Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 05/06/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail

  1. Netanyahu ta tabbatar da bai wa ƴan bindigar da ke adawa da Hamas a Gaza makamai

    Firaiministan Isra'ila Benjamen Netanyahu ya tabbatar gwamnatinsa na bai wa ƴan bindigar da ke adawa da Hamas a Gaza makamai.

    Wata ƙabila da ta yi sansani a Rafah ta yi iƙirarin samar da tsaro ga jerin gwanon kayan agaji, amma aka zarge su da sata.

    Da yake martani game da ikirarin cewar yana baiwa ƙungiyoyin masu laifi makamai, Mista Netanyahu ya ce ya yi amfani da abokan adawar Hamas wajen tserar da rayuwar sojin Isra'ila.

    Wani ɗan siyasar adawa Yair Golan ya ce Mista Netanyahu ya zama barazana ga tsaron Isra'ila.

  2. Hotunan yadda alhazai suka isa filin Muzdalifa bayan saukowa daga Arfa

    Mahajjata

    Asalin hoton, Life Inside Saudi Arabia/X

    Bayanan hoto, Wasu mahajjata kwance a filin Muzdalifa

    Mahajjata sun isa filin Muzdalifa, inda za su kwana kafin gobe su tafi wurin jifa, Alhazan sun safe wunin yau a filin arfa suna gudanar da addu'o'i.

    Mahajjata

    Asalin hoton, Life Inside Saudi Arabia/X

    Bayanan hoto, Wasu alhazai lokacin da suke tsintar duwatsun da za su ji jifa da su a gobe
    Mahajjata

    Asalin hoton, Life Inside Saudi Arabia/X

    Bayanan hoto, Fiye da mutum miliyan 1.6 ne ke gudanar da aikin hajjin a wannan shekara
    Mahajjata

    Asalin hoton, Ministry Of Hajja and Umrah

    Bayanan hoto, Alhazan sun taho ne daga filin Arfa, wasu a ƙafa yayin da wasu suka shiga ababen hawa
    Mahajjata

    Asalin hoton, Ministry Of Hajja and Umrah

    Bayanan hoto, Aikin Hajji ɗaya ne daga shika-shikan Addinin Musulunci
  3. Ba don ni ba da Trump bai ci zaɓe ba - Elon Musk

    Trump da Musk

    Asalin hoton, Reuters

    Gagarumar rigima ta kaure tsakanin Shugaban Amurka, Donald Trump da tsohon mai ba shi shawara, Elon Musk, bayan da biloniyan ya soki shugaban ƙasar kan sabbin dokokinsa kan haraji.

    Cikin wani saƙo da hamshaƙin attajirin ya wallafasa ya shafinsa ya X, ya yi wa Trump gori da cewa ba don taimakonsa ba da Trump din ya fadi zaɓn shugaban ƙasar.

    Sannan ya ci gaba da cewa ba don taimakon da ya bayar ba da tuni jam'iyyar demokrats ce ke da rinjaye a majalisar dattawan ƙasar.

    To sai dai a martanin da shugaba Trump ya mayar ya ce Elon Musk ya ba shi kunya, yana mai cewa attajirin ya fara sukarsa ne bayan da ya yanke tallafin da ake bai wa ababen hawa masu amfani da lantarki.

    Mista Musk - wanda ya ajiye aikinsa a gwamnatin Trump a makon da ya gabata - ya zargi Shugaba Trump da rashin godiyar Allah.

  4. Za ku iya samun ƙarin labaran BBC Hausa a tasharmu ta WhatAspp. Ku shiga ta a nan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Tanzaniya ta rufe kafar sada zumunta ta X saboda 'yaɗa batsa', Farouk Chothia

    Shugaba Samia Saluhu Hassan

    Asalin hoton, Tanzania State House

    Bayanan hoto, Shugabar Tanzaniya, Samia Saluhu Hassan

    Ministan yaɗa labaran Tanzaniya ya ce ƙasar ta yanke shawarar rufe shafin sada zumunta a X, saboda yana bari ana yaɗa hotuna da bidiyon batsa.

    Jerry Silaa ya shaida wa gidan talbijin na ƙasar cewa hakan ya saɓa wa dokoki da al'adu da ɗabi'un ƴan ƙasar

    Makonni biyu da suka gabata, ƴan ƙasar suka bayar da rahoton taƙaita amfani da shafin saboda rikici na siyasa tare da kutse a shafin rundunar ƴansandan ƙasar, sai dai har yanzu ba a kammala rusfe shafin ba.

    Ƙungiyoyn kare haƙƙin bil'adama a ƙasar na sukar matakin da cewa wani nau'i ne na toshe musu ƴancin faɗa albarkacin baki, musamman a wannan lokaci da ƙasar ke tunƙarar zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisa cikin watan Octoba.

    Gwamnatin shugabar ƙasar, Samia Saluhu Hassan na ci gaba da shan zargin yin ƙarfa-ƙarfa, yayin da take yain neman zaɓen wa'adi na biyu.

    Cikin wani saƙo da ƙungiyar kare haƙƙin bl'adama ta LHRC ta wallafa, ta ce a lokacin zaɓukan 2020 ma gwamnatin ƙasar ta rufe shafin X, kuma wannan sabon mataki, na ƙara tuna wa jama'a yadda Tanzaniya ta koma mai tauye ƴancin mutane.

  6. Lokaci ya yi da ya kamata a fara zaɓen wuri a Najeriya - Shugaban Sojoji

    Hafsan sojin ƙasa

    Asalin hoton, Defence HQ/X

    Babban hafsan rundunar sojin ƙasa ta Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya nuna goyon bayansa kan ƙudirin zaɓen wuri da majalisar dattawan ƙasar ta gabatar.

    Janar Olufemi Oluyede, ya ce hakan zai taimaka wa jami'an sojin da ake girkewa domin bayar da tsaro a ranar zaɓe.

    Yayin da yake jawabi ga tawagar majalisar dattawa da suka kai ziyara shalkwatar tsaron ƙasar, ranar Alhamis, babban hafsan ya bayyana ƙudirin a matsayin abin da ya zo a daidai lokacin da ake buƙatarsa.

    “Ayyukanmu a lokacin zaɓe shi ne samar da yanayi mai kyau ga ƴan ƙasa domin kaɗa ƙuri'unsu, kuma saboda wannan aiki yana da matuƙar wahala ga duk sanye da kayan sarki ya samu damar kaɗa ƙuri'a,” in ji shi.

    A watan da ya gabata ne majalisar dattawan Najeriya ta gabatar da ƙudurorin yin kwaskwarima ga dokokin zaɓen ƙasar, inda majalisar ta bijiro da sabbin dokoki, ciki har da ƙudirin zaɓen wuri ga masu ayyuka na musamman a ranar kamar kamar jami'an tsaro da masu aikin zaɓen.

    Ƙasashen duniya da dama dai na gudanar da zaɓen wuri, cikin har da Ghana da ta ɓullo da shi a baya-bayan nan.

  7. Tarayyar Afirka ta nuna damuwa kan haramta wa 'yan wasu ƙasashe shiga Amurka

    AU

    Asalin hoton, @ymahmoudali

    Hukumar Tarayyar Afirka ta bayyana damuwa kan matakin da gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Donald Trump ta ɗauka na sanya takunkumin tafiye-tafiye ga 'yan ƙasashe bakwai na Afirka.

    Cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, African Union (AU) ta amince cewa kowace ƙasa na da ikon kare iyakokinta da tabbatar da tsaron cikin gida.

    Sai dai ta buƙaci gwamnatin Amurka da ta aiwatar da irin wadannan matakai "cikin adalci bisa hujjoji" kuma "bisa la’akari da dangantaka ta dogon lokaci da ke tsakanin Afirka da Amurka".

    "Har yanzu hukumar na nuna damuwa kan yadda irin wannan mataki ka iya haifar da illa ga dangantakar mutane da musayar ilimi da cinikayya da hulɗa ta diflomasiyya da aka shafe shekaru ana ginawa,” in ji sanarwar.

    Ƙungiyar ta buƙaci Amurka ta buɗe kofar tattaunawa da ƙasashen Afirka da abin ya shafa domin warware matsalolin da suka kai ga ɗaukar wannan mataki na takunkumi da hana shiga cikin ƙasar.

    A jiya ne gwamnatin Trump ta haramta tafiye-tafiye ga kasashen Congo Brazzaville, da Equatorial Guinea, da Eritrea, da Somalia, da Chadi, da Sudan, da kuma Libya.

  8. An gurfanar da mutanen da ake zargi da kisan DPO a Kano

    Kwamishinan ƴansandan jihar Kano

    Asalin hoton, Abdullahi Haruna Kiyawa/Facebook

    Bayanan hoto, Kwamishinan ƴansandan jihar Kano, CP Adamu Bakori

    Rundunar ƴansandan jihar Kano ta gurafanr da wasu mutu 29 da take zargi ta da hannun a kisan Baturen ƴansanda na aramar Hukumar Rano, CSP Baba Ali.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce bayan kammala bincike ta gurfanar da mutanen a gaban kotun majistare da ke, Nomansland a birnin Kano.

    Rundunar ta ce daga cikin mutanen da ta gurfanar har da mutum 14 da take zargi da hannu dumu-dumu a kisan Baturen ƴansandan.

    A cikin watan da ya gabata ne aka zargi wasu matasa da kisan Baturen ƴansanda, sakamakon wani hargitsi da ya tashi bayan mutuwar wani matashi a hannun jami'an ƴansanda, wani abu da matasan suka zargi ƴansanda da sakaci a mutuwar matashin.

    Rundunar ƴansandan ta sha alwashin tabbatar da gaskiya da adalci da a wannan shari'a.

  9. Chadi ta dakatar da bayar da biza ga ƴan Amurka da ke son shiga ƙasar

    Mahamat Deby

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Deby

    Ƙasar Chadi ta ce za ta dakatar da bayar da biza ga ƴan Amurka da ke son shiga ƙasar, a wani ɓangare na martanin haramcin shiga Amurka da Trump ya sanya wa wasu ƙasashe ciki har da Chadin.

    Cikin wani saƙo da shugaban ƙasar, Mahamat Deby ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya ce gwamnatinsa za ta mayar da martani yadda ya kamata, ta hanyar dakatar da hayar da biza ga Amurkawa da ke son shiga ƙasarsa.

    "Chadi ba ta da jirage ko biliyoyin dalolin da za ta bayar amma tana da ƙima da daraja'', kamar yadda ya wallafa a shafin nasa.

    Chadi na cikin ƙasashen Afirka bakwai da sabuwar dokar hana shiga Amurka ta shafa.

    Shugaban na Chadi ya kuma gargaɗin yan ƙasarsa kan yunƙurin shiga Amurkan.

    "Daga yau mun dakatar da ƴan Chadi daga shiga Amurka a matsayin ƴancirani ko ba ƴancirani ba."

    Kawo yanzu dai Amurka ba ta yi martani ba kan martanin ƙasar ta Chadi.

  10. 'Fiye da Alhazai miliyan 1.6 ne suka yi tsayuwar Arfa'

    ..

    Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce mutum miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin hajji a wannan shekara.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce daga cikin wannan adadi, mutum miliyan 1,506,576 ƴan ƙasashen waje ne daga ƙasashe 171, yayin da ƴan ƙasar da waɗanda ke zaune a ƙasar 166,654 ke gudanar da ibadar a wannan shekara.

    Hukumar GASTAT ta ce daga cikin masu sauke faralin a bana, mutum 877,841 maza ne yayin da mata suka kai 795,389.

    Haka kuma alƙaluman sun nuna cewa maniyyata miliyan 1,435,017 sun je ƙasar ne ta hanyar jiragen sama, yayin da maniyyata 66,465 suka shiga ƙasar ta kan iyakokin doron ƙasa, sai kuma 5,094 da suka shiga ta tasoshin ruwan ƙasar.

    Alƙaluma

    Asalin hoton, Haramain

  11. Alhajin Najeriya ya rasu a filin Arfa

    Alhazai

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa yayin da Musulmai kusan miliyan biyu ke gudanar da aikin Hajji a ƙasar Saudiyya.

    Shugaban Hukumar aikin hajji ta Najeriya, Abdullahi Saleh Pakistan ne ya bayyana hakan lokacin da ya tattauna da manema labarai yau Alhamis a filin na Arafa.

    Saleh ya ce "mun samu labari akwai alhazanmu guda biyu waɗanda Allah ya yi musu rasuwa, ɗaya ma a nan filin Arfa Allah ya karɓi rayuwarsa, ɗaya kuma tun muna Makka."

    Sai dai shugaban na hukumar aikin hajji ta Najeriya ya ce rasuwar maniyyacin ba ya da alaƙa da tsananin zafi da ake fuskanta a ƙasar ta Saudiyya yayin aikin hajjin.

    Hawan Arfa na daga cikin ginshiƙan aikin Hajji, wanda shi kansa ɗaya ne daga cikin ginshiƙan imani ga mabiya addinin Musulunci.

    Rana ce da dukkanin mahajjata ke taruwa a kai da kuma kewayen dutsen Arfa domin yin addu'o'i na neman dacewa da kuma gafara, a wurin da Annabi Muhammad ya yi jawabi lokacin aikin hajjinsa na ƙarshe.

    Ma'aikatar aikin hajji da Umara ta Saudiyya ta shawarci maniyyata aikin Hajjin na bana da su guje wa yawan zirga-zirga ko fita daga tantunasu tsakanin ƙarfe 10 na safe zuwa 4 na yamma domin kauce wa zafin rana.

    Masana sun yi hasashen cewa yanayin zafi zai kai maki 45 a ma'auni a ranakun aikin Hajjin a garuruwan Makka da Mina.

  12. Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu rasuwa

    ..

    Asalin hoton, Facebook/Adejere Ibrahim

    Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara 86 rasuwa bayan doguwar jinya, a ranar Alhamis.

    Farfesa Jibril Aminu ya riƙe muƙamai da dama a Najeriya da suka haɗa da tsohon ministan Ilimi, tsohon ministan man fetur, jakadan Najeriya a Amurka.

    Marigayin ya wakilci jihar Adamawa a majalisar dattawa har karo biyu.

    Farfesa Umar Pate wanda makusancinsa ne ya bayyana marigayin da mutum mai basira da hazaƙa.

    "Farfesa Jibril Aminu mutum ne mai basira. Bai taɓa ɗaukar na biyu ba a jarrabawa. Duk abin da za ku yi da shi ko kwas ɗin gidanku ne to sai dai ka zo na biyu shi zai zo na ɗaya."

  13. Me ya sa Trump ya hana 'yan wasu ƙasashe shiga Amurka?

    Donald Trump

    Asalin hoton, EPA

    A yau Alhamis ne Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da hana bayar da biza ga mutanen da suka fito daga wasu ƙasashe 12 a duniya.

    Trump ya bayyana tsaron ƙasa a matsayin dalili yana mai cewa ya duba irin ƙwarewar da kowace ƙasa ke da ita a fannin bincike, da tsarin fitar da bayanai, da "ayyukan ta'addanci", da yawan masu ci gaba da zama bayan bizarsa ta ƙare, da kuma aniyarsu ta karɓar 'yan ƙasarsu da aka kora daga Amurka.

    Fadar White House ta ce takunkumin da aka saka musu "zai kare Amurka daga miyagu 'yan ƙasar waje", yayin da Trump ya jingina harin da aka kai a Colorado da matakin nasa.

  14. Matafiya hutun sallah sun maƙale a hanyar Abuja zuwa Kaduna

    Hanyar Abuja zuwa Kaduna

    Asalin hoton, Facebook/Muhammed Murtala Balogun

    Direbobi da fasinjoji sun maƙale tsawon sa’o’i kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sakamakon cunkoson ababen hawa yayin da ake shirin gudanar da bikin babbar sallah gobe.

    Lamarin ya fi ƙamari a daidai yankin Bishini.

    Dubban matafiya ne ke ta kokarin isa garuruwansu domin gudanar da bukukuwan Sallah tare da ‘yan uwa da abokan arziki.

    Hanyar Abuja zuwa Kaduna ɗaya ce cikin manyan hanyoyin da ke haɗa Babban Birnin Tarayya da jihohi da dama na arewacin Najeriya, ciki har da Kano da Neja.

    Hotunan da matafiya ke wallafawa a shafukan sada zumunta na nuna dogayen layukan motocin daga Jere zuwa Katari - wurin da ya dade yana fuskantar irin wannan matsala a lokutan bukukuwa.

    Zuwa yanzu hukumomi ba su komai ba game da musabbabin cunkoson ko matakan da ake ɗauka domin kawo ƙarshen matsalar.

    Hanyar Abuja zuwa Kaduna

    Asalin hoton, Facebook/Muhammed Murtala Balogun

  15. Ƙarin hotunan alhazan Najeriya a filin Arfa

    Milyoyin alhazai na ci gaba da gudanar da ayyukan ibada a filin Arfa a ranar Alhamis, inda wasu ke tururuwa zuwa dutsen na Jabal Rahma, wasu kuwa na gudanar da ibadun nasu ne a cikin tantunan da aka kafa a filin.

    Hukumomin Saudiyya dai sun yi gargaɗin fita daga tantina sakamkon tsananin zafin da ake fama da shi a ƙasar wanda ka iya kai wa digiri 47 zuwa 51.

    ..

    Asalin hoton, NAHCON

    Bayanan hoto, Shugaban hukumar alhazan Najeriya, Farfesa Abdullahi Saleh Usman na jawabi ga mahajjata
    ..

    Asalin hoton, NAHCON

    Bayanan hoto, Ahmad Mu'azu, ma'aikacin hukumar alhazan Najeriya lokacin da yake addu'o'i a cikin tanti a filin Arfa.
    ..

    Asalin hoton, NAHCON

    ..

    Asalin hoton, NAHCON

    ..

    Asalin hoton, NAHCON

    Bayanan hoto, Malam Kabiru na Kwango, fitaccen tauraro a masana'antar Kannywood yake addu'a a tantinsa da ke filin Arfa.
    ..

    Asalin hoton, NAHCON

    Bayanan hoto, Mahajjatan Najeriya a cikin tantinsu a filin Arfa
    ..

    Asalin hoton, NAHCON

    ..

    Asalin hoton, NAHCON

    ..

    Asalin hoton, NAHCON

  16. Gwamnatin Najeriya ta karɓi 'yan ƙasarta 147 da suka maƙale a Nijar

    'Yan Najeriya

    Asalin hoton, Nema

    Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso daga maƙwabciyarta Jamhuriyar Nijar, kamar yadda hukumar bayar da agaji ta ƙasa Nema ta bayyana.

    Mutanen da suka ƙunshi maza 129 da mata 17 da jariri ɗaya, sun sauka ne a filin jirgi na Murtala Muhammed da ke Legas jiya Laraba da misalin ƙarfe 5:20 na yamma.

    Nijar ce babbar hanyar da mazauna yammacin Afirka ke yin zango a yunƙurinsu na shiga ƙasashen Libya da Tunisia domin tsallakawa zuwa nahiyar Turai.

    Wannan dalilin kan jawo mutane da dama su maƙale a ƙasar ta yadda sai wasu ƙungiyoin ƙasashen duniya da gwamnatoci sun agaza musu domin komawa gida.

  17. Ma'aikatan kamfanin lantarki na Abuja na shirin fara yajin aiki

    Lantarki a Abuja

    Asalin hoton, TCN

    Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) sun yi barazanar tsunduma yajin aiki saboda abin da suka ce rashin biya musu buƙatunsu.

    Kamfanin na AEDC na samar wa Abuja babban birnin Najeriya wuta, da kuma jihohin Nasarawa da Kogi da Neja masu maƙwabtaka.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata wasiƙa da ƙungiyoyin ma'aikatan biyu suka aike wa mahukuntan kamfanin domin sanar da su aniyarsu, suna masu cewa "yajin aikin zai iya farawa a kowane lokaci".

    "Ku tuna cewa mun ƙulla yarjejeniya da ku a ranar 27 ga watan Satumban 2024 domin jingine yajin aiki game da rikicin kasuwanci da suka shafi ma'aikata," kamar yadda jaridar ta ambato wasiƙar na bayyanawa.

    "Muna tunasar da ku matsalar ƙin biyan fanshonmu da aka cire mana tsawon wata 16, da ƙin fara biyanmu sabon mafi ƙarancin albashi, da ƙin ƙara wa ma'aikata matsayi tsawon shekara 10, da ƙin tabbatar da ma'aikata na wucin gadi a matsayin cikakku."

  18. Sojin Isra'ila sun gano gawar Isra'ilawa biyu a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan ƙasar biyu da aka yi Garkuwa da su a Zirin Gaza.

    Wasu mayaƙa ne suka kashe Judi Weinstein Haggai mai shekara 70, wadda 'yar ƙasar Canada ce kuma, da mijinta Gadi Haggai mai shekara 72 lokacin da suka kai hari a Kibbutz Nir Oz da ke cikin Isra'ila a watan Oktoban 2023, in ji wata sanarwa.

    An gano gawarwakin nasu ne a kudancin Khan Younis da ke Gaza da tsakar dare kuma aka mayar da su Isra'ila domin gudanar da bincike.

    Har yanzu akwai mutum 56 da ake yin garkuwa da su a Gaza, cikinsu ana tunanin 20 na raye a hannun mayaƙan ƙungiyar Hamas.

  19. Yadda sunan 'Arafa' ya samo asali

    Hajji 2025

    Tsayuwar Arafa ɗaya ce daga cikin rukunnan aikin Hajji, ɗaya daga cikin ibadar Musulmi mafiya girma.

    Filin Arafat na da nisan kimanin kilomita 24 daga garin Makkah, kuma a nan ne mahajjata za su shafe wunin yau Alhamis.

    Sheikh Ibrahim Mansur malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, kuma ya ce akwai maganganun malamai uku dangane da asalin sunan ranar Arafa.

    Magana ta farko, an kira ta Arafa ne saboda a lokacin ne mutane daga sassa daban-daban ke sanin juna saboda haɗuwa a wuri guda. Sai ake kiranta Arfa, kamar yadda malamin ya yi bayani.

    Na biyu kuma, wasu malamai sun ce mala'ika Jibrilu ya ɗauki Annabi Ibrahim yana kewayawa da shi don nuna masa alamomi na aikin Hajji.

    To idan ya nuna abu sai ya tambaye shi, "Aarafta, Aarafta" da Larabci - wato ka gane?. Shi kuma Annabi Ibrahim sai ya ce "Araftu, Araftu" - na gane, na gane.

    ''Wannan dalilin ne ya sa aka saka mata Arafa'', in ji malamin.

    Magana ta uku, lokacin da Allah ya sauko da Annabi Adam da Nana Hawwa'u zuwa duniya sun daɗe ba su haɗu ba. Amma da Allah Ya tashi haɗa su sai ya haɗa su a ranar Arafa.

    ''Wannan haɗuwa da suka yi suka gane juna, sai ya sa ake kiran ta Ranar Arafa'', kamar yadda ya yi bayani.

  20. Dalilin da ya sa Saudiyya ta tsaurara hukunci kan masu yin Hajji ta ɓarauniyar hanya

    Hajji

    Asalin hoton, Saudi Authorities

    Dokokin da hukumomin Saudiyya suka saka a bana sun yi tsaurin da ba a taɓa ganin kamar su ba.

    Daga cikin hukuncin da aka tanada akwai tarar riyal 20,000 ga duk ɗan Saudiyyar da aka kama da yunƙurin yin Hajji ba tare da izini ba.

    Waɗanda ba 'yan ƙasa ba kuma za a tasa ƙeyarsa zuwa ƙasarsu sannan a haramta masa shiga Saudiyya tsawon shekara 10 bayan kammala zaman gidan yari.

    Zuwa ranar Lahadi, hukumomi sun ce sun hana mutane fiye da 269,000 shiga birnin na Makkah, wanda shi ne mafi tsarki a addinin Musulunci.

    Ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka jawo tsauraran matakan akwai binciken da ya gano cewa kashi 80 cikin 100 na alhazan da suka mutu a bara ba su da izinin yin aikin.

    Hakan na nufin ba su samu damar amfana da kayayyakin rage tsananin zafi ba kamar tantuna masu na'urorin sanyaya ɗaki, da ababen hawa, inda zafin ya kai 51C a ma'auni.