Wata kotu a ƙasar Chadi ta yanke wa tsohon Firaministan ƙasar kuma jagoran ƴan adawa Succès Masra hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari, kan kalaman ɓatanci, da na kiyayya da kuma ingiza kisan kiyashi.
Hukuncin na zuwa ne bayan zarginsa da hannu a rikice-rikice da suka janyo mutuwar mutum 42, yawanci mata da ƙananan yara a yankin Mandakao, da ke kudu maso yammacin ƙasar a watan Mayu.
Lauyoyin Masra sun soki hukuncin, inda suka kira hakan da rashin adalci tare da cewa babu gamsassun hujjoji da suka nuna yana da laifi.
Sun kuma kwatanta hukuncin da cewa "ya yi tsauri ga mutumin da bai aikata komai ba."
Jim kaɗan bayan yanke hukuncin, kafofin yaɗa labarai sun ruwaito Masra na faɗa wa magoya bayansa cewa, "Kada ku karaya, ku jajirce tare da tsare gida."
An kama Masra ne wanda ya kasance mai yawan sukar shugaba Idriss Déby Itno a watan Mayu, inda ya shiga yajin cin abinci a watan Yuni don adawa da tsare shi da aka yi.
Ya tsere daga Chadi a shekarar 2022 - sai dai ya koma ƙasar a bara karkashin wani shirin afuwa da aka amince da shi.