Sababbin yarjeniyoyi 9 da ASUU ta cimma da gwamnatin Najeriya

ASUU

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya, ASUU ta ce sun shiga wata sabuwar yarjejeniya da gwamnati, wadda ta ce idan aka ɗabbaƙa, matsalolin da jami'o'in ƙasar suke fuskanta da dama za su kau.

ASUU ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce waɗannan sababbin matakan da suka aminta, gyara ne kan asalin yarjejeniyar ASUU da gwamnatin ƙasar da aka tsara a 2009, wadda aka daɗe ana taƙaddama a kai.

Sanarwar ta ce, "bayan shekaru muna tattaunawa da fama da gwagwarmayar da muka sha, ASUU ta shiga wasu sabuwar yarjejeniya da gwamnatin tarayya a ranar 23 ga watan Disamba."

A Najeriya, jami'o'in ƙasar da yajin aiki kamar Ɗanjuma ne da Ɗanjummai, inda ake yawan shiga yajin aiki, lamarin da yake sa ɗaliban da ya kamata su kammala karatu a shekara huɗu, sukan haura shekara biyar a wasu lokutan.

Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna ya ɗaura ne kan gwargwarmayar da ƙungiyar ta daɗe tana yi, musamman a zamanin gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, inda aka samu wata sabuwar ƙungiyar ta malaman jami'a.

Sabuwar yarjejeniya

A sanarwar da ƙungiyar ta fitar, ta ce sun samu maslaha da gwamnatin Najeriya bayan sun shiga wata sabuwar yarjejeniya.

Wasu daga cikin abubuwan da ke ƙunshe a cikin sabuwar yarjejeniyar su ne:

  • Ƙarin albashin kashi 40: Za a ƙara wa malaman jami'a albashi da kasshi 40
  • Ƙarin fansho: Farfesoshi za su riƙa karɓar fanho daidai da albashinu bayan sun yi ritaya a shekara 70.
  • Ƙuɗaɗe ga jami'o'i: Za a ƙara kuɗaɗen da ake ba jami'o'i musamman ƙarin kuɗi domin bincike da ɗakunan karatu da ɗakunan bincike da samun horo.
  • Cibiyar bincike ta ƙasa: Za a assasa cibiyar bincike ta ƙasa mai suna National Research Council wato NRC, wadda za a ware wa aƙalla kashi 1 na kuɗin shiga na cikin gida wato GDP.
  • Sakar wa jami'o'in ƙasar mara: Za a ba jami'o'in damarmakin da suke buƙata wajen gudanar da kansu.
  • Zaɓar shugabannin ɓangarori: Ya zama za su riƙa zaɓar shugabannin sassa da ɓangarori, kuma su kasance farfesoshi ne.
  • Aiki da sabuwar yarjejeniya: Yarjejeniyar za ta fara aiki ne daga 1 ga watan Janairun 2026
  • Duba yarjejeniyar: Haka kuma sun cimma cewa za a riƙa sake duba yarjejeniyar bayan duk shekara uku.
  • Zagon-ƙasa: Ba za a muzguna wa waɗanda suka jagoranci gwagwarmar ba.

Dama dai ASUU ta nace dole gwamnati ta sabunta yarjejeniyar da suka cimma tun 2009, wadda ta shafi yadda ake gudanar da ayyukan jami'o'i da yanayin aiki da kula da koyarwa.

Yarjejeniya ta haɗa da batutuwan zamantakewar ɗalibai da ikon jami'o'i su gudanar da harkokinsu ba tare da tsoma bakin gwamnati ba wato da bai cin gashin kansu ke nan.

A sanarwar da ASUU ta fitar, ta ce matuƙar gwamnati ta fara ɗabbaƙa waɗannan abubuwan da suke cikin yarjejeniyar da suka shiga ba tare da ɓata lokaci ba, za a samu sauƙin matsalolin da ake yawan samu.

"Shugabannin ƙungiyar ASUU na kira ga gwamnatin Najeriya ta aiwatar da waɗannan matakan da aka tsara, sannan muna kira gwamnati ta tattauna da sauran ƙungiyoyin jami'a domin a samun maslaha."