Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Kayyade miliyan 8.5 kafin- alƙalami na kuɗin aikin Hajjin baɗi da sace mutum 150 a Zamfara
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.
Da dama daga cikin ma'aikatan gwamnatin Najeriya ba su da tarbiyya - Sanusi II
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya zargi da dama daga cikin ma'aikatan gwamnatin Najeriya da aikata cin hanci da rashawa saboda "rashin tarbiyya tun daga tasowarsu".
Da aka tambayi sarkin ta cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels TV a yammacin ranar Laraba dangane da cin hanci da rashawa, Sanusi ya ce da yawa ba a koya musu yin gaskiya da riƙon amana ba.
"Da dama daga cikin mutanen da ke riƙe da ofisoshin gwamnati ba su da wannan tarbiyyar, mafi yawa na shiga gwamnati ne bisa dalilai marasa kyau," in ji shi.
"Ina ganin an rusa kusan baki ɗayan ɗabi'un kirki na ƙasar nan. Marasa tarbiyya ne suke mulkar mu, waɗanda ba su da wani abin alfahari kuma ba su da niyyar barin wani abin alfahari a bayansu.
"Mutane ne da ke alfahari kawai da yawan dukiyarsu, da yawan gidaje, da yawan jiragen da suka mallaka. Ba su taɓa tunanin cewa mutane na yi musu kallon ɓarayi ne.
An kayyade naira miliyan 8.5 kafin alkalami na kuɗin aikin Hajjin 2026
Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, ta bayyana cewa an kayyade naira miliyan 8.5 a matsayin kafin alkalami na kuɗin aikin Hajjin 2026.
NAHCON ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, bayan gudanar da taro da shugabanni da kuma sakatarorin hukumomin aikin hajji na jihohin ƙasar - don fara fara shirye-shiryen ibadar ta wannan shekarar ta Musulunci.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce an kayyade miliyan 8.5 ɗin ne a matsayin kafin alkalami na aikin hajjin baɗi, kafin a kammala tattaunawa don sanin haƙikanin kuɗin.
Ya ce Saudiyya ta sake bai wa Najeriya gurbin kujeru 95,000, kamar yanda ta samu a bara.
Ƴanbindiga sun sace mutum 150 cikin kwana huɗu a Zamfara
Rahotonnin daga jihar Zamfara a yankin arewa maso yammcin Najeriya na cewa ƴanbindiga sun sace mutum 150 a jerin hare-haren da suka kai wasu garuruwan jihar cikin kwanaki huɗu da suka gabata.
Kakakin gwamnatin jihar Zamfara, Mahmud Mohammed Dantawasa ya tabbatar wa da BBC kai hare-haren, kodayake bai yarda ko musanta adadin ba, sai dai ya ce gwamnati na ƙoƙarin kuɓutar da mutanen.
Mazauna garuruwan sun ce ƴanbindigar ɗauke da muggan makamai sun kai jerin hare-hare cikin kwana huɗu a ƙauyukan Sabon Garin Damri da Dakko Butsa (da ke iyaka da Sokoto), da Tungar Abdu Dogo da Tungar Sarkin Daji da Sadeda kuma Tungar Labi.
Ƴanbindigar na bin dare ko lokacin ruwan sama domin auka wa ƙauyukan a lokacin da mutane ke tsaka da barci.
Bayanai sun ce rashin kyawun titunan jihar na taimaka wa ƴanbindigar, inda jami'an tsaro ke fuskantar ƙalubale wajen zuwa wuraren da ƴanbindigar ke cin karensu babu babbaka a kan lokaci.
'Peter Obi ba zai iya cin arewa a 2027 ba saboda kafuwar Tinubu a yankin'
Ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Festus Keyamo ya ce ɗaya daga cikin jagororin sabuwar haɗakar ADC, Peter Obi ba zai iya cin yankin arewacin Najeriya a zaɓen 2027, sakamakon yadda Shugaba Tinubu ya kafu a yankin.
Yayin wata hira da gidan talbijin na Channels, Keyamo ya ce Shugaba Tinubu da jam'iyyarsa ta APC, sun samu kafuwa da tsari a yankin arewacin Najeriya.
Ministan jiragen saman ya kuma ce da wahala haɗakar ADC ta iya yin wani tasiri a fagen siyasar ƙasar.
''Babu inda za su je, indai don batun samun magoya baya ne'', in ji Keyamo.
"Wannan haɗakar da suke kira ADC, abin da take yi shi ne ƙoƙarin haɗa Atiku da Obi a 2027, domin zartar adadin ƙuri'a miliyan takwas da muka samu a 2023'', in ji shi.
"Idan ka tsayar da Obi takara, a yanzu ba zai iya cin arewa ba, saboda yadda muka kafu. Muna da gwamnoni da jagoranci mai ƙarfi a yankin'', in ji ministan.
Jihohin Najeriya 31 na fuskantar barazanar ambaliya
Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan sama a wasu sassan Najeriya, hukumar kula da madatsun ruwa da kuguna ta ƙasar, NiHSA ta yi gargaɗin samun mummunar ambaliya a ƙananan hukumomin 198 cikin jihohi 31 tsakanin 7 zuwa 21 ga watan Agustan da muke ciki.
Cikin wata sanar wa hukumar ta fitar, ta ce fiye da garuruwa 832 ne ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar.
Hukumar ta kuma yi gargaɗin lalacewar tituna fiye da 100, yayin da ake fargabar ambaliyar za ta tilasta wa mutane barin gidajensu.
Gargaɗin na zuwa ne bayan da farkon makon nan hukumar ta yi gargaɗin samun ambaliyar a jihohin ƙasar 19.
Tuni dai wasu jihohin suka fara fuskantar ambaliyar.
'Aƙalla mutum 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya'
Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla 'yan Najeriya 24,000 ne suka ɓata tun daga shekarar 2014 waɗanda galibinsu yara ne ƙanana, sanadiyyar rikicin Boko Haram.
Kakakin ƙungiyar Aliyu Dawobe ya shaida wa BBC cewa jihohin Borno da Yobe da Adamawa ne kan kan gaba inda suke da adadiu 16,000.
Aliyu Dawobe ya ce ƙungiyarsu ta samu ƙorafe-ƙorafe daga mutane daban-daban da ƴan'uwansu suka ɓata, kuma tana bakin ƙokarinta wajen taimaka musu domin gano yaran.
ICRC ta ce ko a wannan shekarar kaɗai ta gano mutum 11 ƙari kan mutane 13 da aka gano.
Kakakin ƙungiyar ya ce wasu daga cikin ririn waɗannan mutane sun watsu ne cikin duniya, yayin da wasunsu ke tsare a hannun hukumomi, wasu kuma sun sake garuruwa.
Gwamnatin Kano za ta mayar da gidan yarin Kurmawa gidan tarihi
Gwamnatin jihar Kano ta ɓullo da shirin mayar da gidan yarin Kurmawa - da ya kwashe shekara fiye da 100 - gidan tarihi domin adana abubuwan da suka faru lokacin mulkin mallaka.
Gidan yarin mai shekara 115, an gina shi ne lokacin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar sarkin Kano domin a riƙa ɗaure masu laifi a ciki.
A bisa ƙa'idar da aka gina gidan yarin Kurmawa zai ɗauki fursunoni 690 ne kawai.
Mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin yaɗa labara, Ibrahim Adam ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.
Ibrahim Adam ya ce za a mayar da fursunonin da ke ɗaure a gidan yarin zuwa sabon gidan fursunan Janguza na zamani, da ke kusa da barikin soji a kan babban titin Kano zuwa Gwarzo.
Mashawarcin gwamnan Kano ya ce za a mayar da Kurmawa gidan tarihi ne domin taskance abubuwan tarihin da suka faru a zamanin mulkin mallaka.