Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/12/2025

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. An yanke wa tsohon madugun ƴan tawayen Congo hukuncin ɗaurin shekaru 30

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a birnin Paris ta yanke wa tsohon madugun 'yan tawayen Congo hukuncin daurin shekaru 30 saboda samun sa da laifin aikata laifukan cin zarafin bil'adama a gabashin jamhuriyar dimukuradiyyar Congo shekaru 20 da suka gabata.

    An samu Roger Lumbala da laifin azabtarwa da fyade a yaƙin Congo na biyu.

    Lumbala ya nemi mafaka a Faransa amma maimakon haka a kama shi.

    Lauyan daya ke kare shi ya ce laifin da ake zargi, an tafka su ne lokaci mai tsawo da kuma ba a Faransa ba. Ya na da kwanaki goma na daujkaka kara.

  2. An kama Chabi Yayi, ɗan tsohon shugaban ƙasar Benin

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga jamhuriyar Benin na cewa an kama Chabi Yayi, dan tsohon shugaban kasar Thomas Boni Yayi a jiya Lahadi, mako guda bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

    Kawo yanzu ba a bayyana dalilin kama shi ba, sai dai ana rade-radin hakan na da nasaba da yunkurin juyin mulkin kasar.

    Jam'iyyar Chabi Yayi ta yi allawadai da kama shi tare da cewa an take masa hakkinsa da kundin tsarin mulki ya bashi na 'yancin dan adam tare da bukatar a gaggauta sako shi.

    Shugaba Patrice Talon dai ya sha alwashin hukunta duk masu hannu a yunkurin juyin mulkin.

    Hukumomi a jamhuriyar Benin sun kama mutane da dama bayan yunkurin juyin mulkin, ciki har da tsohon ministan tsaron kasar Candide Azannai, wanda aka tsare kan zargin shiryawa hukumumi makarkashiya, da tunzura mutane yin tawaye.

    Hukumomin sun kuma aike da sammacin kasa da kasa domin kama dan fafutukar kare muradun 'yan Afurka mai kin jinin kasashen yamma, Stellio Gilles Capo Chichi da aka fi sani da Kemi Seba, kan zargin goyon bayan yunkurin juyin mulkin.

    A ranar da akai yunkurin juyin mulkin dai wasu sojojin jamhuriyar Benin sun karbe ikon gidan talbijin din kasar na wucin gadi, tare da sanar hambarar da mulkin shugaba Patrice Talon, to amma sojojin da ke goyon bayan shugaban da tallafin sojin Najeriya da Faransa suka dakile juyin mulkin.

    Kwanaki biyu bayan hakan Thomas Boni Yayi ya wallafa wani bidiyo a ciki ya na allawadai da yunkurin juyin mulkin na sojin kasar.

  3. Da me Ɗangote ya dogara a zarge-zarge kan Farouk Ahmad na NMPDRA?

    ..

    Asalin hoton, Getty Images/NMDPRA website

    A karo na biyu shugaban rukunin kamfanin Aliko Dangote ya fito fili ya yi zargi shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da kuma sufurin man fetur a Najeriya, NMDPR.

    Attajirin mafi kuɗi a Afirka ya zargi Farouk Ahmed cewa yana biya wa yaransa guda huɗu kuɗin makarantar da ya kai dalar Amurka miliyan 5 a wata sakandire a Switzerland.

    Ɗangote ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya kira a birnin Legas ya ce bai ga ta hanyar da Farouk wanda ma'aikacin gwamnati ne zai iya samun waɗannan kuɗin da har zai biya wa yaransa kuɗin makaranta ba a ƙasar waje.

    "Ya kamata shi Farouk ya zo ya bayar da bahasi dangane da abin da ya yi ya kuma tabbatar bai yi abin da zai jefa ƴan Najeriya cikin ƙangin wahala ba, abin da ka iya zama yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa," in ji Ɗangote.

    " Ya kamata Hukumar Ɗa'ar Ma'aikata ta Najeriya ko kuma duk wata hukuma da ke da ruwa da tsaki kan wannan batu da ta binciki al'amarin. Idan ya ƙi amincewa da zargin to ba wai kawai zan wallafa kuɗin makarantar da yake biya ba, zan kai makarantun kotu domin a matsa musu sao sun bayyana abin da shi Farouk yake biyan su."

  4. Amfani 6 da albasa ke yi a jikin ɗan'adam

    Albasa

    Asalin hoton, John Harper via Getty Images

    Albasa kayan lambu ne da ake amfani da ita wajen girki domin inganta ɗanɗano da ƙamshi. Takan zo da launin ja ko kuma fari.

    Ana iya cin ta ɗanye, ko a soya ko a gasa ko kuma a jefa ta cikin abinci, musamman a cikin miya.

    "Sanadarin sulphur da ke cikin albasa na yaƙi da ƙwayoyin cuta da kuma kumburi a sassan jiki," in ji ƙwararriya kan harkar abinci, A'isha Bala Ahmad, kamar yadda ta shaida wa BBC.

    Ta kuma ce akwai alamun da ke nuna cewa mutanen da ke yawan cin albasa ba su cika kamuwa da cutar daji, wato kansa ba, saboda tana da sinadarai masu tsaftace jiki.

  5. Ana samun nasara a tattaunawar Ukraine da Rasha

    Ukraine Russia

    Asalin hoton, Getty Images

    Jagoran masu shiga tsakani daga ɓangaren Ukraine a tattaunawar sulhu da Amurka, wadda ke gudana a birnin Berlin na Ukraine ya ce an samu ci gaba a yunkurin kawo ƙarshen yaƙi da Rasha.

    Rustem Umerov ya ce ya ce Ukraine na fatan cimma yarjejeniyar da za ta kusanto da zaman lafiya a karshen taron na wannan rana.

    Kwanaki biyu aka kwashe ana tattaunawa tsakanin shugaba Zelensky da tawagar Amurka ƙarƙashin jagorancin Steve Witkoff da kuma surikin Donald Trump, Jared Kushner.

    A gaba zai gana da shugabannin ƙasashen Turai Ukraine da ƙawayenta sun dage sai an baiwa Kyiv tabbataccen tsaro ya yin cimma yarjejeniya.

  6. An kama ɗan daraktan Hollywood bisa zarginsa da hannu a mutuwar iyayensa

    Amurka

    Asalin hoton, Reuters

    Ƴansanda a Los angeles sun ce sun kama tare da tsare ɗan darakatan fina-finan Hollywood Rob Reiner da matarsa Michele da aka tsinci gawarsu.

    An kama ɗansa ɗin mai suna Nick Reiner sannan aka tsare shi bayan bayar da belinsa a kan dala miliyan 2.9, kamar yadda alƙaluman LASD ya nuna.

    An tsinci gawarsu a gidansu da yammacin ranar Lahadi.

    Rob Reiner, wanda ke da shekara 78 ya yi fina-finai da dama da suka hada da 'Standa by me' da 'When Harry met Sally' da sauransu.

    Tsohon shugaban Amurka Barack Obama, ya ce shi da matarsa ​​Michelle suna takaici bayan sun samun labarin mutuwar ma'auratan.

  7. Yankunan Sudan na ci gaba da fuskantar barazana - Hukumar abinci

    Sudan

    Asalin hoton, Mohamed Zakaria/BBC

    Hukumar samar da abinci ta duniya WTF ta yi gargadi ana samun ƙaruwar tashe-tashen hankula a yankin Kordofan da ke Kudancin Sudan inda rikici ya rincaɓe a birnin Kadugli.

    Mataimakin shugaban hukumar samar da abinci ta MDD Carl Skau ya ce a makon da ya gabata, "yayin da muka yi ƙokarin shiga da jerin gwano jirgi maras matuƙi ya kai wa ɗaya daga cikin motocinmu na ɗaukar kaya hari."

    Gwamnatin mulkin soji ta ɗora alhakin harin kan dakarun RSF. Shirin samar da abinci na MDD ya ce baya iya shiga birnin yayin da ake kai wa motocin da ke dauke da kayan abinci hari.

    Hukumar ta Kadugli na dan da rikidewa kamar El Fashir inda mutane ke mutuwa saboda tsananin yunwa.

  8. Maharan Australia na da alaƙa da ƙungiyoyiin jihadi - Albanese

    Aus

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Australia Anthony Albanese ya ce bude wutar da wasu mutane biyu suka yi lokacin bukin Yahudawa a gaɓar kogin Bondi da ke Sydney na da alaƙa da ƙungiyar masu tsattsauran ra'ayi.

    Aƙalla mutum 15 ne suka muta sakamakon buɗe wa ɗaruruwan mutane wuta da wani uba tare da ɗansa suka yi yayin bikin daren farko na Hanukkah.

    An gano, hukumar tattara bayanan Austaralia ta bincike ɗan game da alaƙarsa da ƙungiyar IS.

    Wakilin BBC ya ce tun harin ranar 7 ga watan Oktoba a yaƙin Gaza, makarantu da wuraren ibadar Yahudawa da kuma gidaje ke fuskantar hare-hare yanayin ƙyamar Yahudawa da tayar gobara. Dubban mutane sun halarci bikin cikin dare a gabar kogin Bondi don taya Yahudawa addu'o'i.

  9. An kashe mutum ɗaya tare da sace wasu a wani harin coci a Kogi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum ɗaya aka kashe yayin da aka sace wasu da dama bayan da ƴanbindiga suka kai hari wani coci a jihar Kogi da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, kamar yadda jami’an gwamnati suka bayyana.

    Harin ya faru ne da safiyar Lahadi a reshen cocin Evangelical (ECWA) da ke yankin Aaaaz-Kiri a ƙaramar hukumar Kabba/Bunu.

    Wani jami’in gwamnatin jihar, wanda ya yi magana da BBC amma ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigar sun kutsa cikin cocin ne a lokacin ibada, suka buɓe wuta, sannan suka yi awon gaba da wasu mambobin cocin, ba tare da bayyana adadinsu ba.

    Wadannan hare-hare na baya-bayan nan na kara nuna matsalar rashin tsaro da ke ci gaba da addabar Najeriya, musamman a yankunan arewa da tsakiyar ƙasar, inda ƙungiyoyin ‘yan bindiga ke kai hare-hare da sace-sacen jama’a da farmaki a ƙauyuka da kuma wuraren ibada.

  10. Amurka ta ce an samu ci gaba a tattaunawar tsagaita wuta a Ukraine

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Tattaunawa tsakanin Ukraine da Amurka da nufin cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha na ci gaba a birnin Berlin na Jamus, inda aka shiga rana ta biyu.

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da babban mai shiga tsakani a tattaunawar, Rustem Umerov, sun gana da wakilin Amurka Steve Witkoff da surukin shugaban Amurka Donald Trump, Jared Kushner, na tsawon sa’o’i biyar a ranar Lahadi.

    Taron ya samu halartar Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz.

    Wata sanarwa daga Amurka ta ce, “an samu gagarumin ci gaba” a tattaunawar. Haka kuma, tawagar ta ci gaba da ganawa da safiyar ranar Litinin.

    Kafin fara taron na Litinin, Volodymyr Zelensky ya nuna shirinsa na janye burin Ukraine na shiga ƙungiyar tsaro ta Nato, muddin aka ba ƙasarsa ingantattun tabbacin tsaro.

    Ya ce ganin yadda “wasu abokan hulɗa daga Amurka da Turai” ba sa goyon bayan shigar Ukraine cikin Nato, shi yanzu yana neman tabbacin tsaro mai ƙarfi da zai yi kama da sashe na 5 na yarjejeniyar Nato, wadda ke tanadian kariya ta bai wa juna taimako idan aka kai wa ɗaya hari.

  11. Shugaban Najeriya zai iya dakatar da gwamna - Kotun Ƙoli

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke hukunci cewa shugaban ƙasa na da ikon dakatar da zaɓaɓɓen jami’in gwamnati a lokacin da aka ayyana dokar ta ɓaci a wata jiha.

    Hukuncin ya fito ne a ranar Litinin daga kwamitin alƙalai bakwai, inda alƙalai shida suka amince da matsayar kotun, yayin da alƙali guda ɗaya ya bayar da ra’ayi na daban.

    Karar dai ta fito ne daga gwamnatin jihar Adamawa tare da wasu jihohi guda goma da gwamnoninsu ke ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

    Sun ƙalubalanci matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers a watan Maris na wannan shekara, tare da dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da dukkan ‘yan majalisar jihar na tsawon watanni shida.

    Masu ƙarar sun yi hujjar cewa ƙundin tsarin mulki bai ba wa shugaban ƙasa ikon dakatar da jami’an da aka zaɓa da ke kan mulki ba. Sai dai, a hukuncin da Alƙali Mohammed Idris ya karanta, Kotun ta bayyana cewa Sashe na 305 na ƙundin tsarin mulki ya bai wa Shugaba damar ɗaukar “matakan gaggawa” domin dawo da zaman lafiya da daidaito a duk inda aka ayyana dokar ta ɓaci.

    Kotun ta ce tunda ƙundin tsarin mulkin bai fayyace irin matakan gaggawar da za a ɗauka ba, hakan na bai wa shugaba damar amfani da fahimtarsa wajen yanke hukunci kan matakin da ya dace.

    Duk da haka, alƙali ɗaya daga cikin kwamitin ya yi fatali da wannan matsaya, inda ya ce ko da yake Shugaba na da ikon ayyana dokar ta ɓaci, bai kamata ya yi amfani da ikon wajen dakatar da jami’an da aka zaɓa kuma ke kan mulki kamar gwamna da ‘yan majalisa ba.

    Wannan hukunci ya zo kusan watanni uku bayan an kawo ƙarshen dokar ta ɓaci a jihar Rivers tare da mayar da gwamnan da majalisar jihar kan mukamansu.

  12. ECOWAS za ta canza salo wajen daƙile juyin mulki zuwa amfani da ƙarfin soji

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabannin ƙungiyar bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirk (ECOWAS) sun amince da sauya tsarin martani ga juyin mulki daga saka takunkumai zuwa amfani da ƙarfin soji da kuma hanyoyin diflomasiyya domin daƙile yaɗuwar juyin mulki da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro a yankin.

    An yanke wannan shawara ne a ranar Laraba a Abuja yayin wani babban taron shugabannin ƙungiyar, bayan faruwar juyin mulki a Guinea-Bissau a watan Nuwamba da kuma yunkurin juyin mulki a Benin ranar 7 ga Disamba.

    Juyin mulkin Guinea-Bissau ya zama na tara a yammaci da tsakiyar Afirka cikin shekaru biyar.

    A Benin, sojojn Najeriya ƙarkashin jagorancin ECOWAS sun daƙile yunƙurin juyin mulkin.

    Taron ECOWAS ya amince da tura rundunar soja zuwa Guinea-Bissau domin kare shugabanni da muhimman hukumomin ƙasa.

  13. An kashe matashin da 'ya kashe' ladanin masallaci a Kano

    ...
    Bayanan hoto, Masu zaman makokin kisan da aka yi wa ladani bayan an yi jana'iza

    Wannan labari na ƙunshe da bayanan da za su iya tayar da hankali.

    Matasa a birnin Kano sun kashe wani matashi da ake zargi da kisan ladanin wani masallaci a birnin Kano, arewa maso yammacin Najeriya.

    Bayan kashe matashin, sun kuma ƙona gidan iyalinsa.

    Lamarin ya faru ne a unguwar Hotoro, inda bayanai suka tabbatar da cewa matashin ya yi wa ladanin, mai suna Zubairu Kasim, yankar rago ne da asubahin yau Litinin sa'ilin da yake shirin kiran sallar asubahi.

    Lokacin da BBC ta isa inda abin ya faru, ta iske ƴan'uwa da sauran al'ummar unguwar na zaman makoki bayan jana'izar ladanin.

    A lokacin da ya tattauna da BBC, ɗan mamacin, Isa Kasim, ya ce: “Da asuba ne mahaifina ya fita kiran sallah, inda ya yi kira na farko sai ya zauna yana ɗan lazimi kafin ya yi kira na biyu. Sai kawai wani ya shiga cikin masallacin da makami, ya kama mahaifina ya danne shi ya masa yankan rago, a taƙaice dai ya cire masa maƙogaro.”

    Bayan faruwar haka ne wasu daga cikin matasan unguwar suka taru suka hallaka matashin da ya kashe ladanin.

    Isa Kasim ya ƙara da cewa: “Allah ya yi shi ma wanda ya kai harin ba zai tsira ba, ƴan unguwa suka yi tara-tara har suka cimma wanda ya kashe shi, inda suka kashe shi, shi ma.”

    Ya ƙara da cewa "Bayan da ƴan unguwa suka kashe wanda ya kai harin, sai su ka ga maƙogwaron mahaifina a cikin aljihunsa a leda."

    Hukumomi sun tura jami'an tsaro unguwar domin tabbatar da doka da oda bayan ɗan yamutsin da aka samu.

    ...
  14. Ƴanbindiga sun sace mutum huɗu tare da jikkata uku a Kano

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ’Yanbindiga sun kai hari a ƙauyen Lakwaya da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a Jihar Kano a daren Lahadi da misalin karfe 10 na dare, inda suka sace mutum huɗu tare da jikkata wasu uku.

    Mai unguwar Namandala, Babangida Bello ne ya tabbatar wa BBC da afkuwan lamarin inda ya ce yanbindigar kusan 30 ne suka kutsa ƙauyen.

    Ya bayyana cewa "Cikin mutum huɗu ɗin da ƴanbindigar suka ce, guda biyu samu sun kuɓuce.".

    Ya ƙara da cewa "yanbindigan sun sace garken dabbobi guda hudu daga unguwar."

    Ya kuma ce nan take aka sanar da jami’an tsaro, kuma sun kawo ɗauki cikin gaggawa.

    Wannan hari ƙari ne ga wasu hare-hare da ’yanbindiga suka yi a baya-bayan nan a jihar, waɗanda suka yi sanadiyar asarar rayuka da garkuwa da mutane.

    Rahotanni na nuna cewa, kananan hukumomi akalla uku a arewacin jihar da ke maƙwabta da Jihar Katsina sun fuskanci hare-hare irin wannan.

    Masu sharhi na zargin yanbindigan na fitowa ne daga yankin Katsina.

    Mai unguwan ya yi kira ga gwamnati da ta tura ƙarin jami’an tsaro domin kawo dauki da farfado da tsaro a unguwar.

    Gwamnatin jihar dai ta yi alkawarin ɗaukar duk matakan da suka dace don tabbatar da tsaro da hana ’yan ta’adda samun mafaka a jihar.

  15. Fadar shugaban ƙasa ta musanta zargin amfani da EFCC wajen cin zarafin ’yan adawa

    ...

    Asalin hoton, Tinubu/X

    Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta yi watsi da zargin da wasu ’yan siyasar adawa ke yi na cewa gwamnati na amfani da hukumar EFCC wajen cin zarafin masu adawa da gwamnati.

    Fadar ta kuma musanta zargin cewa dimokuraɗiyya na cikin barazana saboda wasu manyan ’yan siyasa suna sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

    A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar 14 ga Disamba, ya bayyana cewa waɗannan zarge-zargen yunƙuri ne na rikitar da al’umma domin neman riba ta siyasa.

    Sanarwar ta ce wasu ’yan siyasar adawa na yin surutu ne kawai saboda gazawarsu a siyasa.

    Sanarwar ta ce "zargin da ake yi kan yadda manyan ’yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC ba ya da tushe, domin kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ’yan ƙasa ’yancin shiga kowace jam’iyya da suke so ko sauya ra’ayi a duk lokacin da suka ga dama."

    "Babu wanda aka tilasta masa shiga APC, kuma masu sauya sheƙar suna yin hakan ne saboda abin da suka gani a matsayin nasarorin shirye-shiryen gyaran tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu." in ji sanarwar.

    Game da zargin cewa “Gwamnati na amfani da hukumar EFCC amatsayin makami, fadar shugaban ƙasa ta jaddada cewa hukumar na da ’yancin cin gashin kanta bisa doka, kuma tana gudanar da aikinta ba tare da tsoma bakin kowa ba.

    Sanarwar ta ce aikin EFCC shi ne bincike da gurfanar da masu aikata laifukan kuɗi ba tare da la’akari da jam’iyya ko matsayin mutum ba, tare da ƙara da cewa Shugaba Tinubu ba ya ba da umarni kan wanda za a bincika ko a gurfanar.

    Fadar shugaban ƙasa ta kuma yi kira ga ’yan siyasar da ake bincike da su tsaya su kare kansu a gaban doka idan sun san ba su da laifi, maimakon yin zarge-zargen siyasa.

  16. Dangote ya zargi hukumar NMPDRA da zagon ƙasa da cin hanci

    Dangote

    Asalin hoton, X/@AlikoDangote

    Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Nijeriya, NMDPRA ta ƙi cewa komai kan zarginta da ɗaukar wasu matakai da suke daƙile matatun man fetur na cikin gida ta hanyar yi musu zagon ƙasa.

    Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Aliko Dangote ne ya bayyana hakan a wajen wani taron menama labarai, inda a ciki ya zargi hukumar da daƙile ayyukan matatun na cikin gida da hana su rawar gaban hantsi ta hanyar yi musu zagon ƙasa, sannan ya zargi hukumar da shugabanta da cin hanci da rashawa.

    Dangote ya kuma yi zargin cewa kuɗaɗen da shugaban hukumar Farouk Ahmed ke kashewa sun yi yawa, inda ya ce sun fi ƙarfin abin da ma'aikacin gwamnati yake samu, wanda a cewarsa hakan zai janyo rashin yarda da aminci daga ɓangaren ƴan ƙasa.

    BBC ta tuntuɓi kakakin hukumar ta NMDPRA domin jin ta bakinsa kan zargin, amma ya ƙi cewa komai har zuwa lokacin haɗa wannan labarin.

    Dangote ya buƙaci hukumar ɗa'ar ma'aikata ko kuma wasu hukumomin gwamnatin ƙasar da suke da alhakin bincike, "da su bincika wannan batun," in ji shi.

    A baya dai hukumar ta zargi matatar man fetur ta Dangote da yunƙurin rufe kowa ta hanyar yin kaka-gida a ɓangaren harkar man fetur, sannan ta ce man da matatar za ta riƙa fitarwa ba zai wadatar da ƴan Najeriya ba.

    Najeriya wadda ita ce ta fi kowace ƙasa arzikin man fetur a Afirka, ta daɗe tana fitar da man fetur ɗinta a tace zuwa ƙasaashen waje, sai kuma ta shiga da man.

    A ɗaya ɓangaren kuma, matatar Dangote wadda za ta iya tace ganga 650 a kullum, an assasa ta ne domin tacewa da sayar da man fetur a Najeriya a farashin naira.

  17. Kotu a Hong Kong ta samu fitaccen ɗan jarida Jimmy Lai da laifin cin amanar ƙasa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Hong Kong ta gano wani babban dan jarida kuma mai rajin kare dimokradiyya, Jimmy Lai da laifin cin amanar kasa da kuma hada baki da wasu sojojin kasashen waje.

    Mr Lai wanda ɗan asalin ƙasar Birtaniya ne, ya je kotun domin saurarar shari'ar.

    Tuni dai Lai mai kimanin shekaru 78 da haihuwa ya soki hukuncin inda ya bayyana shi a matsayin bita da ƙullin siyasa.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗanadam da kuma ƙasashen yamma sun yi allawadai da hukuncin.

    Lai shi ne fitaccen mutumin da aka fara tuhuma a ƙarƙashin wata dokar tsaron kasa mai cike da ce-ce-ku-ce wadda China ta ɓullo da ita a 2020.

  18. Bello Matawalle ya mayar da martani kan zargin alaƙarsa da ƴanbindiga

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙaramin ministan tsaron Najeria Bello Matawalle da ƙasurgumin ɗan bindigar nan Bello Turji, sun mayar da martani kan ce-ce-ku-cen da ake ci gaba da yi game da zargin ministan da alaka a 'yan bindiga lokacin da yake gwamnan Zamfara.

    Cikin wani faifan bidiyo, Bello Turji ya musanta ikirarin cewa ya karɓi kuɗi daga Bello Matawalle sai dai ya amsa cewa ya taɓa haɗuwa da gwamnan a wancan lokaci a fadar gwamnati yayin tattaunawar zaman lafiya.

    A cikin wata hira da aka yi dashi, Matawalle ya amince cewa an aikawa yan bindiga wasu abubuwa amma a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cimma ne.

    Waɗannan maganganu dai sun tayar da ƙura a Najeriya saboda yadda wasu ke zargin tsohon gwamnan na Zamfara da hannu wajen marawa ƴanbindiga baya amma a tattaunawar da suka yi a kafan yaɗa labarai ta intanet ta DCL Hausa, ya musanta waɗannan zarge-zarge.

    "Shi zargi wanda ba a tabbatar da shi a kotu ba ba zama gaskiya ba, duk wani me zargi na ya je kotu, amma da sharaɗi, idan aka tabbatar da duk abin da ya fadi ba gaskiya bane a kai, toh duk abin da na aza mai na damaiji dole sai ya biya." in ji ƙaramin ministan.

    Matawalle ya ƙara da cewa "Waɗannan kawai zarge-zarge ce na ƴan siyasa saboda su sa min wani baƙin jini saboda suna ganin zan koma nayi takarar gwamna."

    Matawalle ya kuma yi zargin cewa gwamnan Zamfara na yanzu na iya amfani da irin waɗannan zarge-zarge domin samun nasara a siyasa.

    "Ko shi gwamnan da ya gaje ni yana ganin sai yayi haka yake samun nasara, yana ganin sai ya ɓata min suna zai iya komawa gwamna." Matawalle ya ƙara da cewa.

    Toh sai dai, babban mai taimakawa gwamnan jihar Zamfara a kan harkokin yaɗa labarai, Mustapha Jafaru Kaura ya ce zargin da Matawalle ya yi wa gwamna Dauda Lawal ba gaskiya bane.

  19. Za mu inganta ɓangaren shari'a - Zaɓaɓɓen shugaban Chile

    Chile

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Zababben Shugaban Chile Jose Antonio Kast, ya yi alkawarin dawo da martabar shari'a a kasar bayan nasarar da ya samu a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka yi a jiya Lahadi.

    Shugaba Kast ya ce "za mu dawo da martaba da kimar bangaren shari'a a dukkan yankunanmu."

    Shugaban ya samu nasara da kashi 58 cikin dari na kuri'un da aka kada inda ya samu nasara akan abokiyar takararsa Jeannette Jara.

    Chile ta samu shugaban da ya dace wajen farfado da kasar daga yanayin da ta shiga tun bayan kawo karshen mulkin kama karya na janar Pinochet a 1990.

    Mr Kast ya kuma yi alkawarin magance duk wasu muggan laifuka da ake aikatawa a kasar da kuma mayar da dubban 'yanci rani marassa takardu kasashensu.

  20. Harin da ya yi ajalin Yahudawa 15 mugunta ne - Gwamnatin Australia

    Yahudawa

    Firaiministan Australia, Anthony Albanese, ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen kawar da masu nuna kyama ga Yahudawa bayan abin da ya kira harin muguntar da aka kai wajen da Yahudawa ke wani biki a bakin tekun Sydney da ke Bondi.

    Wasu 'yan bindiga biyu ɗa da mahaifi ne suka kai harin wajen bikin Hanukkah inda dubban mutane suka taru. An kashe mutane 15, sannan wasu fiye da 40 sun jikkata inda suke karbar magani a asibiti.

    Daga cikin wadanda suka ji rauni har da Ahmed al Ahmed, wanda aka kira gwarzo saboda kokarin da ya yi na fada da 'yan bindigar har ya kwace bindiga daga hannun daya daga cikinsu.

    An dai kashe daya daga cikin maharan inda gudan kuma ya ji rauni.