Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 28 ga watan Maris 2025
Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Aliyu Jaafar da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

Asalin hoton, Bola Tinubu/Facebook
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yi tir da kashe matafiya da aka yi a jihar Edo, inda ya buƙaci a gaggauta nema tare da kama waɗanda suka aikata laifin.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ya fitar yau Alhamis, Tinubu ya bai wa ƴan sanda da sauran jami'an tsaro umarnin gudanar da cikakken bincike da nufin hukunta masu laifi.
"Na kaɗu matuka da jin wannan mummunar labari na kisan wasu matafiya," in ji Tinubu.
Ya jajantawa iyalan waɗanda aka kashe musu ƴan uwa a lamarin, inda ya tabbatar da cewa ba za a bari ɓata-gari su riƙa zubar da jinin bayin Allah ba a Najeriya.
Shugaban ya ce ɗaukar doka a hannu ba shi da muhalli a Najeriya - kuma dukkan ƴan Najeriya na da ƴancin yin tafiya zuwa kowane sassa a faɗin ƙasar.
Ya kuma yaba wa gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo da shugabannin al'umma a jihar bisa ɗaukar matakin domin hana yaɗuwar lamarin.

Asalin hoton, Reuters
Tsohon firaministan Kenya Raila Odinga ya isa Sudan ta Kudu domin taimakawa wajen shiga tsakani, a wani yunƙuri na kwantar da tarzoma tsakanin Shugaba Salva Kiir da mataimakin shugaban ƙasa na farko, Riek Machar.
Majalisar ɗinkin duniya ta yi gargaɗin cewa Sudan ta Kudu na gab da sake faɗawa cikin mumunan rikici bayan tsare Mr Machar da aka yi a gidansa a ranar Laraba.
Alaƙa tsakanin shugabannin biyu na ci gaba da yin tsami a makonnin da suka gabata.
Ana kuma samun ƙaruwar rikice-rikicen ƴan bindiga.

Asalin hoton, Government House Gombe
Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta yi Alla-wadai da kisan wasu matafiya da gungun mutane suka yi a jihar Edo.
Wata sanarwa da ta fito daga wajen shugaban ƙungiyar gwamnonin, Muhammad Inuwa Yahaya, ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin kama waɗanda suka aikata "wannan ta'asar" don hukunta su.
Ƙungiyar ta kwatanta harin a matsayin ƙeta hakkin ɗan'adam, inda ta ce ba za ta lamaunci ɗaukar doka a hannu ba.
Ta kuma jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ƴan uwansu a lamarin.
"Mun damu matuka kan kisan bayin Allah da ba su aikata komai ba, da kuma irin yadda aka kashe su," in ji Inuwa Yahaya wanda kuma ya kasance gwamnan Gombe.
Ya ce abin da aka aikata ya saɓa wa doka, don haka ya zama dole hukumomi su gudanar da cikakken bincike kan yadda aka kashe mutanen ta hanyar cinna musu wuta.
Gwamna Inuwa Yahaya ya nanata cewa kowane ɗan Najeriya yana da ƴancin yin tafiya zuwa ko'ina, ba tare da nuna bambancin addini ba.
Ya buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakin da ya dace don hana afkuwar irin haka a nan gaba, inda ya yi kira da a kwantar da hankali.

Greenland ta sanar da kafa sabuwar gwamnati sa'oi kaɗan kafin ziyarar da mataimakin shugaban Amurka JD Vance zai kai yankin ba tare da gayyata ba.
Jam'iyyu huɗu cikin biyar ɗin da suka lashe kujeru a zaɓen ƴan majalisu da aka yi a farkon wannan watan sun kafa haɗaka mai ƙarfi.
Firaminista mai jiran gado Jens- Frederik Nielsen ya jaddada muhimmancin haɗin kai, a lokacin da mutanen yankin ke fuskantar matsi da takura daga ƙasashen waje.
Kalamansa na zuwa ne bayan shugaba Trump ya sha nanata cewa Amurka na neman karɓe iko da yankin na Greenland.

Asalin hoton, STR/AFP via Getty Images
Aƙalla mutum 144 sun mutu yayin da wasu 736 suka jikkata a Myanmar bayan girgizar ƙasa da aka yi a tsakiyar ƙasar a safiyar yau.
Shugaban gwamnatin mulkin ƙasar Min Aung Hlaing ne ya faɗi hakan, inda ya ce ana hasashen adadin zai haura hakan.
Shugaban gwamnatin ya ce mutum 96 sun mutu a yankin Nai Pyi Taw yayin da 132 suka jikkata, haka-zalika mutum 18 sun mutu a yankin Saigaing 300 kuma sun jikkata, sai yankin Mandalay inda mutum 30 suka mutu.

Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya yi Alla-wadai da kashe wasu matafiya da aka yi a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar arewa maso gabashin Esan a ranar Alhamis da ta gabata, wato 27 ga Maris, inda ya bayyana kisan da na dabbanci.
Ana ta dai yaɗa wasu faya-fayan bidiyo, wanda a ciki aka nuna wasu matasa sun zagaye wasu mutane da ake tunanin mafarauta ne ƴan arewa da suka taso daga kudancin ƙasar za su koma gida wataƙila domin bikin sallah.
A wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan jihar, Fred Itua ya fitar, ya ce, "Binciken farko-farko ya nuna cewa matafiya ne da suka taso daga Fatakwal na jihar Rivers suka ratso ta garin, sai ƴan banga suka kama su da tunanin cewa ɓatagri ne."

Asalin hoton, EPA
Shugaba Vladimir Putin ya sha alwashin ''ƙarfafa jagorancin Rasha a yankin maƙurar duniya na Artic'' yayin da yake gargaɗin cewa ''rikici kan wasu yankuna a yankin'' na tsananta.
Misalin farko da ya bayar shi ne yadda Trump ke ƙoƙarin mallakar yankin Greenland.
Sai dai shugaban Rashan bai soki yunƙurin takwaransa na Amurka ba.
Wani abu da ke nuna alamun goyon baya, ganin cewa Amurka da Rasha na ƙoƙarin sake gina alaƙarsu.
''A taƙaice dai, da gaske Amurka take yi game da shirinta kan Greenland'' a cewar Putin da yake jawabi a birnin Murmansk.
''Wadannan shirye-shiryen na da daɗaɗɗiyar tarihi. Kuma alamu sun nuna Amurka za ta ci gaba da yin dabaru wajen cimma burinta''
A lokacin da Joe Biden ke kan mulki, Rasha da Amurka na fitowa fili suna sukar junansu.

Asalin hoton, EPA
Gwamnatin mulkin sojin Myanmar ta miƙa buƙatar taimako ga ƙasashen duniya, wanda ka kasafai take yin hakan ba, bayan wata girgizar ƙasa da aka samu a tsakiyar ƙasar mai ƙarfin maki 7.7.
Wani mai magana da yawun gwamnatin da ke babban birnin ƙasar Naypyidaw, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa suna buƙatar agaji cikin gaggawa.
Girgizar ƙasar ta fi ƙamari ne a kusa da birnin Mandalay wanda ke da mutane miliyan ɗaya da rabi.
An sanya dokar ta-ɓaci a yankuna shida na ƙasar.
Hukumar kula da ƙasa da ma'adinai na Amurka ta yi gargaɗin cewa tasirin Iftilain zai iya faɗaɗa, kuma akwai yiwuwar dubban mutane sun mutu.
Girgizar ƙasar ta shafi makwafciya Thailand inda hukumomi suka ce mutane uku sun mutu, 68 na asibiti, yayin da ake ci gaba da neman mutane fiye da 80 bayan wani gini mai tsawo ya rushe.

Gwamnatin jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ta raba tallafin kuɗi ga iyalan waɗanda gobarar tankar man fetur ta rutsa da su.
Ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun jama'a ne suka bayar da tallafin tun lokacin da gobarar ta tashi a bara, inda aka samu fiye da naira miliyan dubu daya.
Sai dai gwamnatin ta ce ba duka bane suka zo hannu.
Zuwa yanzu an raba wa mutum 210 naira miliyan 840.
An bai wa kowanne naira dubu ɗari biyar a hannu, inda daga bisani za a saka sauran miliyan 3 da rabi a asusun ajiyarsu ta banki.
A watan Oktoban bara ne wata motar dakon mai ta kife a garin Majiya na ƙaramar hukumar Taura da ke jihar Jigawa, bayan ta taso daga jihar Kano a kan hanyarta ta zuwa jihar Yobe.
Daga bisani motar ta kama da wuta wanda ya yi sanadiyar kashe mutane fiye da 200 da ake tunanin suna ƙoƙarin ɗibar fetur ɗin da ke zuba a motar da ta faɗi ne.


A cikin shirin Ku San Malamanku na wannan mako mun kawo muku tattaunawa da malamin addinin Musulunci Sheikh Hamma Adama Biu.
Sojojin Isra'ila sun umurci mazauna wasu yankunan kudancin Beirut su fice.
Sojojin sun ce za su kai hari ne kan ƴan ƙungiyar Hezbolla da ke kudancin Lebanon waɗanda suka ce sun harba rokoki biyu zuwa Isra'ila.
Sun ce sun yi nasarar kakkaɓo ɗaya daga cikin rokokin yayin da ɗayan kuma ya gaza tsallakowa kan iyaka.
Tun da farko ministan tsaron Isra'ila Isreal Katz, ya yi gargaɗin cewa idan har ba a samu kwanciyar hankali a arewacin Isra'ila ba, to hakazalika ba za a samu kwanciyar hankali a Beirut ba.
Sai dai Hezbollah ta ce ba ta da hannu a harba rokokin, kuma tana mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila da aka ƙulla a watan Nuwamba.
Ɓangarorin biyu na ci gaba da zargin junansu da ƙin bin ƙa'idojin yarjejeniyar.

Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a Sipaniya ta ce mai horas da ƙungiyar ƙwallon kafa ta Real Madrid, Carlo Ancelotti, zai gurfana a gabanta a ranar Laraba bisa zargin shi da ha'inci wajen biyan haraji.
Masu gabatar da ƙara na zargin shi da ƙin bayyana fiye da dala miliyan ɗaya na kuɗaɗen da yake samu na ƙimar kallonsa a talibijin a lokacin da yake horar da Real Madrid.
Sai dai Mista Ancelotti wanda yake cikin fitattun masu horas da ƴanƙwallon ƙafa a duniya da suka fi samun nasara, ya musanta aikata laifin.

Asalin hoton, FB/Sultanate Council
Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar, wanda shi ne shugaban Majalisar ƙoli ta addinin Musulunci a ƙasar ya buƙaci al'umma su duba jinjirin watan Shawwal na shekarar Musulunci ta 1446 (Bayan Hijira) a gobe Asabar.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar Sarkin Musulmin ta fitar a yau Juma'a, wadda ta samu sa hannun shugaban kwamitin da ke bai wa sarkin Musulmi shawara kan harkokin addinin Musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaidu.
Sanarwar ta ce "Ana sanar da Musulmai cewa Asabar, 29 ga watan Maris, 2025, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Ramadan, ita ce ranar da za a yi duban jinjirin watan Shawwal na shekarar 1446 (Bayan Hijira).
"Saboda haka ana buƙatar Musulmai su dubi watan a ranar Asabar, sannan idan sun gani su kai rahoto ga hakimi ko dagacin yankinsu, wanda shi kuma zai isar da saƙon ga Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar."
Ganin jinjirin watan Shawwal ne zai tabbatar da ƙarshen azumin Ramadan, inda za a gudanar da sallar Eid el-Fitr a ranar ɗaya ga watan na Shawwal.
Idan aka ga jinjirin watan a ranar Asabar, hakan na nufin za a yi hawan sallah ƙarama a ranar Lahadi bayan yin azumi 29, sai dai idan aka gaza ganin watan, Sarkin Musulmin - bisa al'ada - zai bayar da sanarwar cike azumi 30 kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Asalin hoton, TINUBU FACEBOOK
Za a gudanar da wata addu'a ta mausamman ga Najeriya yau Juma'a a babban masallacin ƙasa da ke Abuja, a matsayin wani ɓangare na murnar cikar shugaban ƙasar shekara 73 da haihuwa.
Fadar shugaban ƙasar ce ta sanar da haka a cikin wata sanarwa da mai bashi shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.
Sanarwar ta ce Tinubu zai haɗu da al'umma Musulmi a massalacin a yau Juma'a domin addu'ar, domin zagayowar ranar haihuwarsa wadda za ta kasance gobe Asabar 29 ga watan Maris.
Sanarwar ta ce za a yi amfani da damar wajen yin godiya ga Allah da ya ba shi tsawon rai kuma yake taimakasa gudanar da gagarumin aikin jagorantar Najeriya.
Sanarwar ta ce shugaba "Tinubu ya yi imanin cewa gabatar da addu'o'i a matsayin ƙasa ɗaya wani babban abu ne dai zai taimaka wajen kai ƙasar ga ci gaba da zaman lafiya."
Tinubu ya kuma buƙaci ɗaukacin al'ummar musulmi su yi addu'oi'n ga ƙasar a duk inda suke.
Shugaban ƙasar ya kuma miƙa godiyarsa ga ƴan Najeriya bisa goyon bayan da suke ba gwamnatinsa a ƙoƙarin da yake yi ba dare ba rana wajen bunƙasa tattalin arziƙi da inganta tsaro da kuma faɗaɗa samun damarmaki ga ƴan ƙasar.
Ya ce '' ina matuƙar godiya ga Allah na rayuwar da ya ba ni damar hidimtawa Najeriya. A yayin da nake murnar zagoyowar ranar haihuwata, zuciyata a cike take da sabuwar fata ga Najeriya. Ina buƙatar ƴan Najeriya su yi addu'a, da haɗin kansu zamu shawo kan matsalolinmu kuma mu gina ƙasar da kowa zai amfana'."
Tinubu ya kawo sauye-sauye da dama a ɓangaren tattalin arziƙin ƙasar tun bayan hawan sa kan mulki a shekara 2023, sai dai al'ummar ƙasar na kokawa kan yadda tsare-tsaren gwamnatin ke jefa su cikin ƙunci, sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi da kuma talauci.
Wasu masana a harkar jin sauti na ganin cewa yawan amfani da abin sauraron sauti, wato headphones na iya yin illa ga yadda mutum ke iya tantance sautuka daban-daban.

Asalin hoton, Reuters
An sami girgizar ƙasa mai ƙarfi a tsakiyar Myanmar wanda ƙarfinta ya kai har Thailand da Yunnan da ke kudu maso yammacin China.
Hukumar kula da yanayi na Amurka ta ce girgizar ƙasar ta kai maki 7.7 kuma tana da zurfin kilomita 10.
Girgizar ƙasar ta fi girma a kusa da birnin Mandalay.
Hotuna sun nuna yadda wata gada ta ruguje cikin kogin Irrawaddy da kuma yadda wasu tituna suka tsage a babban birnin ƙasar Naypyidaw.
Mazauna birin Bangkok, babban birnin Thailand sun fito kan tituna da gudu bayan gidajensu sun soma girgiza.
Wani gini mai tsawo da ake kan gina wa ya ruguje.
Ƴansanda sun ce gwamman ma'aikata sun maƙale a ciki.
A yanzu haka gwamnati na gudanar da taron gaggawa kan iftila'in.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, AFP
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayar da shawarar sanya gwamnatin riƙo a Ukraine bisa jagorancin majalisar ɗinkin duniya.
Da yake magana a Murmansk, Putin ya ce idan anyi haka, daga bisani sai a gudanar da zaɓe domin miƙa mulki ga abin da ya kira ''gwamnatin da za ta iya'' wadda za ta iya fara tattaunawar zaman lafiya.
A nasu martanin, wani minista a Ukraine ya ce a ko da yaushe Mista Putin na bijiro da batutuwa na rashin hankali domin jinkirta samun zaman lafiya.
Wani mai magana da yawun majalisar tsaron Amurka ya ce kundin tsarin mulki da alummar Ukraine ne kawai za su iya zaɓen gwamnatin ƙasar.

Asalin hoton, Huw Evans Picture Agency
Sarki Charles na Birtaniya ya yi zaman asibiti na ɗan gajeren lokaci sakamakon matsalolin da ya samu game da magungunan cutar daji.
Ba a faɗi takamaimai matsalolin ba amma an soke tarukan da aka shirya zai yi da jakadu da yammacin ranar Alhamis.
Tuni aka kuma soke ayyukan da aka tsara zai gudanar a yau Juma'a.
A watan Fabarairun bara ne aka gano Sarki Charles, mai shekara saba'in da shida yana ɗauke da wani nau'in cutar daji da ba a bayyana ba.
Ya koma gudanar da hidindimunsa watanni biyu bayan nan duk da cewa yana ganin likita duk mako.

Asalin hoton, Getty Images
Firaiministan Canada, Mark Carney ya ce daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin ƙasarsa da Amurka ta zurfafa haɗin gwiwar tattalin arziki da haɗin kai wajen tabbatar da tsaro ta zo ƙarshe.
Ya ce ya zama dole Canada ta rage yawan dogaro kan Amurka saboda a yanzu Washington ba abar dogaro ba ce.
Mista Carney ya ce ba su san mataki na gaba da Amurka za ta ɗauka ba, amma abin da suka sani shi ne kowa a gida sarki ne kuma za su iya tsara makomarsu.
Mista Carney yana magana ne bayan da Shugaba Trump ya sanar da sabbin haraji kan dukkanin motocin da aka shiga da su Amurka daga ƙasashen waje - wani mataki da zai yi tasiri sosai kan Canada.
Firaiministan ya yi alƙawarin ɗaukan matakan ramuwar gayya da za su yi gagarumin tasiri kan Amurka wanda kuma ba za su girgiza Canada ba.