Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Sallama

    Masu bibiyarmu nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.

    Sai kuma gobe idan Allah ya ka mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan, mu kwana lafiya

  2. Babu hannuna a korar Wike daga PDP - Fintiri

    Ahmadu Umaru Fintiri

    Asalin hoton, Ahmadu Umaru Fintiri/X

    Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya nesanta kansa daga matakin da jam'iyyar PDP ta ɗauka na korar ministan Abuja, Nyesom Wike da wasu daga jam'iyyar.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinta X, Ahmadu Fintiri ya ce ya yi imanin cewa babu abin da matakin zai haifar sai ƙara dagula jam'iyyar.

    Da maraicen yau Asabar ne PDP ta fitar da sanarawar korar Wike da wasu jiga-jigan jam'iyyar saboda abin da ta kira yi mata zagin-ƙasa.

    Jam'iyyar ta ce ta ɗauki matakin ne a wajen babban taronta na ƙasa da ke gudana a birnin Ibadan na jihar Oyo, bisa amincewar mafiya rinjayen ƴaƴanta.

    Sai dai gwamnan na Adamawa wanda ke cikin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ya nesanta kansa da matakin.

    ''Ni, Ahmadu Umaru Fintiri, gwamnan Adamawa ina son na bayyana ƙarara cewa na nesanta kaina daga wannan matsayi da PDP ta ɗauka na dakatar da Wike daga cikinta''.

    Gwamnan ya ƙara da cewa ba zai goyi bayan duk wani mataki da zai ƙara jefa jam'iyyar cikin rikici ba.

    ''A matsayina na halastaccen ɗan jam'iyya, ina goyon bayan zaman lafiya da kwanciyar hankalin jam'iyyarmu, don haka ba zan goyi bayan duk wani mataki da zai wargaza ta ba'', in ji Fintiri.

    Gwamnan ya kuma yi kira ga jam'iyyar ta rungumin hanyoyin sasanci domin warware duka matsalolin da jam'iyyar ke fuskanta.

  3. Ƴanbindiga sun kashe wani fitaccen ɗansiyasa a Zamfara

    Moriki

    Asalin hoton, B. Moriki

    Ƴan bindiga sun kashe wani fitaccen ɗansiyasa a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Alhaji Umar S Fada Moriki na ɗaya daga cikin jiga-jigan ƴansiyasar jihar.

    Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne ranar Asabar da safe a kan babban titin Gusau zuwa Tsafe, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Gusau.

    Cikin wata sanarwa da jam'iyyar APC reshen jihar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Yusuf Idris ya ce marigayin ya gamu da ajalinsa ne bayan halartar taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar, wanda ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Mohammed Bello Matawalle ya jagoranta.

    Mai shekara 62 ya taɓa rike mukamin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zurmi, sannan ya riƙe muƙamin babban darakta a wata hukuma kafin ya zama mataimakin gwamna na musamman kan samar da lantarki a karkara.

    A zaɓukan 2023 da suka gabata ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar ƙananan hukumomin Zurmi da Shinkafi.

  4. Fafaroma ya buƙaci masu shirya film su taimaka a yaƙi rashin adalci

    Fafaroma

    Asalin hoton, Getty Images

    Fafaroma Leo ya buƙaci masu shirya fina-finai su yi amfani da fasaharsu wajen yaƙi da ƙunci da rashin adalci da wasu al'umma ke fuskanta.

    Ya gana da masu shirya fina-finan ne a wajen wani taron baje kolin basira, inda manyan ƴan fim suka taru.

    Fafaroma Leo ya ce shirin fim, hanya ce ta bayar ad gudunmuwa ga ci gaban duniya da kuma ƙarfafa gwiwar masu ƙaramin ƙarfi.

    Jaruman fina-finan sun kuma gabatar da kyautuka ga babban limamin na Katolika.

  5. Labarai da dumi-dumi, Jam'iyyar PDP ta kori Nyesom Wike

    Wike

    Asalin hoton, Nyesom Wike

    Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta sanar da korar ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu jiga-jiga daga cikinta, saboda abin da ta kira yi wa jam'iyya zagon-ƙasa.

    Cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce ta ɗauki matakin ne domin kawo haɗin kai da ladabtarwa a jam'iyyar da kuma mayar da hankali ga zaɓukan 2027 masu zuwa.

    Sauran mutanen da jam'iyyar ta kora sun haɗar da Samuel Anyanwu da Kamaldeen Ajibade da Ayo Fayose da Austin Nwachukwu da kuma wasu.

    Sanarwar ta ce matakin ya samu amincewar mafiya rinjayen wakilan jam'iyyar da ke halartar babban taronta na ƙasa da ke gudana a birnin Ibadan na jihar Oyo.

  6. 'Gwamnonin Osun da Rivers da Taraba ba su hartarci taron PDP ba'

    Fubara

    Asalin hoton, Siminalayi Fubara/Facebook

    Rahotonni daga birnin Ibadan na jihar Oyo na cewa gwamnonin jihohin Osun da Taraba da kuma Rivers ba su halarci babban taron jam'iyyar PDP da ke guda a birnin ba.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa ba a ga fuskokin gwamnonin a wurin taron ba.

    Babbar jam'iyyar hamayyar ta Najeriya na gudanar da babban taronta na ƙasa domin zaɓen sabbin shugabanninta.

    An dai samu mabambantan umarnin kotuna da suka ci karo da juna game da taron, inda wasu suka bai wa jam'iyyar damar ci gaba da taron, yayin da wasu kuma suka hana.

    Jam'iyyar ƙarƙashin tsagin shugabanta na ƙasa, Amb. Iliya Damagum ta ci gaba da gudanar da taronta a birnin na Ibadan.

    Kawo yanzu gwamnonin da suka hallara a wurin taron sun haɗar da na jihohin Bauchi da Plateau da Zamfara da kuma Oyo mai masaukin baƙi.

    Haka kuma akwai tsoffin gwamnonin jihohin Akwa Ibom da Neja da kuma Kano.

  7. Sulhun da ake yi da ƴanbindiga a Katsina ne ke haifar da hare-haren Kano

    Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

    Asalin hoton, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

    Jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce sulhu da ƴanbindiga da wasu al'umomin jihar Katsina ke yi ne ya janyo samun hare-hare a wasu yankunan jihar Kano.

    Yayin da yake jawabi a wurin taron yaye ɗalibai na jami'ar skyline da ke Kano, Sanata Kwankwaso ya ce gwamnatin tarayya ce ya kamata ta yi sulhu ba ƙaramar hukuma ba.

    Tsohon gwamnan jihar Kanon ya ce ƴan bindiga na shiga Kano daga Katsina su kashe mutane bayan sulhu a wasu ƙananan hukumomi.

    ''Babu laifin sulhu amma dole gwamnatin tarayya ta sa baki, babu ma'ana ƙaramar hukuma ɗaya ta ɗauki matakin ita kaɗai, dole gwamnatin tarayya ta sa baki'', in ji shi.

    Kwankwaso ya kuma yi kira ga shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ƙara mayar da hankali kan matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

    Dole shugaban ƙasa ya nuna jajircewa a matsayin babban kwamandan hafoshin tsaro.

  8. Abubuwan fashewa sun raunata mutum 20 a Argentina

    Kafar yada labarai ta Argentina ta ce akalla mutum 20 sun ji rauni bayan fashewar abubuwa a wani rukunin masana'atu da ke kusa da babban birnin kasar.

    Fashewar abubuwan da aka samu a wasu gine-gine sun haɗa da ta wasu sinadarai da ake amfani da su wajen aikin noma, kuma sun jawo tashin gobara a wurin.

    Wasu bidiyo sun nuna yadda wutar ke tashi, ga kuma bakin hayaƙi duk ya turnuke sararin samaniya.

  9. Sojan sama na Najeriya sun kashe 'yanfashin daji a jihar Zamfara

    Jirgin saman yaƙi na Najeriya

    Asalin hoton, Nigeria Airforce

    Rundunar sojan sama ta Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe 'yanfashi da dama waɗanda ba ta faɗi adadinsu ba a garin Tsafe na jihar Zamfara bayan wani hari ta sama.

    Mai magana da yawun rundunar,,Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an kai hare-haren ne kan sansanin 'yanfashi na Sauri ranar Juma'a bayan tattara bayanan siri.

    Ya ce bayanai sun tabbatar da 'yanbindigar na karakaina a wurin da suka ɓoye shanun sata da ke kan wani tsauni da ke ba su kariya da kuma ajiye kayayyaki.

    "An kai hare-hare da dama waɗanda suka dira kan 'yanfashin da ke yunƙurin guduwa cikin duhun daji, inda aka bi su kuma aka kashe su," in ji sanarwar.

  10. Mayaƙan Iswap sun kashe sojojin Najeriya da 'yan sa-kai a jihar Borno

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Army

    'Yanbindiga da ake zargin na ƙungiyar Iswap ne masu iƙirarin jihadi sun kashe dakarun sojan Najeriya biyu da 'yan sa-kai na CJTF biyu sakamakon kwanton ɓauna da suka yi musu a garin Damboa na jihar Borno.

    Wata sanarwa da rundunar sojan Najeriya ta fitar a yau Asabar ta ce dakarunta na tsaka da aikin fatiro ranar Juma'a ƙarƙashin jagorancin kwamandan rundunar 25 Brigade, Birgediya Janar M Uba, lokacin da maharan suka far musu a Wajiroko.

    "Dakarun sun yi bajintar kauce wa kwanton ɓaunar 'yanbindigar, inda suka tilasta musu tserewa ba tare da cimma manufarsu ba," kamar yadda Laftanar Kanar Appolonia Anele ya bayyana cikin sanarwar.

    A gefe guda kuma, rundunar ta musanta rahotonnin da wasu kafofin yaɗa labarai a Najeriya suka ruwaito cewa maharan sun yi garkuwa da Janar Uba yayin harin.

    Tun da farko rahotonnin sun ce janar ɗin ya koma sansaninsu a ƙafa bayan kubuta daga hannun 'yanbindigar.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa maharan sun ƙwace baburan hawa 17 a lokacin harin.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Ba ni goyon bayan taron PDP saboda nasarar da na yi a kotu - Sule Lamido

    Sule Lamido

    Asalin hoton, Facebook/Sule Lamido

    Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido ya ce ba shi goyon bayan babban taron jam'iyyarsu ta PDP kuma ba zai je taron ba saboda nasarar da ya yi a ƙorafin da ya shigar gaban kotu na dakatar da taron.

    Lamido ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan kotun tarayya a Abuja ta umarci PDP ta dakatar da shirin taron har sai ta ba shi damar yin takarar shugabancin jam'iyyar.

    "Na je kotu ne domin ƙwato 'yancina da jam'iyyata ta ƙwace," a cewarsa cikin wata hira da gidan talabijin na Channels TV a yammacin Juma'a.

    Haka nan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Lamdio ya musanta labarin da ya ce ana yaɗawa cewa ya janye ƙarar tun kafin a yanke hukuncin bayan ganawarsa da gwamnan Oyo kuma wai yana goyon bayan taron.

    "Ba zan je taron da kotu ta yi hukunci a kansa ba. Me ya sa zan je? Idan na je taron na yi watsi da nasarar da na samu kenan. Zan yi biyayya ga hukuncin kotun saboda ni mai biyayya ne ga jam'iyya da ya yarda da doka da oda."

    A makonnin da suka gabata ne tsohon gwamnan ya zargi PDP da "juya masa baya" bayan an hana shi sayen tikitin takara domin neman muƙamin shugaban jam'iyyar na ƙasa, wanda za a gudanar a yau Asabar da Lahadi.

  12. Kalli yadda filin taron PDP ya ɗauki harama

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo

    Ana gudanar da taron ne a birnin Ibadan na jihar Oyo da ke kudancin ƙasar, kuma jam'iyyar ce ke mulkin jihar ƙarƙashin Gwamna Seyi Makinde.

    Ana sa ran wakilai kusan 3,000 ne za su kaɗa ƙuri'unsu a yau Asabar zuwa Lahadi domin zaɓen sabon shugabancin jam'iyyar a matakin ƙasa domin maye gurbin na yanzu ƙarƙashin Umar Ilya Damagun.

  13. Filin taron PDP ya ɗauki harama

    Taron PDP a Ibadan

    Asalin hoton, PDP

    Shugabanni da wakilai da magoya bayan babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP sun yi wa filin wasa na Lekan Salami tsinke domin halartar babban taronta na ƙasa.

    Ana gudanar da taron ne a birnin Ibadan na jihar Oyo da ke kudancin ƙasar, kuma jam'iyyar ce ke mulkin jihar ƙarƙashin Gwamna Seyi Makinde.

    "Duk wanda ya kamata ya zo wurin nan ya zo, gwamnonimu da sanatoci masu-ci da marasa ci dukkansu suna nan mun hallara a Ibadan," kamar yadda ɗan kwamatin amintattun PDP Farfesa Umar Tsauri ya shaida wa BBC.

    Ana sa ran wakilai kusan 3,000 ne za su kaɗa ƙuri'unsu a yau Asabar zuwa Lahadi domin zaɓen sabon shugabancin jam'iyyar a matakin ƙasa domin maye gurbin na yanzu ƙarƙashin Umar Ilya Damagun.

    Sai dai ana gudanar da taron ne bayan umarnin kotu aƙalla biyar daga shari'o'i aƙalla uku da suka ce a yi taro ko kada a yi bisa dalilai daban-daban.

  14. Bam ya kashe mutum shida a ofishin 'yansandan Indiya

    Kashmir na Indiya

    Asalin hoton, EPA

    Kafar yaɗa labaran Indiya ta ce akalla mutum shida sun mutu bayan wani abu ya fashe a ofishin 'yansanda da ke yankin Kashmir na ƙasar.

    Wuta ta tashi a wani gini da ke Srinagar a daren jiya. Har yanzu ba a san abin da ya haddasa fashewar ba.

    Wakilin BBC ya ce rahotanni sun ce ana tunanin lamarin da ya faru tsautsayi ne, kuma da alama ya faru ne lokacin da ake kokarin adana wasu abubuwan fashewa a wani wuri da ke da nisa daga inda lamarin ya aufku.

  15. Umarnin kotu na biyar ya goyi bayan taron PDP na ƙasa

    Wasu 'yan PDP

    Asalin hoton, PDP

    Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya za ta shiga babban taronta na ƙasa da ƙwarin gwiwa sakamakon sabon umarnin kotu da ya goyi bayan taron.

    Cikin hukuncin da ta bayar a jiya Juma'a, babbar kotun jihar Oyo ta ce jam'iyyar ta ci gaba da shirin yin taron kamar yadda ta tsara, sannan ta nemi hukumar zaɓe Inec ta tura wakilai domin saka ido kan sa.

    Mai Shari'a Ladiran Akintola ya jaddada umarnin da ya bayar na ranar 3 ga watan Nuwamba, wanda ya hana shugabancin jam'iyyar ɗaukar duk wani matakin da zai kawo tsaiko ga taron.

    Wannan ne umarnin kotu aƙalla na biyar da ya goyi bayan taron ko akasin haka tun daga watan Oktoba, yayin da Ministan Abuja da abokan siyasarsa ke adawa da gudanar da shi.

    Tuni wakilai da 'ya'yan jam'iyyar suka yi wa filin wasa na Lekan Salami tsinke a birnin Ibadan na jihar ta Oyo domin halartar taron Asabar da Lahadi, inda za a zaɓi sababbin shugabanni a muƙamai daban-daban.

  16. Kwamatin amintattu na PDP ya yi watsi da rahoton kwamatin sasantawa

    Shugabannin PDP

    Asalin hoton, PDP

    Kwamatin Amintattu na jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ya yi watsi da rahoton kwamatin sasantawa da aka kafa domin haɗa kan 'ya'yan jam'iyyar a ƙasa baki ɗaya.

    A cewar rahotonni, kwamatin ya bayar da shawara a ranar Alhamis cewa a dakatar da babban taro na Ibadan har sai an samu cikakken umarnin kotu da ya ce a yi hakan da kuma goyon hukumar zaɓe ta Inec.

    Sannan kwamatin, ƙarƙashin jagorancin Hassan Adamu, ya bayar da shawarar kafa kwamatin riƙon ƙwarya na shugabanci saboda yawan umarnin kotuna masu karo da juna kan babban taron.

    Sai dai wata sanarwa da shugaban kwamatin amintattun, Sanata Adolphus Wabara, ranar Juma'a ya ce shawarwarin da kwamatin sasantawar ya bayar ba su dace da matsayar shugabancin jam'iyyar ba.

    "Kwamatin amintattu na bayyanawa ƙarara cewa abubuwan da rahoton ya ƙunsa bai dace ba kuma ba su matsayar amintattun ba," in ji sanarwar.

    "Idan kwamatin amintattu bai amince da shi ba ba zai taɓa zama matsayar jam'iyya ba."

  17. Trump zai nemi BBC ta biya shi diyyar dala biliyan biyar a kotu

    Donald Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Trump ya ce zai shigar da BBC ƙara ta neman diyyar dala biliyan biyar duk da afuwar da ta nema kan wani bidiyon rahotonsa da ta haɗa kuma ta cire wasu kalamansa.

    An wallafa rahoton ne game da jawabin da ya yi jim kaɗan kafin harin da magoya bayansa suka kai majalisar dokokin Amurka a watan Janairun 2021.

    Mista Trump ya shaida wa manema labarai cewa watakila a mako mai zuwa ne zai shigar da karar, sannan zai yi magana da firaministan Birtaniya kafin lokacin.

    BBC ta nemi afuwar shugaban bayan da ta amince cewa ta yi kuskure wajen cire wani ɓangare na jawabinsa, wanda kuma hakan kuskure ne.

    Amma duk da haka BBC ta yi watsi da batun bukatarsa ta biyan diyya, tana mai cewa babu wata hujja ta ɓata suna a cikin rahoton.

  18. Maraba

    Mun sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Asabar.

    Ku biyo mu domin sanin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.