Sai da safe
Nan muka kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi.
Ku biyo mu gobe da safe domin samun wasu sababbi.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/09/2025.
Isiyaku Muhammed
Nan muka kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi.
Ku biyo mu gobe da safe domin samun wasu sababbi.

Asalin hoton, Reuters
Hukumomi a ƙasar Namibia sun tura daruruwan sojoji domin kashe gobarar da ta kama kusan 1 bisa 3 na wani muhimmin gandun daji.
Etosha National Park na ɗaya daga cikin fitattun wurare da masu yawon bude-idanu ke zuwa a kudancin Afirka.
Wajen ya yi fice sosai saboda filin da yake da shi mai faɗin gaske da kuma yalwar gishiri, wanda ake iya hango shi tun daga sararin samaniya - fari-fat.
Ma'aikatar muhalli ta ƙasar ta ce sama da mako ɗaya wutar take ta ci, kuma ta yi illa sosai ga gandun.
Gandun da ke arewacin kasar ta Namibia - wadda yawancinta hamada ce - na ɗauke da nau'ukan dabbobi masu shayarwa, musamman baƙin karkanda da ke fuskantar ƙarewa yanzu a duniya.

Asalin hoton, Dangote Group
Gwamnatin Najeriya ta nemi ƙungiyar manyan ma'aikatan man fetur da gas da kuma matatar Dangote su jingine rikicin da ke tsakaninsu, kuma ta kira su domin shiga tsakani.
A yau Lahadi ne ƙungiyar ta Petroleum and Natural Gas Senior Staff Association of Nigeria (PENSASSAN) ta sanar da fara yajin aiki a ƙasa baki ɗaya sakamakon abin da ta kira korar ma'aikata da matatar Dangote ta yi bayan sun ayyana sha'awar shiga ƙungiyar.
Ministan Ƙwadago Maigari Dingyadi ya bayyana cewa wakilan ɓangarorin biyu za su gana da juna a hedikwatar ma'aikatarsa da ke Abuja.
"Ina neman ɓangarorin biyu da su tunan muhimmancin ɓangaren fetur da gas ga Najeriya, saboda shi ne ƙashin bayan tattalin arzikin ƙasa," a cewar ministan kamar yadda wata sanarwa daga ofishinsa ta bayyana a yau Lahadi.
"Yajin aiki ba asarar kuɗin shiga kawai zai jawo ga ƙasa ba, zai ƙaro wahalhalu ga 'yan Najeriya. Daga baya ma zai yi tasiri a ɓangaren tsaron ƙasa," in ji sanarwar da Patience Onuobia ta fitar a madadin ministan.

Asalin hoton, Reuters
Aƙalla mutum ɗaya aka kashe tare da raunata wasu tara bayan wani ɗanbindiga ya buɗe wa masu ibada wuta a jihar Michigan da ke Amurka.
Rundunar 'yansanda ta ce harin da aka kai a cocin Church of Jesus Christ of Latter-day Saints ya faru ne yayin da ɗaruruwan mutane ke tsaka da ibadar Lahadi.
Wanda ake zargin namiji ne mai shekara 40, kuma an ce ya cinna wa cocin wuta amma an kashe ta. Sai dai ana fargabar za a samu ƙaruwar waɗanda harbin ya ritsa da su idan aka samu damar shiga cikin ginin.
'Yansanda sun ce sun harbe maharin kuma babu wata sauran barazana.
Denmark ta haramta wa mazauna ƙasar amfani da jirage marasa matuƙa a makon nan.
Tun daga ranar Litinin ne aka dinga ganin manyan jirage marasa matuƙa na shawagi a sararin samaniyar ƙasar, ciki har da waɗanda suka kusanci sansanonin sojin ƙasar, da waɗanda suka sa aka dakatar da tashin jiragen sama.
Haramcin zai fara aiki daga Litinin zuwa Juma'a. Nan gaba a makon ne kuma ƙasar za ta karɓi baƙuncin tarukan Tarayyar Turai.
Har yanzu ba a san wanda ke tayar da jiragen ba, amma Firaministar Denmark Mette Fredriksen ta nuna cewa akwai yiwuwar Rasha ce.

Asalin hoton, Getty Images
Kotu ta yanke wa tsohon ministan noma da raya karkara a China hukuncin kisa bayan kama shi da laifin cin hanci da rashawa.
Kotun da ke lardin Jilin ta ce Tang Renjian ya karɓi rashawar kuɗi da gidaje da suka kai darajar fiye da dala miliyan 37 lokacin da yake kan muƙaminsa daga 2007.
Sai dai kotun ta ce ta dakatar da aiwatar da hukuncin kisan nasa tsawon shekara biyu saboda ya masa laifinsa.
Jam'iyyar kwamunisanci mai mulkin China ta kori Mista Tang a watan Nuwamban 2024, wata shida bayan fara bincike a kan sa da kuma sauke shi daga muƙaminsa.

Asalin hoton, AFP
Ɓangaren soji na ƙungiyar Hamas ya bayyana cewa biyu daga cikin Isra'ilawan da suke garkuwa da su, sun ɓace bayan luguden wuta da Isra'ila ta yi a wasu garuruwa na birnin Gaza da ke yankin na Falasɗinu da ke fama fama da hare-hare.
Rundunar ta al-Qassam ta buƙaci Isra'ila ta tsagaita wuta na aƙalla kwana ɗaya domin ta samu nasarar ceto mutanen guda biyu.
Sojojin Isra'ila dai na ci gaba da kutsawa cikin birnin Gaza ne da zimmar mamaye tsakiya da arewacin binin na Gaza.
A daidai lokacin da ya rage awanni kaɗan kafin ganawar Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da takwaransa na Amurka, Trump ya ce akwai labari mai daɗi,
Trump ya rubuta cewa, "mun samu wata dama babbar domin gyara abubuwa a yankin Gaba ta Tsakiya," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar manyan ma'aikatan kamfanonin mai da iskar gas ta Najeriya, PENGASSAN ta fara yajin aikin sai mama ta gani domin nuna rashin amincewa da sallamar ma'aikata da Matatar Dangote ta jihar Legas ta yi a makon jiya, lamarin da ya jawo musayar yawu.
Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Lumumba Okugbawa ne ya bayyana hakan, inda ya ce za su fara yajin aikin ne ba tare da ɓata lokaci ba.
"Mun buƙaci dukkan mambobin ƙungiyar PENGASSAN su dakata da zuwa aiki daga yau Lahadi 28 ga watan Satumba," in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Tun da farko dai ƙungiyar ta buƙaci mambobinta da su dakata da sayar wa matatar ta Dangote da ɗanyen mai da iskar gas.
Ana dai ta takun-saƙa ne tsakanin matatar da ƙungiyar tun bayan da matatar ta sanar da koron wasu ma'aikata, lamarin da ƙungiyar ta ce ba za ta lamunta ba.
Wasu daga cikin ma'aikatan dai sun yi zargin cewa an kore su ne daga aiki saboda sun shiga ƙungiyar ta PENGASSAN.

Asalin hoton, Reuters
Hare-haren Rasha waɗanda aka ce an yi sama da awa 12 ana luguden wuta a sassan ƙasar Ukraine sun kashe aƙalla mutum huɗu, sannan sama da mutum 70 suka jikkata.
Shugaban Ƙasa Volodymyr Zelensky ya ce waɗanda suka rasu a babban birnin ƙasar, Kyiv suke, inda aka harba mafi yawan bama-baman.
Ya ce daga cikin waɗanda suka rasu har da wani ƙaramin yaro mai shekara 12.
Zelensky ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa za ta mayar da martani, inda ya ƙara da cewa, "hare-haren na nuna cewa Rasha na so a ci gaba da gwabza yaƙin ne."
Sai dai Rasha ta ce ta kai hare-haren ne a kan makaman Ukraine da wasu kamfanonin da suke taimakon ƙasar a yaƙin.
Daga cikin kamfanonin da hare-haren suka illata akwai gidan burodi da kamfanin mota da wasu gidaje kamar yadda Zelensky ya bayyana.
Zelensky ya ce yankunan Zaporizhzhia da Khmelnytskyi da Sumy da Mykolaiv da Chernihiv da Odesa na cikin wuraren da hare-haren suka illata.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Dubban mutane ne suka halarci zanga-zangar nuna kyamar kisan mata a birnin Buenos Aires, inda suke neman a yi adalci ga wasu mata biyu da aka azabtar har suka mutu, a wani al'amari da ya girgiza ƙasar Argentina.
An yi ta tafka muhawara a kan kisan gillar da aka yi wa Lara Gutierrez 'yar shekaru goma sha biyar da kuma Morena Verdi del Castillo, ƴar shekara ashirin a duniya.
Ƴansanda sun yi imanin cewa wata kungiyar masu safarar muggan kwayoyi ce ke da alhakin kisan, kuma an yada shi a bidiyo domin ya zama izina ga wasu.
Wakilin BBC ya ce 'yan sanda sun kama mutane goma sha biyu da ake zargi, amma har yanzu ana ci gaba da neman mutumin da aka ce shine shugaban kungiyar makasan.

Asalin hoton, AFP
Kungiyar tsaro ta NATO ta shaidawa kanfanin dillancin labarai na Reuters cewa tana ci gaba da inganta ayyukanta a tekun Baltic domin mayar da martani ga kutsen jirage marasa matuka da aka samu a Denmark, ciki har da girke garkuwar tsaron sararin samaniya.
Ana sa ran sabbin matakan za su taimaka wajen inganta ayyukan kungiyar da aka kaddamar a farkon wannan shekarar, bayan da aka wayoyin lantarki na karkashin ruwa da kuma bututun iskar gas a yankin Baltic.
Kasashe da dama na NATO sun zargi Moscow da keta sararin samaniyar su da jirage marasa matuka, to amma jiya Asabar ministan harkokin wajen Rasha ya gargadi NATO da Tarayyar Turai kan duk wani yunkuri na yi wa Rasha kutse.
A jawabin da ya yi a zauren Majalisar Dinkin Duniya, Sergei Lavrov ya yi watsi da zargin da ake yi wa Moscow na shirin kai hari kan makwabtanta na yammacin Turai, yana mai cewa don haka ita ma Rasha ba za ta lamunci haka ba.

Asalin hoton, X/@AlikoDangote
Matatar man fetur ta Dangote ta janye dakatar da sayar da man fetur a naira. inda ta ce abokan hulɗarta za su iya sayen man ta hanyar amfani da naira maimakon dala.
An samu canjin ne kimanin awa 24 bayan matatar ta sanar da dakatarwar, bayan shugaban hukumar tattara haraji na Najeriya, kuma shugaban kwamitin amfani da naira a kasuwancin man fetur, Dr. Zacch Adedeji ya shiga tsakani.
Gwamnatin Najeriya ce ta hannun kamfanin man fetur na gwamnatin ƙasar wato NNPCL ta kafa kwamitin domin ganin ana sayar da man fetur ga dilolin cikin Najeriya a naira maimakon dala.
A ranar Juma'ar da ta gabata ce matatar ta Dangote ta sanar da dakatar da amfani da naira wajen sayar da fetur, lamarin da ta ce zai fara aiki a ranar Asabar, 28 ga watan Satumba saboda a cewarta nauyin ya mata yawa, kuma ba za ta iya ci gaba ba.
Sai dai kuma a ranar Asabar ɗin matatar ta sake fitar da wata sanarwa, inda ta ce za ta ci gaba da sayar da fetur ɗin a naira.

Akalla mutum 39 ne suka mutu inda sama da hamsin suka jikkata sakamakon wani turmutsutsi da aka samu a wajen wani taron siyasa a jihar Tamil Nadu da ke kudancin Indiya.
Mutanen sun cika makil a wajen taron ne don ganin fitaccen jarumin fim a kasar da ya koma dan siyasa, wato Vijay.
Ƴan sanda sun ce dubban mutanen da suka taru, sun zarce yadda aka zata. Daga baya Vijay ya ce ya yi bakin cikin abun da ya faru.
Firaiministan Indiya Nerandra Modi, ya kira lamarin a matsayin na tayar da hankali. Babban Ministan jihar Tamil Nadu ya ba da umarnin gudanar da bincike karkashin jagorancin wani tsohon alkali mai ritaya.
Turmutsutsi irin wannan a tarukan siyasa da na addini ya zama kamar wani ruwan dare a Indiya.

Asalin hoton, EPA
Takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa Iran sun sake fara aiki a karon farko cikin shekaru goma.
Sun hada da haramta ayyukan da suka shafi shirinta na nukiliya da makamai masu linzami. Manyan kasashen yammacin duniya na zargin Teheran da gazawa wajen cika alkawurran da suka rataya a wuyanta, ko da yake ta musanta neman mallakar makamin.
Wakilin BBC ya ce cikin wata sanarwa da suka fitar, ministocin harkokin wajen Birtaniya da Faransa da Jamus, sun ce za su ci gaba da bin sabbin hanyoyin diplomasiyya don tabbatar da ganin cewa Iran ba ta mallaki makamin ba.
Tuni dai mutane a kasar suka fara ganin tasirin takunkuman, ta yadda tuni aka fara samun hauhawar farashin kayayyaki da kuma yadda jama'a ke ta rugawa suna sayan kadarori musamman gwal don adanawa saboda kaucewa asara.

Asalin hoton, NRC
Hukumar jirgin ƙasa ta Najeriya NRC ta ce ta kammala gyare-gyare a hanyar dogon Abuja-Kaduna, inda ta ce jirgin zai koma aikin jigilar fasinja a hanyar a mako zuwa.
A ranar 26 ga watan Agusta ne dai jirgin ya tuntsure, inda wasu mutane da dama suka samu raunuka, lamarin da ya sa aka dakatar da aikin jirgin domin a yi gyara.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Callistus Unyimadu ya fitar, ya ce hukumar ta yi aiki tuƙuru wajen tabbatar da kammala gyare-gyaren cikin tsanaki.
"A ƙoƙarinmu na inganta jin daɗi da walwalar fasinja, NRC ta mayar wa fasinja 512 kuɗin tikitin fasinjojin da suke cikin jirgin da ya tuntsure. Sannan muna shirye-shiryen mayar da kuɗin sauran fasinjojin suma domin tabbatar da kowa ya karɓi kuɗinsa."
Sai dai sanarwar ba ta bayyana asalin ranar da jirgin zai koma aiki ba, inda ya ce, "nan da kwanaki kaɗan za mu bayyana asalin ranar da za mu fara jigila, da kuma tsare-tsarenmu."
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Lahadi daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya na labaran kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a cikin Najeriya da sauran sassan duniya.
Ku leƙa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da tafka muhawara.