Wannan labari na ƙunshe da bayanan da za su iya tayar da hankali.
Matasa a birnin Kano sun kashe wani matashi da ake zargi da kisan ladanin wani masallaci a birnin Kano, arewa maso yammacin Najeriya.
Bayan kashe matashin, sun kuma ƙona gidan iyalinsa.
Lamarin ya faru ne a unguwar Hotoro, inda bayanai suka tabbatar da cewa matashin ya yi wa ladanin, mai suna Zubairu Kasim, yankar rago ne da asubahin yau Litinin sa'ilin da yake shirin kiran sallar asubahi.
Lokacin da BBC ta isa inda abin ya faru, ta iske ƴan'uwa da sauran al'ummar unguwar na zaman makoki bayan jana'izar ladanin.
A lokacin da ya tattauna da BBC, ɗan mamacin, Isa Kasim, ya ce: “Da asuba ne mahaifina ya fita kiran sallah, inda ya yi kira na farko sai ya zauna yana ɗan lazimi kafin ya yi kira na biyu. Sai kawai wani ya shiga cikin masallacin da makami, ya kama mahaifina ya danne shi ya masa yankan rago, a taƙaice dai ya cire masa maƙogaro.”
Bayan faruwar haka ne wasu daga cikin matasan unguwar suka taru suka hallaka matashin da ya kashe ladanin.
Isa Kasim ya ƙara da cewa: “Allah ya yi shi ma wanda ya kai harin ba zai tsira ba, ƴan unguwa suka yi tara-tara har suka cimma wanda ya kashe shi, inda suka kashe shi, shi ma.”
Ya ƙara da cewa "Bayan da ƴan unguwa suka kashe wanda ya kai harin, sai su ka ga maƙogwaron mahaifina a cikin aljihunsa a leda."
Hukumomi sun tura jami'an tsaro unguwar domin tabbatar da doka da oda bayan ɗan yamutsin da aka samu.