lalata ababen more rayuwa da suka haɗa da rijiyoyin burtsatse da makarantu da asibitoci wanda hakan ya kara tsananta halin da jama’a ke ciki." rahoton ya ƙara da cewa.

    Amnesty International ta gargadi cewa korar manoma daga gidajensu na kara haddasa yunwa da talauci.

    A jihar Plateau, an bayyana cewa mutum 65,000 ne suka rasa matsugunansu, a Benue kuwa adadin ya kai 450,000.

    "Sababbin ƙungiyoyin 'yan bindiga da suka hada da Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi, da Mamuda a Kwara, na kara tsananta rikici." in ji rahoton

    Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati da ta dauki matakan gaggawa domin dakile irin waɗannan hare-hare da kisan gilla, tana mai cewa “lokaci na kurewa, yayin da hare-haren ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya ke kara tsananta.”

  18. Ko Tinubu ya sauke rabin alƙawarin da ya ɗauka bayan shekara biyu?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Najeriyar yanzu, babu ko shakka ta sha bamban da Najeriyar da aka sani shekara biyu da suka gabata, lokacin da Bola Tinubu ya karbi mulkin ƙasar.

    Abubuwa da dama sun sauya tun daga lokacin da aka rantsar da sabon shugaban ƙasar, inda nan take ya furta ɗaya daga cikin manyan manufofin da suka sauya lamurran ƙasar tun bayan samun ƴanci - cire tallafin man fetur.

    Wannan ɗaya ne daga cikin alƙawurran da Tinubu ya ɗauka tun a lokacin yaƙin neman zaɓe.

  19. Isra’ila ta sanar da shirin faɗaɗa matsugunan yahudawa a gaɓar Yamma da Kogin Jordan

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Ministocin Isra'ila sun amince da gina sabbin matsugunan yahudawa guda 22 a gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye, wanda wannan shi ne mafi girma cikin shekaru da dama.

    Yawancin wadannan matsugunan tuni a riga a gina su a matsayin wuraren zama ba tare da izini daga gwamnati ba, amma ministan tsaro Israel Katz da ministan Kuɗi Bezalel Smotrich sun tabbatar cewa yanzu za a halasta su bisa doka ta Isra’ila.

    Yawancin al’ummar duniya na ganin wadannan matsugunan ba bisa doka bane kuma ba bisa ka’idojin ƙasashen duniya sai dai Isra’ila na kalubalantar wannan ra’ayi.

    Katz ya bayyana cewa faɗaɗan matsugunan na da nufin hana kafuwar ƙasar Falasɗinawa, wadda yake ganin za ta zama barazana ga Isra’ila.

    Tun bayan yaƙin Gabas ta Tsakiya na 1967, Isra’ila ta gina kusan matsugunan yahudawa 160 a gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Gabashin Ƙudus, inda yanzu yahudawa kusan 700,000 ke zaune.

  20. Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya sa shi na tsuke bakin aljihun gwamnati

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta barin mukaminsa na shugabancin hukumar tsuke bakin aljihun gwamnatin Amurka da ake kira da Doge karkashin jagorancin shugaba Trump.

    Musk ya jagoranci hukumar da ake kira Doge, wajen rage dubban ma'aikatan gwamnatin ƙasar, abun da ya haifar da babbar suka.

    Sai dai tafiyar ta sa ta zo ne a yayin da rashin jituwa ke daɗa ƙamari tsakaninsa da shugaba Trump, bayan ya soki wani ƙudurin shugaban da ya ce zai haifar da gagarumin giɓi ga gwamnati, wani abu da ya ce zai shafi aikinsa.

    Sai dai duk da haka, ya miƙa godiyarsa ga shugaba Trump bisa damar da ya bashi, yana cewa hukumar za ta ci gaba da yin karfi.