Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta yi ƙarin haske kan wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zaumunta wanda ya nuna wani matashi ya tinƙari wajen da shugaba Tinubu yake lokacin da ya kai ziyara jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan jihar, DSP Mansir Hassan ya fitar, ta ce matashin mai suna Umar Mohammed wanda ke zaune a anguwar Muazu, yana da lalurar ƙwaƙwalwa.
"Binciken mu ya gano cewa matashin masoyin shugaba Tinubu ne da kuma gwamna Uba Sani. Saɓanin abin da ya faru - an tantance shi kafin shiga cikin fiin taron a Murtala Square, yana sanye da karamar riga ɗauke da hoton Tinubu da Uba Sani.
"Yana tsaye cikin wajen da aka keɓe wa magoya bayan jam'iyyar APC, sai kwatsam ya shata shingen tsaro sannan ya yi ƙoƙarin kutsawa zuwa wajen da Tinubu yake saboda yana cike da murnar ganinsa," in ji sanarwar ƴansandan.
Sai dai nan take jami'an tsaro suka kama matashin, inda bincike ya gano cewa ba shi da wata manufa illa farin cikin ganin shugaban ƙasa da kuma gwamna Sani.
Sanarwar ƴansandan ta ce an gudanar bincike sosai a kansa, kuma babu wani makami da aka samu a jikinsa.
Don haka kwamishinan ƴansandan jihar, CP Rabiu Muhammad ya gargaɗi al'umma da kuma masu yaɗa labarai marasa tushe da su guji yaɗa karya ko kuma siyasantar da al'amuran tsaro don cimma manufarsu ta siyasa.
Ƴansandan sun kuma ce an jirkita bidiyon matashin da nufin sauya masa ma'ana.
"Muna ci gaba da bincike kan lamarin kuma za mu gayyaci duk waɗanda ke yaɗa labaran karya don yi musu tambayoyi da kuma hukunta su idan muka same su da laifi," in ji sanarwar.