Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni dangane da muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 25 ga Disamba 2025.

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. Sojojin Isra'ila sun kashe kwamandan rundunar Quds a Lebanon

    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kashe wani babban mamba a rundunar Quds ta Iran mai karfin fada a ji a Lebanon.

    Sojojin sun bayyana shi da Hussein Mahmoud Marshad al-Jawhari, da suka ce yana da hannu a shirya kai wa Isra'ilawa hari a kasashen Lebanon da Syria.

    Dakarun Quds su ne ke kula da rundunar juyin juya hali na Iran, su na kuma taka muhimmiyar rawa a yankunan Syria da Yemen.

    An dai cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah ta Lebanon a shekarar da ta gabata, amma duk da hakan sojojin Isra'ila na ci gaba da kai wa kungiyar mai samun goyon bayan Iran hare-hare.

  2. Mabiya addinin Kirista suna fargabar hare-haren mabiya Hindu a wuraren bikin Kirsimeti

    Hindu

    Asalin hoton, EPA

    Mabiya addinin Kirista da kungiyoyin kare hakkin dan'adam sun nuna damuwa kan yunkurin masu tsaurin addinin Hindu za su kai hari a wuraren da ake bukukuwan Kirsimati a kasar India.

    Kungiyar mabiya darikar Katolika ta ce hare-haren sun hada da cin zarafin masu wakokin bushara, da majami'u da wuraren da kiristoci ke taruwa.

    Bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna gungun wasu mutane na lalata bishiyoyin Kirismati da akai wa ado a Raipur, da ke jihar Chhattisgarh.

    Wakilin BBC ya ce kungiyoyin mabiya addinin Hindu sun zargi limaman addinin Kirista da kokarin sauyawa mutane addini.

    A bangare guda kuma firai ministan Narenda Modi ya halarci bikin Kirsimati da aka yi a wata babbar coci da ke birnin Delhi, duk da kasancewarsa dan addinin Hindu.

  3. An kama mutum 150 bisa zargin yunƙurin kai hari kan masu bikin kirsimeti a Turkiyya

    Turkiyya

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomi a Turkiyya na tsare da sama da mutum 100 da ake zargi 'yan kungiyar IS ne da ke shirya kai hari a lokacin bukukuwan Kirsimati da sabuwar Shekara.

    Wakilin BBC ya ce ba a yi cikakken bayani kan shirin kai harin ba a birnin Santambul, amma ofishin mai shigar da kara na gwamnati a birnin Santambul, ya ce an samu bayanan sirri da ke nuna harin mabiya addinin Kirista za a kai wa hare-haren.

    Ofishin mai gabatar da karar ya ce 'yan sanda sun kai samame wurare 120 a birnin, inda suka kama mutum 150.

  4. Bai kamata mu manta da mutanen Gaza ba - Fafaroma

    Pop

    Asalin hoton, Reuters

    A sakonsa na bikin Kirsimati na farko a matsayin Limamin mabiya darikar Katolika, Fafaroma Leo ya yi ja hankali kan halin da 'yan gudun hijira da marasa matsugunai ke ciki, ciki har da al'ummar Falasdinu na cikin yanayi a Gaza.

    A lokacin da yake sanya wa mabiya albarka a abin da ake kira da Urbi Et Urbi a dandalin St Peters, Fafaroma Leo ya ce, ''ya ku 'yan uwa maza da mata, Allah yana jarabtar bayinsa ta hanyoyi da dama, amma bai kamata mu manta da al'ummar Gaza da ke rayuwa a tantuna cikin tsananin sanyi da zubar ruwan sama ba.''

    Fafaroma ya yi kira ga duniya a zauna lafiya, da kira ga Rasha da Ukraine su zubda makaman yaki da hawa teburin sulhu.

    Ya kuma yi addu'a ga kasashen Sudan da Kongo, da sassan da ake fama da tashin hankali.

  5. Harin jirgi mara matuƙi ya ƙona tankokin mai biyu a Rasha

    Putin

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Krasnodar da ke kudancin Rasha, sun ce harin jirgi maras matuki ya janyo gobara lokacin da ya fada kan tankokin mai biyu da ke tashar ruwa ta Temryuk.

    Jami'ai sun ce wutar ta yadu a nisan kilomita 2000 amma 'yan kwana kwana sun yi nasarar kashe ta.

    Tashar ruwa ta Temryuk, na kusa da gadar Kerch da ta hada Rasha da yankin Kirimiya da ta mamaye.

    Kawo yanzu Ukraine ba ta ce uffan kan harin ba, sai dai a baya-bayan nan ta na yawan kai hari Rasha lamarin da ake ganin zai janyo cikas a kokarin kawo karshe tsakanin kasashen biyu.

  6. Ladanin masallacin Madina ya rasu

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ladanin Masallacin Annabi da ke Madina ya rasu

    Hukumomi a Saudiyya sun ce Sheikh Faisal Nouman ya rasu a birnin Madina ranar Laraba bayan fama da jinya.

    An naɗa Sheikh Faisal a matsayin ladanin masallacin a shekarar 2002, kuma ya gaji kakansa da mahaifinsa a wannan aiki.

  7. Sabbin yarjejeniya 9 da ASUU ta cimma da gwamnatin Najeriya

    ASUU

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya, ASUU ta ce sun shiga wata sabuwar yarjejeniya da gwamnati, wadda ta ce idan aka ɗabbaƙa, matsalolin da jami'o'in ƙasar suke fuskanta da dama za su kau.

    ASUU ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce waɗannan sababbin matakan da suka aminta, gyara ne kan asalin yarjejeniyar ASUU da gwamnatin ƙasar da aka tsara a 2009, wadda aka daɗe ana taƙaddama a kai.

    Sanarwar ta ce, "bayan shekaru muna tattaunawa da fama da gwagwarmayar da muka sha, ASUU ta shiga wasu sabuwar yarjejeniya da gwamnatin tarayya a ranar 23 ga watan Disamba."

  8. Boko Haram ce ta kai harin ƙunar bakin-wake a masallacin Maiduguri - Rundunar soji

    Soji

    Asalin hoton, HQ Nigerian Army

    Rundunar sojin ƙasan Najeriya ta tabbatar da harin ƙunar bakin-wake da aka kai masallacin Maiduguri, inda ta ce ɗan Boko Haram ne ya kai harin.

    A yammacin jiya Laraba ne ɗan ƙunar bakin-waken ya kai hari a wani masallaci da ke kasuwar Gamborou a cikin garin Maiduguri a daidai lokacin da musulmi suke gudanar da sallar Maghriba.

    A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce, "binciken farko-farko ya tabbatar da cewa ɗan Boko Haram ne ya kai harin na ƙunar bakin-wake, inda ya kashe kansa da mutum biyu a nan take."

    Sanarwar ta ƙara da cewa wasu mutum biyu daga cikin aƙalla 32 da suka jikkata sun rasu a asibiti, sannan akwai wasu guda biyu da ke cikin matsanancin hali.

    A ƙarshe, rundunar ta yi kira ga al'ummar Maiduguri da su kwantar da hankalinu, "sannan su zama masu sa ido tare da nesantar tarukan mutane, sannan su kai ƙarar duk wani abu da ba su gane ba ga jami'an tsaro cikin gaggawa."

  9. Ma'aikatar Shari'ar Amurka ta ce tana buƙatar lokaci kafin sakin takardun Epstein

    Jena-Lisa Jones ɗaya daga cikin ƴan matan da Epstein ya lalata

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar shari'ar Amurka ta ce tana bukatar karin wasu makwanni kafin sakin dukkanin bayanai da suka shafi Jeffrey Epstein wanda ya mutu a gidan yari kan laifukan lalata.

    Sanarwar na zuwa bayan gano wasu takardu masu alaka da shi sama da miliyan daya.

    Tuni hukumar FBI ta mika takardun ga lauyoyi domin yin nazari.

    Tun da farko dai bangaren shari'ar na Amurka ya saɓa wa'adin da yanmajalisa suka bayar na sakin dukkanin bayanan da suka shafi Mr Epstein.

  10. Za mu ci gaba da kare ƴancin addini a Najeriya - Tinubu

    Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ci alwashi ci gaba da tabbatar da ƴanci addini ga dukkanin al'umar ƙasar, inda ya ce ba kamata wani ɗan ƙasar ya fuskanci matsala ba saboda addininsa ko ƙabilarsa.

    Tinubu ya bayyana haka ne a saƙonsa na bikin kirsimeti a ya aike wa ƴan Najeriya, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta ci gaba da yin duk abin da ya kamata domin kare martabar addini da tsaron ƴan ƙasar.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yi fatan alheri ga kiristoci da sauran ƴan ƙasar, sannan ya ce "bayan bikin, ina sake tunatar da kiristoci cewa su yi koyi da halayen ƙwarai na Yesu da ma yin amfani da saƙonsa na zaman lafiya."

    Ya ce tun bayan ɗarewarsa karagar mulki yake ta ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar, "ta hanyar tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya. Duk ƴan Najeriya suna da ƴancin rayuwa da gudanar da ibadarsa da kuma neman abin da suke so."

    Tinubu ya ce babu wani ɗan ƙasar da ya cancanci fuskantar ƙalubale ko barazana saboda addininsa ko ƙabilarsa, "saboda dukkan addinai suna bayyana muhimmancin son Allah da mutunta ɗan'adam. Don haka waɗannan abubuwan da suka haɗa mu ɗin ne ya kamata mu ci gaba da ɗabbaƙawa sama da abubuwan da suka raba mu domin cigaban ƙasarmu."

    Ya ce ya samu damar tattaunawa da jagororin manyan addinai na ƙasar, "tun bayan da aka fara batun muzgunawa wani ɓangare da kuma batun matsalar tsaro, kuma za mu ci gaba da tattaunawa tare da samar da haɗin kai domin daƙile barazanar tsaro da tabbatar da zaman lafiya."

  11. Atiku ya zargi Tinubu da amfani da ƙananan hukumomi domin tilasta wa gwamnoni shiga APC

    ..

    Asalin hoton, Atiku/X

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi kira ga shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta aiwatar da hukuncin kotun ƙoli da ta yanke kan bai wa ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kai.

    A watan Yulin 2024 ne dai kotun ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa gwamnatin jihohi su sakar wa kananan hukumomin ƙasar mara dangane da kuɗaɗensu da yadda za su tafiyar da su.

    A makon da ya gabata ne kuma shugaba Tinubu ya yi wa gwamnonin ƙasar barazanar fara tura wa kananan hukumomin ƙasar kuɗaɗen nasu kai tsaye idan har gwamnonin ba su fara aiwatar da hukuncin kotun ba.

    Wannan ne ya sa tsohon mataimakin shugaban na Najeriya, kuma madugun adawa, Atiku Abubakar, a shafinsa na X ya zargi Tinubu da ƙoƙarin siyasantar da hukuncin kotun ƙolin inda ya ce shugaban ya kamata a zarga dangane da ƙin aiwatar da hukuncin da gangan domin amfani da hukuncin kotun wajen tilasta gwamnoni na jam'iyyun hamayya sauya sheƙa zuwa APC.

  12. Syria ta kama ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar IS

    Shugaban Syria, Ahmad al-Sharaa

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Syria sun ce sun kama ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar IS kusa da Damascus.

    Taha al Zoubi wanda aka fi sani da Abu Omar an kama shi tare da wasu mabiyansa da dama, a cewar wata sanarwa daga ma'aikatar harakokin cikin gida ta Syria.

    An kuma kama makamai a farmakin da aka kai tare da taimakon dakarun kawance da Amurka ke jagoranta.

  13. NLC ta nemi ƴan Najeriya su yi watsi da "dokar harajin da aka yi wa cushe"

    Joe Ajaero

    Asalin hoton, NLC

    Ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta yi kira ga ƴan Najeriya da su yi watsi da "dokar harajin da aka yi wa cushe ko kuma ta ƙarya"

    Shugaban ƙungiyar Joe Ajaero ne ya buƙaci hakan a saƙonsa na Kirsimeti ga ƴan ƙasar, inda ya ce latata dokar babu abin da zai haddasa illa yanke ƙauna ga shugabannni a tsakanin ƴan Najeriya.

    Ajaero ya kuma buƙaci ƴan Najeriyar da su haɗa kansu wajen neman daidaito daga gwamnati inda ya sake nanata buƙatar da ke akwai wajen wayar da kan ma'aikata su yi facali da duk wasu tsare-tsaren gwamnati da ka iya lalata harkokin tattalin arziƙin ƙasa.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin majalisar wakilai mai binciken zarge-zargen cushen ya ce zai gaggauta aikin binciken domin ganin an gano gaskiyar al'amarin domin ɗaukar matakin da ya dace.

  14. Ƙasashe 14 sun yi alawadai da shirin Isra'ila na yin gine-gine a yankin Falasɗinawa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasashen duniya 14 da suka haɗa da Faransa da Birtaniya da Jamus da kuma Japan sun yi alawadai da amincewar da gwamnatin Isra'ila ta yi na gina sabbin matsugunan Yahudawa a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan.

    Sanarwar ƙasashen ta hadin guiwa ta yi kira ga Isra'ila ta janye matakin.

    Ƙasashen sun ce masu cewa ya saɓa wa dokar ƙasa da ƙasa kuma zai ƙara rura wutar rikici da rashin zaman lafiya a yankin.

    Gwamnatin Isra'ila ta ce an amince da matakin ne domin hana samar da kasar Falasdinu.

  15. Tarique Rahman zai koma Bangladesh bayan shekaru 17

    arique Rahman, zai koma ƙasar bayan shafe shekara 17 yana gudun hijira.

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran nan ba da dadewa ba ne magaji ga zuriyar Zia masu tasiri a Bangladesh, Tarique Rahman, zai dawo kasar bayan shafe shekara 17 yana gudun hijira.

    Shi ne shugaban jam'iyyar siyasa mafi girma ta BNP a kasar, kuma dan tsohuwar Firaminista Khaleda Zia.

    Tuni Jam'iyyar BNP ta yi shirin tarbarsa, inda ta ce tana sa ran mutane miliyan biyar za su hallara a Dhaka babban birnin kasar, inda zai yi jawabi ga magoya baya.

    Tarique Rahman zai dawo ne gabanin zaben da za a yi a watan Fabrairu.

  16. Dubban Kiristoci masu yawon buɗe ido sun ziyarci cocin Bethlehem

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban masu ibada da masu yawon bude ido ne suka halarci taron adduo'i a cocin Bethlehem inda aka haifi Yesu Almasihu

    A ranar Laraba ne aka fara gudanar da bikin Kirsimeti a Bethlehem da ke gabar yamma da kogin Jordan da aka mamaye tun bayan da aka fara yakin Gaza.

    Wannan daya daga cikin wadanda suka tafi Bethlehem ne ke cewa ta dauki lokaci tana shirin gudanar da wannan balaguro, kuma wannan kiristimati ta kasance mafi muhimmanci a wajenta.

    Tsohuwar coci ce a Bethlehem da Littafi Mai Tsarki ya ce a nan ne aka haifi Yesu Almasihu.

  17. Ko gwamnatin Najeriya za ta dakatar da sabon haraji bayan zargin cushe?

    ..

    Asalin hoton, Bayo/X

    A yanzu da ya rage saura mako ɗaya kafin sabuwar dokar haraji ta fara aiki a hukumace a Najeriya, kallo ya fara komawa sama ne kan ko aiwatarwar za ta yiwu ko kuma za a dakatar.

    Wannan na zuwa ne bayan muhawarar da ta kaure a ƙasar bayan an yi zargin samun sauye-sauye a dokar daga ƙudurin dokar da aka gabatar a majalisar ƙasar, aka tattauna tare da tafka muhawara kafin amincewa.

    Zargin dai ya haifar da muhawara mai zafi a tsakanin ƴan Najeriya tun bayan da ɗan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Sokoto Abdulsammad Dasuki ya ja hankalin majalisar kan abin da ya bayyana da bambance-bambance da ya ce ya gano a tsakanin ƙudurin dokar haraji da majalisar ta amince da shi, da kuma wanda aka sanya wa hannu ya zama dokar da za a yi amfani da shi.

    A watan Yunin 2025 ɗin ne dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sababbin dokokin haraji huɗu a wani mataki na sauya fasalin tsarin karɓa da tattara haraji na ƙasar.

    Gwamnatin ta ce sabbin dokokin za su sauƙaƙa tsarin, da rage wahalhalun haraji kan ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni, da kuma taimakawa wajen inganta karɓar haraji.

  18. Tambayoyi shida da ya kamata ku san amsarsu dangane da ranar Kirsimeti

    Fafaroma Leo XIV yana ɗaga hannu ga dandazon mabiya a cocin St. Peter's

    Asalin hoton, Getty Images

    Yau ce ranar 25 ga watan Disamba da mabiya addinin Kirista a faɗin duniya ke bukukuwan murnar haihuwar Yesu Almasihu, wanda Kiristoci suka yi amannar cewa shi ne mai ceto.

    A duk lokacin wannan biki, mabiya addinin na Kirista na shagulgulan murna da suka hada da abinci da sanya sabbin sutura da musayar kyautuka da kuma sada juna da salama.

    Albarkacin wannan rana BBC ta zaƙulo wasu muhimman abubuwa dangane da ranar ta Kirsimeti.

  19. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin kai tsaye na BBC Hausa barkan ku da safiyar yau Alhamis wadda ita ranar Kirsimeti da mabiya addinin Kirista ke shagulgulan murnar haihuwar Yesu Almasihu.

    Muna fatan za a yi bukukuwa lafiya sannan mu ga sabuwar shekarar 2026 ita ma lafiya.

    Yau ma kamar kullum mun sake dawo da shafi inda za mu ci gaba da kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da wannan shafi. Mun gode