'Kano na sa ran samun jarin naira tiriliyan biyar a shekara biyar'

Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon
'Kano na sa ran samun jarin naira tiriliyan biyar a shekara biyar'

Gwamnatin jihar Kano ta ce tana sa ran samun masu zuba jari da ya kai ƙimanin naira tiriliyan biyar nan da shekara biyar masu zuwa, bayan kaddamar da kundin harkokin zuba jari na jihar, kamar yadda babban darektan hukumar bunƙasa zuba jari na jihar, Muhammad Nazir Halliru ya shaida wa BBC.

Ya ce nan gaba kaɗan jihar za ta yi gagarumin taro don kaddamar da kundin wanda zai zama jagora ga masu sha'awar zuba jari a fannoni daba-daban, ciki har da noma, ababen more rayuwa, kyere-kyere da kuma ilimi a faɗin jihar.

Halliru ya kuma ce sun samu wani kamfani da zai zo ya gina babban kamfani na samar da iskar gas ta CNG, wanda ya ce zai samar wa mutane aikin yi da kuma rage irin wahalhalu da ake sha wajen amfani da fetur da man gas na dizil.