Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 11/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 11/11/2025

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Annur Muhammad

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa nan muka kawo ƙarshen wannan shafi namu na yau.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu

  2. Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci NNPCL ya mayar da naira tiriliyan 210 cikin asusun gwamnati

    Kamfanin NNPCL

    Asalin hoton, NNPCL/X

    Majalisar Dattawan Najeriya ta yi fatali da bahasin babban kamafnin mai na ƙasa NNPCL game da naira tiriliyan 210 da ake alaƙanta kamfanin da ɓacewarsu.

    Kwamitin majalisar dattawan kan asusun gwamnati ƙarƙashin jagorancin Sanata Aliyu Wadada da ya ɗauki watanni yana bincikar batun ya ɗauki matakin ne ranar Talata bayan da shugaban kamfanin, Bayo Ojulari ya kasa bayyana a gaban kwamitin, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

    An kira zaman ne domin bai wa NNPCL damar bayar da bahasi kan tambayoyi 19 da kwamitin ya gabatar wa kamfanin kan ɓacewar naira tiriliyan 210.

    A watannin da suka gabata ne kwamitin ya gano wasu kuira-kurai a yadda kamfanin ya tafiyar da ayyukansa tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023, inda kwamitin ya gano wasu kuɗaɗen ba a ga inda suka shiga ba da suka kai naira tiriliyan 107 da naira tiriliyan 103.

    Lamarin dai ya haifar da ayoyin tambaya game da yadda kamfanin ya riƙa kashe kuɗaɗe.

  3. Erdogan ya jajanta wa iyalan sojojin ƙasar da suka mutu a hatsarin jirgi

    Erdogan

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban ƙasar Turkiyya ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka mutu a lokacin da wani jirgin sojin ƙasar ya faɗi a kan iyakar ƙasashen Georgia da Azerbaijan.

    Ma'aikatar tsaron Turkiyya ta ce jirgin na ɗauke da aƙalla mutum 20 a lokacin da ya faɗi jim kaɗan bayan ya tashi daga Azerbaijan a yau Talata.

    Kawo yanzu ba a san haƙiƙanin adadin waɗanda suka mutu a hatsarin ba.

    Haka ma babu bayanai kan abin da ya haifar da hatsarin jirgin.

  4. Gasar Kofin Duniya mai zuwa ce ta ƙarshe a gare ni - Ronaldo

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafar nan na duniya, Cristiano Ronaldo, ya ce Gasar Kofin Duniya da za a yi a shekara mai zuwa zai kasance na ƙarshe a gareshi.

    Ƙasarsa ta Portugal na gab da samun gurbi a gasar da Amurka da Canada da Mexico za su ɗauki baƙunci.

    Ronaldo, mai shekara 40 ya kasance yana buga gasannin Kofin Duniya tun 2006.

    Ɗan wasan - wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or, ta ɗan wasan ƙwallon ƙafa mafi ƙwazo har sau biyar - a shekarun baya-bayan nan ya riƙa fuskantar tambayoyi kan yaushe zai yi ritaya.

  5. 'Safarar mai ba bisa ƙa'ida ba na haifar wa Najeriya asarar maƙudan kuɗi'

    Wasu masana tattalin arziki a Najeriya sun tabbatar da cewa fataucin ɗanyen man fetur ba bisa ƙa'ida ba, na daga cikin manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a yanzu.

    Masanan sun ce Najeriya na asarar kimanin dala diliyan $15 na kuɗin shiga ga ƙasar a kowace shekara.

    Wannan ɓarna na faruwa ne ta hanyar da ɓarayi ke amfani da na’urori na zamani don haƙo da tallata haramtaccen man ga ƙasashen Duniya.

    Duk da matakai daban-daban da gwamnati ke ɗauka, girman matsalar na ci gaba da haifar da giɓi mai girma a cikin kuɗaɗen shiga ga gwamnatin ƙasar.

  6. UNICEF ya zargi Isra'ila da hana shigar da sirinji don riga-kafin ƙananan yara a Gaza

    Asusun tallafa wa ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya ce Isra'ila ta hana shigar da fiye da sirinji miliyan ɗay zuwa Gaza domin riga-kafin ƙananan yara.

    Unicef ya ce tarin kayayyakin agaji da suka ƙunshi magungunan yara da na'urorin adana riga-kafin ƙananan yara, na wajen yankin suna jiran ba su dama tun watan Agusta.

    Asusun ya ce kayayyakin na da matuƙar muhimmanci ga gangamin riga-kafin da ake son yi wa yaran yankin.

    Unicef ya ce an shigar da agaji mai yawa tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Gaza, amma har yanzu ba a barin wasu muhimman abubuwa sun shiga yankin ba.

    Isra'ila ta ce tana bari ana shigar da agaji Gaza, kamar yadda yarjejeniyar ta tanada, tare da yin watsi da iƙirarin cewa tana taƙaita shigar da abincin jarirai.

  7. 'An kwashe tsawon lokaci ba a yi rikicin addini ko na ƙabilanci ba Kaduna'

    Uba Sani

    Asalin hoton, Uba Sani/Facebook

    Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce an ɗauki tsawon shekara biyu da rabi ba tare da samun rikicin addini ko na ƙabilanci a jihar Kaduna ba.

    Yayin da yake jawabi a wurin wani taro da cibiyar kula da al'amura ta duniya ta shirya ranar Talata a birnin Legas, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta samu nasarar magance matsalar tsaro a jihar ta hanyar ɓullo da dabarun gwamnatin da ta haɗa kowa da kowa.

    Jawabin gwamnan na zuwa ne makonni bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi zargin cewa ana aikata kisan kiristoci a Najeriya, tare da yin barazanar ɗaukar matakin soji kan ƙasar.

    Jihar Kaduna na daga cikin jihohin Najeriya da suka yi fice da rikicin addini da ƙabilanci a shekarun baya, kuma ta fuskanci hare-haren ƴanbindiga masu garkuwa da mutane.

    Gwamna Uba Sani ya ce gwamnatin ta ɓullo da matakan masu yawa na ganin an magance matsalar tsaro a jihar.

  8. An katse intanet a Lardin Ulyanovsk na Rasha saboda yaƙin Ukraine

    Rasha

    Asalin hoton, EPA

    Hukumomi a yankin Ulyanovsk da ke Rasha sun ce za a katse intanet a sassa da dama na lardin har sai lokacin da aka kai karshen yakin Ukraine.

    Hukumomin sun kuma ce kastewar, wadda su ka ce Moscow ce ta bayar da umurnin yi, za a yi ne kusa da wasu muhimman wurare, amma zai iya shafar wasu biranen baki daya.

    Mazauna wasu yankunan Rasha ma sun bayar da rahotannin kastewar intanet din.

    A wasu lokutan a kan katse intanet a biranen Rasha ne a lokacin da Ukraine ke kai harin jirage marasa matuka domin kawo cikas ga fasahar da ke taimakawa wajen gano wurare ta GPS.

    Sai dai hukumomin sun ce katse intanet din ba zai shafi muhimman shafukan intanet ba kamar na gwamnati.

  9. An yanke wa Sarauniyar Kirifto hukuncin ɗaurin shekara 12

    ...

    Wata kotu a Birtaniya ta yanke wa wata mata ƴar asalin China hukuncin ɗaurin shekara 12 saboda samunta da hannu a wata badaƙalar kuɗin Bitcoin ta biliyoyin daloli.

    An samu Qian Zhimin da laifin yunƙurin badaƙalar fiye da bitcoin dubu 60 - wanda a yanzu ya kai darajar dala biliyan shida da rabi.

    Wata kotu a Landan ta samu bayanan yadda Ms Qian ta gudanar da wani aiki na damfarar dubban mutane a China kafin ta gudu zuwa Birtaniya.

    Masu shigar da ƙara sun ce ta shiga ƙasashen Turai masu yawa inda ta riƙa sayen gwala-gwakai masu tsada, amma ta fara ɗaukar hankali ne bayan da ta yi yunƙurin sayen wata kadara mai daraja a Landan.

  10. Waɗanda suka rasu a fashewar mota a Indiya sun kai 12

    India

    Asalin hoton, RAJAT GUPTA/EPA/Shutterstock

    Jam'iai a Indiya sun ce zuwa yanzu mutum 12 ne su ka mutu bayan fashewar wani abu a mota jiya Litinin a birnin Delhi.

    Hukumar bincike ta kasar NIA, ta karbe ragamar binciken karkashin dokar yaki da ta'addanci.

    Rahotanni a kafafen yada labarai na Indiya sun ce bisa bidiyon da aka samu na CCTV, masu bincike na zargin wanda ya tayar da abin fashewar, wani likita dan kashmir da ke zama a Delhi ne ke zaune a kujerar direba.

    Akwai kuma rahotannin da ke cewa an kama wasu yan uwan wanda ake zargin daga kauyen su mai suna Pulwama a yankin kashmir da ke karkashin ikon Indiya, ciki har da mahaifiyar sa.

    Wakiliyar BBC ta ce Firaminista Narendra Modi ya sha alwashin za a hukunta wadanda su ka kitsa kai harin.

  11. Majalisar Isra'ila tana tattauna ƙudirin hukuncin kisa kan 'laifin ta'addanci'

    Netanyahu

    Asalin hoton, AFP

    An gabatar da wani ƙuduri a gaban majalisar dokokin Isra'ila domin yin dokar hukuncin kisa kan wanda aka kama da laifin ta'addanci a ƙasar.

    Ɗan majalisar ƙasar mai tsattsauran ra'ayi, Itama Ben Gvir ne ya gabatar da ƙudirin, inda ya yi barazanar ficewa daga jam'iyyarsa idan har ba a amince da ƙudurin ba.

    Wakilin BBC ya ce akwai alamar hukuncin zai fi aukuwa ne a kan Falasɗinawa da aka kama da laifin ƙaddamar da hare-hare a Isra'ila.

    Sai dai hukumomi a Falasɗinu sun kira ƙudurin dokar da wani matakin zalunci da ake yunƙurin ɗauka kan mutanen yankin Falasɗinu.

  12. Turkiyya na zargin abokin adawar shugaban ƙasar da laifuka 140

    Turkiyya

    Asalin hoton, EPA

    Masu shigar da kara a Turkiyya sun sanar da tuhume-tuhume fiye da 140 wa Ekrem Imamoglu, babban abokin hamayyar shugaba Recep Tayyip Erdogan da ke gidan yari.

    Idan aka tabbatar da laifukan da ake zarginsa, zai iya fuskantar daurin shekaru dubu biyu.

    Akasarin tuhume-tuhumen na da alaka ne da zargin zamba ko yaudara.

    An kama mista Imamoglu, wanda a baya shi ne Magajin Garin Istanbul, a watan Maris kan laifin cin hanci da ta'addancin, laifukan da ya musanta aikatawa.

    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam a turai ta nemi hukumomi a Turkiyya su yi watsi da tuhume-tuhumen su kuma sake shi. Ana kuma tuhumar mutum fiye da 400 tare da shi.

  13. Wani abin fashewa ya yi ajalin mutum 12 a Pakistan

    Pakistan

    Asalin hoton, AFP

    Wani abin fashewa ya yi ajalin aƙalla mutum 12 a Islamabad, babban birnin ƙasar Pakistan kamar yadda rahotanni daga ƙasar suka nuna.

    Haka kuma bayan waɗanda suka rasu, akwai wasu waɗanda suka jikkata da a yanzu suke samun kulawa a asibiti, ciki har da waɗanda suke cikin matsanancin hali.

    Rundunar ƴansandan ƙasar ta ce tana gudanar da bincike domin gano musababbin lamarin domi kare sake aukuwarsa.

    Fashewar ta zo ne kwana ɗaya bayan wata mota ta fashe a babban birnin India, Delhi, inda mutane da dama suka rasu.

  14. Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP

    PDP

    Asalin hoton, PDP/X

    Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta sake dakatar da jam'iyyar PDP daga gudanar da babban taronta da take shirin yi a garin Ibadan na jiyar Oyo.

    Wannan shi ne karo na biyu da kotu ta hana gudanar da taron, wanda babbar jam'iyyar hamayyar ke shirin yi a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamban da ake ciki.

    Haka kuma kotun ta hana INEC sa ido kan babban taron ko kuma amincewa da sakamakon taron wanda ake sa ran fitar da sababbin shugabannin jam'iyyar.

    Sai dai kafin wannan hukuncin na biyu, wata kotun a jiyar Oyo ta umarci jam'iyyar da ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryenta na babban taron, wanda hakan ya haifar taraddudi.

    Mai shari'a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, bayan tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya shigar da ƙara, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Lamido ya shigar da ƙara ne yana buƙatar kotu ta dakatar da jam'iyyar daga zaɓen fitar da sababbin shugabanni, inda ya ƙalubalanci abin da ya kira hana shi shiga takarar da ya ce an yi.

  15. NAFDAC za ta fara aiwatar da haramcin sayar da barasa a leda da ƙananan kwalaba

    Nafdac

    Asalin hoton, Nafdac/X

    Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta ce za ta fara aiwatar da dokar hana haɗawa da sayar da barasa a leda da ƙananan kwalabe da ba su kai mil 200 ba daga watan Disamban wannan shekarar ta 2025.

    Darakta-janar ta hukumar, Mojisola Adeyeye ce ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da manema labarai a ranar Talata a Abuja.

    "An haramta amfani da barasan ne domin tabbatar da lafiyar matasa manyan gobenmu," in ji Adeyeye, sannan ta ƙara da cewa daga lokacin ba za a sake tsawaita wa'adin ba, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Ta ce yadda ake samun yawaitar barasa a leda da ƙananan kwalabe ya taimaka wajen yawaitar barasan a hannun mutane saboda sauƙinsa.

    "Mutane suna samun barasa cikin sauƙi da rahusa, wanda hakan ya sa ake ƙara samun mashaya a tsakanin al'umma," in ji ta.

  16. Ecuador ta kwashe fursunoni 300 daga gidan yarin da mutum 30 suka rasu

    Fursuna

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ecuador ya ce an sauya wa wasu fursunoni 300 masu hatsari wurin zama zuwa wani gidan yari mai matakan tsaro kwana guda bayan kashe sama da fursunoni 30 sakamakon bore a yankin kudancin ƙasar.

    Wakilin BBC ya ce Shugaba Daniel Noboa ya ce kungiyoyi masu aikata laifuka na son kalubalantar gwamnatin ta hanyar kaddamar da wata manufa, amma gwamnati ta dauki mataki.

    Daga cikin wadanda aka sauya wa gidan yari har da tsohon mataimakin shugaban Equador Jorge Glas.

  17. Majalisar dattawan Amurka ta amince da kasafin kuɗin dawo da ayyukan gwamnati

    Amurka

    Asalin hoton, Reuters

    Majalisar dattijan Amurka ta kada kuri'ar amincewa da wani kudurin kasafin kudi domin dawo da ayyukan gwamnati da aka dakatar.

    'Yan jam'iyyar Republican sun samu kuri'u 60 da suke bukata bayan da wasu yan Democrats suka goyi bayan kudirin duk da bai kunshi kudaden tafiyar da inshowar lafiya ba da suke jayayya a kai ba.

    A gobe Laraba ake sa ran kudirin zai tsallaka majalisar wakilai domin amincewa kafin a tura wa shugaba Trump ya sa hannu.

  18. Miliyoyin ƴan gudun hijira za su shiga ƙunci saboda hunturu - MDD

    MDD

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa miliyoyin 'yan gudun hijira za su fuskanci matsanancin yanayin hunturu sakamakon kalubalen raguwar kayan jinkai, yayin da ake tunkarar yanayin sanyi.

    Wakilin BBC ya ce hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da 'yan gudun hijirar Syria miliyan daya sun koma gida bayan faduwar gwamnatin Bashar Al Assad.

    Hukumar ta yi kira ga masu hannu da shuni da su taimaka da tallafin dala miliyan 35 bayan rage kudaden tallafin da gwamnati ke yi ya jefa ayyukanta cikin mawuyacin hali.

    Ta ce kudaden za su taimaka wajen kai tallafin barguna da magani da abin dumama daki ga yan gudun hijirar Syria da Afghanistan da kuma Ukraine.

  19. An kammala kilomita 39 a titin Abuja-Kaduna-Kano - Gwamnati

    Abuja Kaduna

    Gwamnatin Najeriya ta ce an kammala kilomita 39 a ɓangarori daban-daban na titin Abuja–Kaduna–Kano da ake ci gaba da yi.

    Ƙaramin ministan ayyuka na Najeriya Barista Bello Goronyo ne ya bayyana haka, inda ya ce gwamnatin ƙasar na sa ido sosai kan yadda kamfanin da ke kwangilar, Infiouest International Limited ke gudanar a aikin domin tabbatar da an kammala sashe na 1 na aikin titin kafin watan Afrilun shekarar 2026.

    Ya ce zuwa yanzu an buɗe sababbin ɓangarori guda takwas domin aikin ya ƙara sauri, inda ya ce suna da tabbacin titin zai yi ƙarkon da zai kai shekara 50 ana amfani da shi.

    "Gwamnatin Bola Tinubu ba gina tituna kaɗai take yi ba, tana ma yunƙurin tabbatar da titunan suna da inganci da ƙarko. Burinsa shi ne shugabannin da za su nan gaba su mayar da hankali kan wasu ayyukan daban, ba gyare-gyaren tituna ba," in ji Goronyo, kamar yada jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Ministan ya kuma yaba wa gwamnatin tarayya bisa sakin kuɗi isassu domin tabbatar da aikin na tafiya kamar yada ake so.

  20. An buɗe taron sauyin yanayi a Brazil

    COP30

    Asalin hoton, Getty Images

    An bude babban taron sauyin yanayi na duniya wato COP30 a birnin Belem na Brazil Da yake jawabi ga wakilai dubu 50 daga sassan duniya.

    Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva ya kira taron a matsayin na aiwatarwa.

    Ya ce matsalar dumamar yanayi ta jefa miliyoyin mutane cikin yunwa ta talauci.

    Donald Trump - wanda ya bayyana sauyin yanayi a matsayin wata damfara - bai aika wata tawagar kirki ba ta Amurka.