Tanzania ta soke bikin ranar samun ƴancin kai

Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin ƙasar Tanzaniya ta soke bikin ranar samun ƴancin kai na wata mai zuwa.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin firaminista Mwigulu Nchemba ta ce za a ayi amfani da kuɗin da za a kashe a ranar bikin ne wajen sake gina ababen more rayuwa da suka lalace a tarzomar bayan zaɓen da aka yi a baya-bayan nan.
Sanarwar dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan adawa da sauran ƙungiyoyi ke kira ga jama'a da su hallara a ranar bikin samun ƴancin kai - 9 ga watan Disamba - don gudanar da zanga-zanga game da kashe-kashen da aka yi bayan zaɓen shiugaban ƙasa a watan jiya.
Ƴan adawa sun yi imanin cewa ɗaruruwan mutane ne suka mutu a wannan rikicin.
Har yanzu dai gwamnati ba ta bayar da adadin waɗanda suka mutu ba, sannan ta kafa kwamitin bincike.
Shugaba Samia Suluhu Hassan ta lashe zaɓen da kashi 98 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen wanda ƴan adawa suka bayyana a matsayin "izgili ga dimokraɗiyya".
An dai haramtawa manyan abokan hamayyarta yin takara: Tundu Lissu na tsare ne bisa zargin cin amanar ƙasa, zargin da ya musanta, yayin da aka ƙi amincewa da takarar Luhaga Mpina.
Tuni dai masu sa ido kan zaɓe masu zaman kansu suka bayar da rahoton alamun da ke nuna cewa an yi maguɗin zaɓe tare da cewa zaɓen bai cika ƙa'idojin dimokradiyya ba.

















