Ministocin a Najeriya: Su wane ne ƙusoshin gwamnatin Tinubu?

Daga: Africa Visual Journalism Team

...

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da ministocinsa a ranar Litinin, kimanin wata uku bayan kama aiki.

Majalisar ministocin mai ƙunshe da mutum 45 na cike da tsofaffin gwamnoni da ƴan majalisar dokoki.

Kimanin rabin ministocin tsofaffin gwamnoni ne da tsofaffin ƴan majalisa.

Majalisar ministocin kuma ta ƙunshi ƙwararru daga ɓangarori da dama, kamar lafiya da fasahar sadarwar zamani.

Shugaban ƙasar ya kuma ci gaba da ministoci biyu daga tsohuwar gwamnatin magabacinsa Muhammadu Buhari, wato Heineken Lokpobiri da Festus Keyamo.

Kamar sauran gwamnatocin baya, ban da ta Goodluck Jonathan, mata ba su samu abin da ya kai kashi 20 cikin ɗari na muƙaman ministocin ba.

Ga bayani game da sabbin jiga-jigan gwamnatin Tinubu da kuma rawar da za su iya takawa.

Ministocin Bola Tinubu

  • Bola Ahmed Tinubu

    Shugaban ƙasa @officialABAT

    An rantsar da Bola Ahmed Tinubu Shugaban Najeriya na 16 a ranar 29 ga watan Mayu

    Ya yi gwamnan Jihar Lagos daga 1999-2007

    Ya taɓa zama sanata daga Lagos kuma ya samu horo a matsayin akanta

  • Kashim Shettima

    Mataimakin Shugaban Ƙasa @KashimSM

    Kashim Shettima shi ne Mataimakin Shugaban Najeriya mai ci

    Tsohon gwamnan Jihar Borno ne kuma tsohon sanata

    Ya yi aiki a ɓangaren banki na tsawon lokaci

  • Mohammed Badaru

    Ministan Tsaro @Badaru_Abubakar

    An naɗa Mohammed Badaru matsayin Ministan Tsaro

    Ya yi gwamna a Jihar Jigawa daga 2015 zuwa 2023

    Shi ne mai Gungun Masana'antun Talamiz, wani babban kamfani da ke da harkoki a ɓangaren motoci da sarrafa kaya da noma da kuma kiwo

    Badaru Abubakar ya kammala Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya inda ya samu digiri a fannin Akanta

  • Dr Bello Matawalle

    Ƙaramin Minista, Tsaro @Belomatawalle1

    An naɗa Bello Matawalle Ƙaramin Ministan Tsaro

    Ya yi gwamna a Jihar Zamfara wa'adi ɗaya

    Yana da horon aikin malanta, kuma ya taɓa zama Ɗan Majalisar Wakilai

  • Olawale Edun

    Ministan Kuɗi kuma Ministan kula da Harkokin Tattalin Arziƙi

    An naɗa Olawale Edun Ministan Kuɗi kuma Ministan kula da Harkokin Tattalin Arziƙi

    Shi ne Mashawarcin Shugaba Bola Tinubu na Musamman kan Manufofin Kuɗi

    Ya taɓa zama Kwamishinan Kuɗi a Jihar Lagos

    Ya yi aiki a Bankin Duniya kan tsare-tsaren tattalin arziƙi da harkoki kuɗi na ƙasashen Caribbean da Latin Amurka.

    Ya haɗa gwiwa wajen kafa Bankin Stanbic IBTC.

  • Atiku Bagudu

    Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi @AABagudu

    An naɗa Atiku Bagudu Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi

    Ya yi gwamna a Jihar Kebbi daga 2015 zuwa 2023 kuma ya taɓa zama sanata.

    Amini ne ga Sani Abacha, marigayi ɗan mulkin kama-karya na Najeriya. An taɓa kama shi a Amurka saboda halasta kuɗin haram, batun da ya cimma sasantawa a kan zaɓin a dawo da shi Najeriya.

  • Tahir Mamman

    Ministan Ilmi @pro_oon

    An naɗa Tahir Mamman, Ministan Ilmi.

    Ya kasance shugaban Jami'ar Baze ta Abuja

    Kuma shi farfesa ne a fannin shari'a kuma lauya mai muƙamin SAN.

    Ya taɓa zama babban darakta a Kwalejin Koyon Aikin Lauya ta Najeriya daga 2005 zuwa 2013.

  • Olubunmi Tunji Ojo

    Ministan Cikin Gida @BTOofficial

    An naɗa Olubunmi Tunji Ojo, Ministan Cikin Gida

    Ya zama ɗan Majalisar Wakilai

    Yana da digiri na biyu a fannin Sadarwar Dijital da Musayar Bayanai daga Jami'ar Lodon Metropolitan

  • Tanko Sununu

    Ƙaramin Minista, Ilmi @sununu4u

    An naɗa Tanko Snunu, Ƙaramin Ministan Ilmi

    Tanko Sununu, ya kasance Ɗan Majalisar Wakilai daga Kebbi

    Ya kasance likitan haihuwa da mata a Cibiyar Lafiya ta Tarayya, Birnin Kudu, inda ya yi aiki tun daga 2012

  • Ali Pate

    Ministan kula da Harkokin Lafiya da Walwalar Jama'a @muhammadpate

    An naɗa Ali Pate Ministan kula da Harkokin Lafiya da Walwalar Jama'a

    Likita ne kuma shi farfesa ne fannin Lafiyar Al'umma a Jami'ar Harvard

    Ya taɓa zama Daraktan Lafiya da Abinci mai Gina Jiki da Yawan Jama'a kuma Daraktan Samar da Kuɗi kan Harkokin Mata da Ƙananan Yara da Masu tasowa a Bankin Duniya

  • Tunji Alausa

    Ƙaramin Minista, Lafiya da Walwalar Jama'a

    An naɗa Tunji Alausa, Ƙaramin Ministan Lafiya da Walwalar Jama'a

    Shi ne ya assasa kuma shugaban Cibiyar kula da Ƙoda da Cibiyar kula da Wankin Ƙoda ta Illinois a Amurka

    Likitan ƙodan na da gogewar aiki ta tsawon shekara 30 a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu

  • Ibrahim Geidam

    Ministan Harkokin Ƴan sanda

    Ana naɗa Ibrahim Geidam, Ministan Harkokin Ƴan sanda

    Ya yi gwamna a Jihar Yobe har karo uku kuma sanata ne daga jihar a wa'adi na biyu

    Ya samu digirinsa ta farko a fannin Akanta kuma shi mamba ne a Cibiyar Ƙwararrun Akantocin Gwamnati ta Najeriya

  • Imaan Suleiman Ibrahim

    Ƙaramar Minista, Harkokin 'Yan sanda @immaculateIman

    An naɗa Imaan Suleiman Ibrahim Ƙaramar Ministar Harkokin Ƴan sanda

    Ta kasance Babbar Daraktar Hukumar hana Fasa-ƙwaurin Ɗan'adam kafin a mayar da ita Kwamishiniyar Tarayya a Hukumar kula da 'Yan Gudun Hijira da 'Yan Ci-rani ta ƙasa

  • David Umahi

    Ministan Ayyuka @realdaveumahi

    Ana naɗa David Umahi Ministan Ayyuka

    Ya kasance sanata daga Jihar Ebonyi, inda ya yi gwamna daga 2015 zuwa 2023

  • Ahmed Ɗangiwa

    Ministan Gidaje da Raya Birane

    An naɗa Ahmed Ɗangiwa, MInistan Gidaje da Raya Birane

    Tsohon Manayan Darakta ne a Bankin Ba da Lamunin Gina Gidaje na Tarayya. Shi masanin zanen gine-gine ne

  • Ahmed Tijjani Gwarzo

    Ƙaramin Minista, Gidaje da Raya Birane

    An naɗa Ahmed Tijjani Gwarzo, Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane.

    Ya taɓa zama Mataimakin Gwamna a Jihar Kano daga 2007-2011

    Tijjani Gwarzo a yanzu haka ƙwararren mai bincike ne a Cibiyar Wits School of Governance a Afirka ta Kudu.

    Ya samu digirinsa ta farko a fannin kimiyya.

  • Alƙali Ahmed

    Ministan Sufuri

    An naɗa Alƙali Ahmed, Ministan Sufuri

    Ya taɓa zama sanata daga Jihar Gombe a tsakanin 2010 da 2023

    Ya samu digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Tattalin Arziƙi

  • Dr Betta Edu

    Ministar Harkokin Jin Ƙai da Yaƙi da Fatara @edu_betta

    An naɗa Dr Betta Edu Ministar Harkokin Jin Ƙai da Yaƙi da Fatara

    Ta kasance Shugabar Mata ta ƙasa a Jam'iyyar APC kuma likita ce

    Ta yi digiri na biyu a fannin kula da Lafiyar Al'umma a Ƙasashe masu Tasowa a Kwalejin Nazarin Tsafta da Likitancin Ƙasashe masu Zafi kuma Likitar kula da Lafiya Al'umma daga Jami'ar Amurka ta Texila

  • Waheed Adebayo Adelabu

    Ministan Lantarki @BayoAdelabu

    An naɗa Waheed Adebayo Adelabu Ministan Lantarki

    Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya ne sashen Aikace-aikace

    Ya yi takarar gwamna ba tare da yin nasara ba a Jihar Oyo a shekara ta 2019. Jami'in akantan ya fara aiki ne da Cibiyar PricewaterhouseCoopers.

  • Abubakar Kyari

    Ministan Noma da Wadata Ƙasa da Abinci @SenAbuKyari

    An naɗa Abubakar Kyari, Ministan Noma da Wadata ƙasa da Abinci

    Ya yi sanata daga daga Jihar Borno a tsakanin 2015 - 2022

    Ya yi digirinsa ta biyu a fannin Gudanar da Harkokin Kasuwanci a Jami'ar Webster a St Louis cikin Missourin Amurka

  • Aliyu Sabi

    Ƙaramin Minista, Noma da Wadata Ƙasa da Abinci

    An naɗa Aliyu Sabi, Ƙaramin Ministan Noma da Wadata Ƙasa da Abinci

    Ya yi sanata tsawon wa'adi biyu daga Jihar Neja a tsakanin 2015 da kuma 2023

  • Joseph Ustev

    Ministan Albarkatun Ruwa da Tsafta

    An naɗa Joseph Ustev, Ministan Albaraktun Ruwa da Tsafta

    Ya yi digiri na uku a fannin Albarkatun Ruwa da Injiniyancin Muhalli

    Ya taɓa zama Darakta a Cibiyar Bunƙasa Sana'o'in Dogaro da Kai a Jami'ar Tarayya ta Noma da ke Makurɗi daga 2013 zuwa 2017

    Ya kuma riƙe muƙamin Kwamishina a Ma'aikatar Albarkatun Ruwa da Muhalli ta Jihar Binuwai

  • Bello Muhammad Goronyo

    Ƙaramin Minista, Albarkatun Ruwa da Tsafta @Barrbmgoronyo

    An naɗa Bello Muhammad Goronyo, Ƙaramin Ministan Albarkatun Ruwa da Tsafta

    Ya taɓa zama Kwamishinan Yaɗa Labarai a Jihar Sokoto

  • Abubakar Momoh

    Ministan Raya Neja Delta @MomohHon

    An naɗa Abubakar Momoh, Ministan Raya Neja Delta

    Shi injiniyan gine-gine ne kuma ya taɓa zama ɗan Majalisar Wakilai har karo biyu

  • John Eno

    Ministan Bunƙasa Wasanni @owan_enoh

    An naɗa John Eno, Ministan Bunƙasa Wasanni

    Ya zama sanata daga Jihar Ribas a tsakanin 2015 da 2019

    Ya kuma yi ɗan Majalisar Wakilai da ɗan Majalisar Dokokin Jiha

  • Adegboyega Oyetola

    Ministan kula da Arziƙin Teku @GboyegaOyetola

    An naɗa Adegboyega Oyetola, Ministan Arziƙin Teku

    Ya zama Gwamnan Jihar Osun daga 2018-2022

    Ya fara aiki a ɓangaren inshora bayan ya kammala Jami'ar Lagos da digiri a kan Inshora cikin 1978

  • Bosun Tijani

    Ministan Sadarwa, Ƙirƙire-ƙirƙire da Arziƙin Dijital @bosuntijani

    An naɗa Bosun Tijani, Ministan Sadarwa, Ƙirƙire-ƙirƙire da Arziƙin Dijital

    Da haɗin gwiwarsa aka kamfanin CcHub

    Ya yi digiri na uku a fannin Tattalin Arziƙin Bunƙasa Ƙasa da Ƙirƙire-ƙirƙire daga Jami'ar Leicester

  • Yusuf Maitama Tuggar

    Ministan Harkokin Waje @YusufTuggar

    Ana naɗa Yusuf Maitama Tuggar, Ministan Harkokin Waje

    Ya taɓa zama ɗan Majalisar Wakilai daga 2007 zuwa 2011

    Ya kasance Jakadan Najeriya a Jamus tun daga 2017

  • Festus Keyamo

    Ministan Sufurin Sama da Bunƙasa Harkokin Samaniya

    An naɗa Festus Keyamo, Ministan Sufurin Sama da Bunƙasa Harkokin Samaniya

    Ya yi Ƙaramin Ministan Raya Neja Delta da Ƙaramin Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin Yi a gwamnatin Buhari

    Shi lauya ne kuma ɗan fafutukar kare haƙƙin ɗan'adam

  • Ishak Salako Salako

    Ƙaramin Minista, Muhalli

    An naɗa Ishak Salako, Ƙaramin Ministan Muhalli

    Shi likita ne kuma tsohon Kwamishinan Lafiya a Jihar Ogun

    Ya kasance Babban Jami'i a Inuwar Masu Ruwa da Tsaki ta Ogun ta Yamma

  • Uche Nnaji

    Ministan Sabunta Ƙere-ƙere, Kimiyya da Fasaha @Nwakaibie4Gov

    An naɗa Uche Nnaji, Ministan Sabunta ƙere-ƙere, Kimiyya da Fasaha

    Shi ɗan kasuwa ne

  • Muhammad Idris

    Ministan Labarai da Wayar da Kai

    An naɗa Muhammad Idris, Ministan Labarai da Wayar da Kai

    Shi ne mawallafin jaridar Blueprint kuma Babban Jami'in Talbijin ta Blueprint

    Yana da digiri na biyu a Ingilishi

  • Dr Doris Nkiruka Uzoka-Anite

    Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari @DrDorisAnite

    An naɗa Dr Dorris Aniche Uzoka, Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari

    Likita amma ta koma harkar banki, ita tsohuwar Kwamishiniyar Kuɗi ce da kula da Harkokin Tattalin Arziƙi a Jihar Imo

  • Shuaibu Abubakar

    Ministan Bunƙasa Ƙarafa

    An naɗa Shuaibu Abubakar, Ministan Bunƙasa Ƙarafa

    Shi Babban Darakta ne a Bankin Stanbic IBTC kuma yana da gogewa a fannin harkar bankin kamfanoni da zuba jari da kula da Kadarori

    Ya samu digirinsa ta biyu a Jami'ar Oxford ta Birtaniya da kuma digirin farko da ƙarin ta biyu a Jami'ar Leicester.

  • Dele Alake

    Ministan Bunƙasa Ma'adanai @AlakeDele

    An naɗa Dele Alake, Ministan Bunƙasa Ma'adanai

    Shi ne Mashawarci na Musamman ga Shugaba Bola Tinubu kan Ayyukan na Musamman da Sadarwa da Tsare-tsare

    Ya taɓa zama Kwamishinan Labarai da Tsare-tsare a Jihar Lagos

    Shi ɗan jarida ne

  • Uba Maigari

    Ƙaramin Ministan Bunƙasa Ƙarafa

    An naɗa Uba Maigari, Ƙaramin Ministan Bunƙasa Ƙarafa

    Shi tsohon Mataimakin Gwamna ne a Jihar Taraba amma an tsige shi a wani yanayi mai cike da taƙaddama bayan zaɓen 2003

    Lauya ne shi

  • Heineken Lokpobiri

    Ƙaramin Ministan Albarkatun Man fetur harkar Mai @DrLokpobiri

    An naɗa Heineken Lokpobiri, Ƙaramin Ministan Albarkatun Man fetur sashen Mai

    Ya kasance sanata karo biyu kafin Shugaba Buhari ya naɗa shi Ƙaramin Ministan Noma da Raya Karkara a 2015.

    undefined

  • Ekperipe Ekpo

    Ƙaramin Ministan Albarkatun Man fetur harkar Gas

    An naɗa Ekperipe Ekpo, Ƙaramin Ministan Albarkatun Man fetur harkar Gas

    Ya taɓ zama ɗan Majalisar Wakilai daga 2007 zuwa 2011

  • Simon Baƙo Lalong

    Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin Yi @LalongBako

    An naɗa Simon Baƙo Lalong, Ministan Ƙwadago da Samar da Aikin Yi

    Ya kasance Gwamnan Jihar Filato har karo biyu

    An zaɓe ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato a 1998 kuma ya zama Shugaban Majalisar a 2000

    Lalong shi ne babban daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu

  • Lola Ade-John

    Ministar Yawon Buɗe Ido

    Lola Ade-John ce Ministar Yawon Buɗe Ido

    Ƙwararriya ce a fannin fasahar sadarwa wadda ta yi aiki a Bankin Access da Bankin UBA da Ecobank da Novateur Business Technology

    Ta karanta fannin Kimiyyar Kwamfyuta a Jami'ar Ibadan

  • Nkeiruka Onyejeocha

    Ƙaramar Minista, Ƙwadago da Aikin Yi @nkeiruka_reps

    An naɗa Nkeiruka Onyejeocha, Ƙaramar Ministar Ƙwadaga da Aikin Yi

    Ta kasance 'yar Majalisar Wakilai daga Jihar Abiya

    Ta taɓa riƙe kantomar Ƙaramar Hukumar Umunneochi a Jihar Abiya

  • Lateef Fagbemi

    Ministan Shari'a kuma Atoni Janar na Tarayya

    An naɗa Lateef Fagbemi, Ministan Shari'a kuma Atoni Janar na Tarayya

    Shi Babban Lauya ne mai lambar SAN wanda ya zama lauya a 1984

  • Uju Kennedy-Ohanenye

    Harkokin Mata @UjuKOhanenye

    An naɗa Uju Kennedy-Ohanenye, Ministar Mata

    Ta kasance 'yar kasuwa da harkoki wajen gina rukunin gidaje da ilmi

  • Nyesom Wike

    Babban Birnin Tarayya @GovWike

    An naɗa Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya

    Ya yi Gwamna a Jihar Ribas daga 2015-2023 kuma shi lauya ne

  • Mairiga Mahmud

    Ƙaramar Ministar Babban Birnin Tarayya

    An naɗa Mairiga Mahmud, Ƙaramar Ministar Babban Birnin Tarayya

    Ta taɓa zama kwamishiniyar Ilmi mai Zurfi a Jihar Kano

    Ta kasance wakiliya a Kwalejin Karatun Likitanci na Gaba da Digiri da Cibiyar Likitoci a Kwalejin Afirka ta Yamma

  • Hannatu Musawa

    Ministar Fasaha, Al'adu da Arziƙin Ƙage-ƙage @hanneymusawa

    An naɗa Hannatu Musawa, Ministar Fasaha, Al'adu da Arziƙin Ƙage-ƙage

    Ta kasance Mashawarciya ta Musamman ga Shugaba Tinubu a kan Al'adu da Nishaɗantarwa

    Ita lauya ce kuma tana karatun digiri na uku

  • Zephaniah Jisalo

    Ministan Ayyuka na Musamman da Hulɗa tsakanin Gwamnatoci

    An naɗa Zephanian Jisalo, Ministan Ayyuka na Musamman da Hulɗa tsakanin Gwamnatoci

    An zaɓe shi har karo biyu ɗan Majalisar Wakilai kuma sau biyu yana zama shugaban Ƙaramar Hukumar Abuja Municipal (AMAC)

    Yana da babbar difloma a fannin nazarin halayyar ɗan'adam da difloma a fannin Shari'ar Manyan Laifuka daga Jami'ar Jos, yana kuma da difloma a fannin Hulɗa da Jama'a daga Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Fasaha

  • Kaduna

    Ministan Muhalli
  • Ministan Matasa

Yawan mata a majalisar ministocin Tinubu

Mata ba su da yawa a cikin gwamnatin Tinubu.

Kamar sauran gwamnatocin da suka gabata, baya ga ta Goodluck Jonathan, yawan ministoci mata ba su kai kashi 20% ba.

Sai dai yawan ministoci mata a gwamnatin Tinubu sun zarta na gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.

...

Wanda ya tsara: Olaniyi Adebimpe; Bincike: Damilola Ojetunde da David Ayoola; Wanda ya zana: Boaz Ochieng; Shugabar aiki: Dorothy Otieno.