Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/08/2025

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage da Isiyaku Muhammed

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muka rufe wannan shafin na labaran kai-tsaye na wannan rana ta Lahadi.

    Sai kuma gobe Litinin idan Allah ya nuna mana. Da fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. "Trump na so a yi gaggawar samun maslaha a Zirin Gaza"

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya ce gwamnatin Amurka a ƙarƙashim Donald Trump na so a yi gaggawar kawo ƙarshen tashin-tashinan da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

    Ya ce gwamnatinsu na yin duk mai yiwuwa domin hana Hamas "kashe mutanen da babu ruwansu," da tabbatar da an sako Isra'ilawa da ke hannun Hamas da magance matsalolin da mutanen Zirin Gaza ke fuskanta na matsalolin rayuwa da buƙatar kayan agaji.

    "Shugaban Amurka ya sha nanata cewa shi shugaba ne mai son zaman lafiya," in ji Vance a zantawarsa da Fox News, sannan ya ƙara da cewa Trump na ƙoƙarin tabbatar da waɗannan buƙatun a tare.

    "Yana ƙoƙarin ganin a yi gaggawar samar da maslaha ta hanyar diflomasiyya. Waɗanda Hamas ke garkuwa da su, su koma ga iyalansu, su kuma mutanen Gaza su samu wadataccen kayan agaji."

  3. 'An kama masu yunƙurin juyin mulki a Mali'

    Mali

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga sojojin da ke mulki a Mali sun ce an kama sojoji tsakanin ashirin zuwa talatin bisa zargin hannu a shirin kifar da gwamnati.

    Wasu majiyoyin tsaro sun ce waɗanda aka kama sun haɗa da Janar Abass Dembele, tsohon gwamnan yankin Mopti a tsakiyar ƙasar.

    Wakilin BBC ya ce zuwa yanzu gwamnatin ba ta ce komai ba a hukumance, wadda ita kanta ta ƙwace mulki a 2021.

    Zarge-zargen yunƙurin kifar da gwamnati na nuna ƙaruwar zaman ɗar-ɗar a tsakanin gwamnatin sojin inda rahotanni ke cewa matsalar masu iƙirarin Jihadi na ƙara faɗaɗa a arewacin ƙasar.

  4. Iran ta yi Allah-wadai da yunƙurin Isra'ila na ƙwace Gaza

    IRAN

    Asalin hoton, EPA

    Ministan harkokin wajen Iran, Seyed Abbas Araghchi ya ce ƙasarsa na Allah-wadai da duk "yunƙurin fatattakar mutanen Gaza ko yunƙurin mamaye yankin."

    Araghchi ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a game da shirin Isra'ila na mamaye Gaza.

    Ministan ya bayyana a wata sanarwa tun a farko cewa, "duk wani yunƙurin fatattakar mutane," na cikin tsare-tsare "ƙarar da Falasɗinawa da ƙasarsu, kuma hakan ya saɓa dokokin duniya."

    Haka kuma sanarwar ta buƙaci ƙasashen duniya su tursasa Isra'ila ta daina "cin zalin da take yi."

    Iran da Isra'ila sun shiga yarjejeniyar tsagaita wuta ne a yaƙin da suke gwabza a watan Yuni, amma kowane ɓangaren na gargaɗin yaƙin na iya komawa ɗanye.

  5. 'Har yanzu Peter Obi ɗan Jam'iyyar Labour ne'

    Peter Obi

    Asalin hoton, Peter Obi

    Shugaban ƙungiyar Obidient Movement, Dr. Tanko Yunusa ya ce tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar Labour, Peter Obi na nan a cikin jam'iyyar har yanzu.

    Yunusa ya bayyana haka ne a wajen taron ƙungiyar da aka yi a jihar Oyo, wanda aka tara ƴan siyasa da masana da ƙungiyoyin siyasa a jihar domin tattaunawa game da siyasar ƙasar.

    Jaridar Daily Trust ce ta ruwaito shugaban ƙungiyar yana bayyana hakan, inda ya ce, "domin warware shubuha da ake ciki, har yanzu Peter Obi ɗan Jam'iyyar Labour ne. Kun dai san akwai wasu matsaloli a jam'iyyar waɗanda ake jiran INEC ta kawo maslaha a game da su."

    Ya ƙara da cewa idan aka zaɓi Obi a matsayin shugaban Najeriya, "wa'aɗi ɗaya zai yi, kuma a wannan wa'adin ɗayan ne zai kawo canjin da ake buƙata. Yawancin matsalolin da muke fuskanta za a iya magance su a shekara ɗaya idan aka yi abun da ya dace. Kuma zai iya domin ya yi an gani a lokacin da yake gwamnan jihar Anambra."

  6. Ba za mu bar Gaza ba sai dai mu mutu - Fatma

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Wata mai mai ƴaƴa tara ta ce duk runtsi duk wahala ba za ta bar Gaza ba duk kuwa da yunƙurin da Isra'ila ke yi na faɗaɗa yaƙin da take yi a zirin.

    Fatma Al-Shinbary mai shekara 41 ta shaida wa Reuters cewa za ta tsaya a zirin domin ta cigaba da rayuwa, sannan ta ƙara da cewa, "mafi yawan mutanen zirin ma ba za su fice ba."

    Mijin Fatima yana kwance ne yana jinya, ita ce take ɗawainiya da gidan ta hanyar saa'anta burodi tana sayarwa a sansanin ƴan gudun hijira da suke zama.

    Ta ce ta sha barin inda take zama a shekaru baya da suka gabata, inda ta ce, "na gaji da tsalle-tsalle."

    "Gara mutuwa a gare mu," in ji ta, sannan ta ƙara da cewa, "a duk inda muka je, idan za mu canja waje, mukan tafi ne mu bar kayayyakinmu, a haka muke ta asarar kayayyakinmu."

  7. Mace-mace da ake samu a wurin rabon agaji a Gaza laifin Hamas ne - Netanyahu

    Netanyahu

    Asalin hoton, EPA

    Firaministan Isra'illa, Benjamin Netanyahu ya ce mace-mace da ake samu a wurin rabon kayan agaji a Gaza laifin ƙungiyar Hamas ne.

    Netanyahu ya ce Hamas na sace kayan agaji ne da gangan, wanda a cewarsa yake jawo ƙarancin kayayyakin na agaji a zirin.

    Ya nanata cewa Isra'ila ba ta da hannu a matsananciyar yunwar da ake ciki a Gaza- amma ya tabbatar da cewa lallai mutanen zirin na buƙatar abinci.

    Da ake tambaye shi game da Falasɗinawa da aka kashe a cibiyar GHF, ya ce, "ƴan Hamas ma sun yi harbe-harbe da dama a wajen."

    Hamas dai ta daɗe tana musanta zargin da ake mata na sace kayan agajin da ake aika wa fararen hula a Gaza, sannan wani bincike da gwamnatin Amurka ta yi, wanda kafofin Reuters da CNN suka ruwaito ya nuna cewa babu shaidar sace kayan agaji a Gaza.

  8. Ƙungiyar KACRAN ta wayar da kan Fulani makiyaya muhimmancin rajistar zaɓe

    KACRAN

    Asalin hoton, KACRAN

    Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Kulen Allah Cattle Rearers Association of Nigeria (KACRAN) ta ƙaddamar da shirin wayar da kan Fulani makiyaya muhimmancin rajistar zaɓe, shirin da ta ce zai bi Fulani gida-gida domin jawo hankalinsu su je su yi rajistar ta zaɓe domin a dama da su a harkokin siyasar 2027.

    An ƙaddamar da fara da shirin ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Agustan 2025 a ƙaramar hukumar Jakusko ta jihar Yobe domin taimakawa ha Hukumar INEC ta cimma nasarar aikin da ta fara na cigaba da rajistar zaɓe a Najeriya.

    A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Khalil Muhammad Bello ya fitar, ya ce za a yi shekara ana wayar da kan makiyaya muhimmancin yin rajistar zaɓe da ma kaɗa ƙuri'a da sauran su.

    "KACRAN ta fahimci muhimmancin kaɗa ƙuri'a, shi ya sa ta ƙuduri aniyar ganin ba a bar makiyaya a baya ba duk da kuwa da wahalar da suke fuskanta."

    Ya ce babban burinsu shi ne, "wayar da kan makiyaya domin su shiga a dama da su siyasa - ko dai su yi zaɓe, ko su tsaya takara. Da kuma taimakon makiyaya waɗanda suka ɓatar da katin zaɓensu hanyoyin da za su sabunta katin ko kuma gyara katin domin daidaita bayanai."

  9. Ko ɗabi'ar neman burgewa ce ke hana mata cigaba a wuraren aiki?

    Mata

    Asalin hoton, 10,000 hours/Getty Images

    Faith mai shekara 24 na cikin zauren tattaunawa a ofishinta da ke birnin Nairobi a ƙasar Kenya, amma cikin fargaba. An fara ganawa lafiya ƙalau, har ma tana ta dariya saboda barkwancin da iyayen gidanta ke yi, kwatsam kuma sai abubuwa suka sauya.

    Wani abokin aiki da ya fi ta matsayi ya ce Faith na jin cewa kamar ba za ta iya aiki tuƙuru ba. Amma kafin ta mayar da martani sai wani ya ambaci sunanta.

    "Kuma Faith ta amince da maganata!" Sauran mambobu suka juya suna kallon Faith yayin da abokin nata ke ci gaba da cewa "ai kin yarda ko Faith?"

    Faith ba ta amince ba, amma kuma yanzu tana cikin matsi.

    Latsa nan don karanta cikakken labarin...

  10. Ba mu da zaɓi illa karasa aikin da muka fara a Gaza - Netanyahu

    Netanyahu

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Isra'ila ba ta "zaɓi" illa "karasa aikin" da ta fara wajen ƙarya lagon Hamas.

    Ya bayyana haka ne a taron manema labarai da yake gudanarwa, inda ya ce kashi 70-75 na Gaza na karkashin ikon sojojin Isra'ila.

    Sai dai ya ce har yanzu Hamas na riƙe da wasu yankuna biyu. Na farko shi ne birnin Gaza da kuma wani sansani da ke tsakiyar zirin Gaza.

    A ranar Juma'a, majalisar tsaron Isra'ila ta bai wa dakarun tsaron ƙasar damar "ta warzaga" wuraren biyu.

    Ya ce wannan ita ce "hanyar da ta dace" na kawo karshen yaƙin.

    Ya ƙara da cewa Isra'ila za ta bar fararen hula su tafi wurare masu kariya - inda za su samu abinci da tsaro da kuma agajin lafiya.

  11. Kotu ta ɗaure tsohon Firaministan Chadi shekara 20 a gidan yari

    Succès Masra

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Succès Masra ya kasance mai yawan sukar shugaba Idriss Déby Itno

    Wata kotu a ƙasar Chadi ta yanke wa tsohon Firaministan ƙasar kuma jagoran ƴan adawa Succès Masra hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari, kan kalaman ɓatanci, da na kiyayya da kuma ingiza kisan kiyashi.

    Hukuncin na zuwa ne bayan zarginsa da hannu a rikice-rikice da suka janyo mutuwar mutum 42, yawanci mata da ƙananan yara a yankin Mandakao, da ke kudu maso yammacin ƙasar a watan Mayu.

    Lauyoyin Masra sun soki hukuncin, inda suka kira hakan da rashin adalci tare da cewa babu gamsassun hujjoji da suka nuna yana da laifi.

    Sun kuma kwatanta hukuncin da cewa "ya yi tsauri ga mutumin da bai aikata komai ba."

    Jim kaɗan bayan yanke hukuncin, kafofin yaɗa labarai sun ruwaito Masra na faɗa wa magoya bayansa cewa, "Kada ku karaya, ku jajirce tare da tsare gida."

    An kama Masra ne wanda ya kasance mai yawan sukar shugaba Idriss Déby Itno a watan Mayu, inda ya shiga yajin cin abinci a watan Yuni don adawa da tsare shi da aka yi.

    Ya tsere daga Chadi a shekarar 2022 - sai dai ya koma ƙasar a bara karkashin wani shirin afuwa da aka amince da shi.

  12. Gwamnonin arewa na alhinin mutuwar tsohon ministan noma

    Audu Ogbeh

    Asalin hoton, Pius Utomi Ekpei/AFP via Getty Images

    Shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana kaɗuwarsa kan mutuwar dattijo tsohon ministan noma, Audu Ogbeh - wanda ya rasu ranar Asabar 9 ga Agustan 2025, yana da shekara 78.

    "A madadina da sauran gwamnonin arewa muna miƙa ta'aziyya kan rasuwar wannan dattijo, mai faɗa a ji wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen cigaban ƙasa," in ji Inuwa Yahaya a cikin wata sanarwa.

    Ya ce Ogbeh jagora ne na gari kuma ƙwararren ɗan siyasa wanda za a ci gaba da tunawa da irin rawar da ya taka wajen cigaban dimokraɗiyya a Nijeriya.

    "Ya kawo mutunci da sanin ya kamata a kowane mukami da ya riƙe, ya kuma bautawa ƙasarsa da nagarta.

    Shugaban gwamnonin arewar ya ce mutuwarsa ba rashi ne ga jihar Benue kaɗai ba, har ma da Najeriya baki ɗaya.

  13. NDLEA ta kama wani fasto kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi

    NDLEA

    Asalin hoton, NDLEA

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta ce ta kama wani babban faston majami'ar The Turn of Mercy Church, Adefolusho Olasele, kan zarginsa da hannu a safarar miyagun ƙwayoyi daga Ghana zuwa Najeriya.

    An kama Olasele ne wanda ya shafe tsawon watanni yana tserewa hukumomi a ranar Lahadi, 3 ga Agustan 2025 - a cocinsa da ke Okun Ajah, a jihar Legas.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi ya fitar, ya ce jami'an hukumar sun jira sai da faston ya gama wa'azinsa kafin daga bisani suka cafke shi lokacin da yake barin harabar cocin.

    A cewar Babafemi, faston ya tsere zuwa Ghana a watan Yuni, bayan da jami'ai suka alaƙanta shi da wasu ganyen wiwi da aka kama mai nauyin kilogiram 200 a bakin ruwa na Okun Ajah ranar 4 ga watan Yuni da kuma wanda aka samu a cikin motarsa.

    Babfemi ya ce malamin majami'ar ya amsa cewa yana safarar ƙwayoyi ta ruwa daga Ghana zuwa cikin Najeriya.

  14. Birtaniya za ta fara tisa ƙeyar bakin da suka aikata laifi zuwa gida

    Migrants

    Asalin hoton, Home Office

    Birtaniya ta fitar da sabon tsarin tisa keyar duk wani bako da aka samu da aikata laifi a ƙasar zuwa ƙasarsa ta asali.

    Ministar shari'ar ƙasar, Shabana Mahmood, ta ce shirin tisa ƙeyar mutum gida zai rage asarar kuɗaɗen masu biyan haraji da dala dubu 70 da ake kashewa kowanne fursuna guda a shekara.

    Kafin wannan lokaci duk wani bako da ke zama a Birtaniya da aka samu da laifi, a gidan yarin ƙasar ake ɗaure shi.

    Sai dai waɗanda hukuncinsu ɗaurin rai da rai ne, da waɗanda suka aikata kisa ko ta'addanci - za su cigaba da kasancewa a ɗaure a Birtaniya bisa sabon tsarin.

    Kashi 12 cikin 100 na fursunonin Birtaniya baki ne, kuma gwamnati na fuskantar matsin lambar rage cunkoso a gidajen yarin ƙasar.

  15. Salah ya soki UEFA kan yadda ta yi alhinin mutuwar ɗan wasan Falasɗinawa al-Obeid

    Salah

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ya soki hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, kan wallafa sakon alhinin mutuwar ɗan wasan Falasɗinawa da ya rasu ba tare da ba da cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarsa ba.

    A ranar Alhamis aka kashe Suleiman al-Obeid, wanda aka fi sani da Pelen Falasɗinawa - a hare-haren Isra'ila lokacin da yake jiran karɓan kayan tallafi a kudancin Gaza.

    "Ko za ku faɗa mana ta yaya ya mutu sannan a ina," kamar yadda Salah ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar.

    Obeid wanda ɗan wasan gaba ne, ya zura kwallaye sama da 100 a tsawon rayuwarsa ta tamaula.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Ana zanga-zanga a Isra’ila kan shirin Netanyahu na mamaye Gaza

    Isra'ila

    Asalin hoton, EPA

    Dubban mutane sun fito kan tituna a faɗin Isra'ila, don adawa da matakin gwamnatin ƙasar na faɗaɗa farmakin sojin da take a Gaza.

    A ranar Juma'a ne majalisar tsaron Isra'ila ta amince da sharuɗa biyar na kawo karshen yaƙin, ciki har da shirin karɓe iko da Birnin Gaza, inda sojojin Isra'ilar suka ce za su "shirya karɓe iko" da birnin Gaza.

    Masu zanga-zangar da suka haɗa da iyalan mutum 50 ɗin da ake garkuwa da su a Gaza - ciki har da 20 ɗin da ake kyautata zaton suna raye, suna fargabar cewa shirin zai saka rayuwar ƴan uwansu cikin haɗari, inda suka buƙaci gwamnatin Isra'ila da ta yi ƙoƙarin don ganin an sake su.

    Shugabannin Isra'ila sun yi watsi da sukar da ake yi wa shirinsu, inda Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce "hakan zai taimaka a saki mutanen mu".

    Wata ƙungiya da ke wakiltar iyalan waɗanda ake garkuwa da su ta wallafa a shafin X cewa: "Faɗaɗa farmakin zai saka mutanen mu da kuma sojoji cikin barazana - al'ummar Isra'ila ba su da niyyar saka su cikin haɗari".

  17. Mahara sun kashe mutum biyu, sun ƙona gidaje da dama a Filato

    Filato

    Asalin hoton, ADO MUSA

    Wasu da ake zargin mahara sun afka wa karamar hukumar Bokkos na jihar Filato, inda suka hallaka mutum biyu tare da ƙona gidaje da kuma coci-coci.

    An kai harin ne da tsakar dare ɗauke da manyan makamai waɗanda suka zarta na ƙungiyar ƴan sintiri da ke yankin.

    Shugaban ƙungiyar ci gaban al'ummar Bokkos, Farmasun Fudang ya bayyana mutane biyun da aka kashe ma'ikata ne a wani coci, inda ya ce an kuma ƙona gidaje da dama da kuma coci-coci, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

    Fudang ya ce maharan sun kuma lalata gonaki sannan suka yi awon gaba da shanu da tumakai da awakai da agwagi har ma da abincin da aka adana.

    "Sun zo ne ta hanyar Ding'ak da Kopmur duk da cewa akwai shingen binciken jami'an tsaro a wajen. Sojoji sun yi harbi a iska sai dai ba su fafata da maharan ba," kamar yadda Fudang ya yi zargi.

    Shugaban al'ummar ta Bokkos ya ce harin na zuwa ne kwanaki biyu da kai irin makamancinsa a al'ummar Ndimar - Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma ta jihar da su kai musu ɗaukin gaggawa tare da ganin an hukunta waɗanda ke far musu.

  18. Ƙawayen Ukraine sun ce dole ne a sa ƙasar a tattaunawar zaman lafiya

    Ukraine

    Asalin hoton, EPA

    Ƙasashen Turai da ke goyon-bayan Ukraine sun buƙaci a matsa wa Rasha lamba, gabanin ganawar da shugaba Donald Trump da Vladimir Putin za su yi.

    A wata sanarwar haɗin-gwiwa, Birtaniya da sauran ƙasashe sun jadadda manufar cigaba da kare 'yancin Ukraine.

    Sannan sun ce dole a sa Ukraine a duk wani batu da ya shafi yanke hukunci kan makomarta da zaman lafiya, da kuma alkawarta cigaba da ba ta taimakon soji da kuɗaɗe.

    "Sulhu na dindindin muke so, ba wai tsagaita wuta kaɗai ba, sannan ba za mu aminta da sadaukar da wasu yankunan mu ga Rasha ba saboda zaman lafiya," in ji shugaba Zelensky.

  19. 'Ƙarin mutum 11 sun mutu sakamakon yunwa a Gaza'

    Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Rahotanni sun bayyana cewa ƙarin mutum 11 sun mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki a Gaza, a cewar ma'aikatar lafiya a yankin.

    Wannan ya kawo alkaluman waɗanda suka mutu sakamakon rashin abinci a Gaza zuwa 212, ciki har da yara 98.

    Hare-haren Isra'ila sun hallaka aƙalla mutum 38 da jikkata 491 a cikin sa'o'i 24 da suka wuce.

    Alkaluman waɗanda ke mutuwa na ta ƙaruwa a daidai lokacin ake ruwaito cewa Isra'ila ta bai wa mazauna Gaza wa'adi zuwa 10 ga Oktoban 2025 da su fice daga yankin, bayan wani shiri da ƙasar ke yi na mamaye zirin Gaza - lamarin ya janyo Alla-wadai da kuma ce-ce-ku-ce daga faɗin duniya.

    Sabon tsarin, wanda majalisar ministocin Isra'ila suka amince da shi ranar Juma'a, ya bayar da jerin sharuɗa biyar da za su kawo karshen yaƙin Gaza, inda ɗaya daga ciki ya kasance "karɓe iko da tsaron yankin".

  20. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Lahadi.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ahmad Bawage ne zai kasance da ku a wannan lokaci.