Zaɓen Najeriya 2023: Yadda al’ummar Najeriya ke dakon sakamakon zaɓen shugaban ƙasa

..

Asalin hoton, Getty images/BENSON IBEABUCHI

    • Marubuci, Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist

Tun da asubahin ranar Asabar ne al'umma a faɗin ƙasar suka ringa fita rumfunan zaɓe suna shiga layuka domin zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisar tarayya.

Duk da cewa rahotanni daga sassan ƙasar sun nuna cewa an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, to amma an samu tashe-tashen hankula a wasu yankunan, inda aka far wa masu kaɗa ƙuri'a da farfasa akwatunan zaɓen, a wasu wuraren ma an ƙwace na'urar tantance masu kaɗa ƙuri'a (BVAS).

Hakan ya sa an tsawaita lokacin zaɓe a wasu jihohin zuwa ranar Lahadi.

A yanzu al'umma na dakon sakamakon zaɓe.

"Gaskiya na ƙagara na ga sakamako, saboda ina so in ga cewa wanda na zaɓa ya ci, na ƙagara sosai" - in ji wata da ta kaɗa ƙuri'arta a jihar Katsina, da ke arewacin ƙasar.

Bayanai daga jihohi na cewa a yanzu mutane sun dogara ne da kafafen yaɗa labarai domin samun bayanai kan sakamakon zaɓen na 2023.

Sai dai tun a ranar zaɓen ne ake ta wallafa sakamakon na rumfunan zaɓe daban-daban a shafukan sada zumunta.

Sai dai babu kaofofi masu zamansu da suka tabbatar da sahihancin wadannnan sakamakon.

Ƴan gudun hijira da suka kaɗa ƙuri'a

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokawa kan yadda ake amfani da irin waɗannan shafuka wajen yaɗa labaran bogi da na ƙanzon-kurege.

Sai dai duk da haka irin waɗannan labarai na ci gaba da yaɗuwa kamar wutar-daji.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar ce dai ke da ikon bayyana sakamakon zaɓen a hukumance.

A mafi yawan lokuta an fi sanya ido kan sakamakon shugaban ƙasa, inda a wannan karo aka samu manyan ƴan takara huɗu da ake sa ran za su taka rawar gani.

Sai kuma kujerun sanatoci 109 waɗanda aka yi takara, da kuma na ƴan majalisar wakilai 360.

A bayanin da ya yi ranar Asabar, shugaban Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ce za a fara tattarawa da sanar da sakamakon zaɓen ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 12:30 na rana.

Rahotanni dai na cewa an samu fitowar al'umma da dama domin kaɗa ƙuri'a.

...

INEC ta ce masu kaɗa ƙuri'a miliyan 87,209,007 ne suka karɓi katin zaɓensu.

Ƴan takarar shugabancin Najeriya da suka fi shahara

Su wane ne ke takarar shugabancin Najeriya?

Karin bayani kan 'yan takarar shugaban ƙasa na Najeriya

Zaɓi ɗan takara don ganin bayanansa

Bola Tinubu

All Progressives Congress (APC)

  • Shekaru: 70
  • Ya yi karatun akanta a jami'ar Chicago State University.
  • Gwamnan Jihar Legas karo biyu daga 1999 zuwa 2007.
  • Ya wakilci Legas ta Kudu a Majalisar Dattijai daga 1992 zuwa 1993.
  • Gagarumin ɗan siyasa a Najeriya, wannan ne karon farko da yake yin takarar shugaban ƙasa.
  • Adawa da mulkin soja.
  • Ya ninka kuɗin shigar Jihar Legas na shekara-shekara sama da sau huɗu daga biliyan N22.2 a 1999 zuwa biliyan N220.9 a 2007.
  • Ya fara aiki a matsayin mai binciken kuɗi da kuma ma'aji a kamfanin Mobil Producing Nigeria, ɗaya daga cikin kamfanonin man fetur mafiya girma a ƙasar.
  • Inganta harkokin fitar da kaya daga Najeriya zuwa ƙasashen waje da kuma rage dogaro da sayen kaya daga waje.
  • Rage rabin adadi na rashin aikin yi tsakanin matasa cikin shekara huɗu da kuma ƙirƙirar ayyukan yi miliyan ɗaya a ɓangaren sadarwa cikin shekara biyu.
  • Gyara tsarin shari'a don mayar da hankali kan kare afkuwar laifuka da kuma inganta yarda kan jami'an tsaro.

Atiku Abubakar

Peoples Democratic Party (PDP)

  • Shekaru: 76
  • Ya rike mukamin mataimakin shugaban Najeriya daga 1999 - 2007.
  • Ya samu digiri na biyu a ɓangaren alaƙa tsakanin ƙasashe daga jami'ar Anglia Ruskin University da ke Ingila.
  • Tsohon jami'in kwastam ne wanda ya shiga siyasa a farkon shekarun 1980.
  • Sau biyar yana yin takarar shugaban ƙasa ba tare da nasara ba; a 1993, 2007, 2011, 2015, da kuma 2019.
  • Ya kafa jami'ar American University of Nigeria, wadda ta bai wa 'yan matan Chibock tallafin karatu bayan Boko Haram ta sake su.
  • Hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ke da jari a harkokin fetur da noma da bankuna da sashen haɗa magunguna.
  • Ƙudirin sayar da kadarorin gwamnati.
  • Bai wa 'yan kasuwa ƙarin dama wajen haɓaka tattalin arziki.
  • Inganta haɗin kan ƙasa ta hanyar daidaito, da adalci tsakanin ƙabilun Najeriya.
  • Sauya tsarin tafiyar da gwamnati.

Peter Obi

Labour Party (LP)

  • Shekaru: 60
  • Gwamnan Jihar Anambra sau biyu daga 2007 zuwa 2014.
  • Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019.
  • Ɗan kasuwa ne da ya karanta fannin falsafa a Jami'ar Najeriya, Nsukka.
  • Ya kafa wata gidauniya mai kuɗi dala miliyan 156 ƙunshe da kadarori ya zuwa lokacin da ya bar gwamnati.
  • Ya sauya Anambra daga matsayi na 26 zuwa na 1 a jerin jihohin da suka fi cin jarrabawar fita daga sakandare ta NECO da WAEC.
  • Ya mallaki harkokin hada-hada da suka samar da dubban ayyukan yi.
  • Tabbatar da sa ido a aikin gwamnati da kuma yaƙi da rashawa.
  • Mayar da Najeriya ƙasa mai sayarwa maimakon mai saye.
  • Fifita rayuwar ɗan Adam ta hanyar zuba jari a ɓangaren ilimin-komai-da-ruwanka na STEM, da sashen lafiya, da kuma ayyukan raya ƙasa.

Rabiu Kwankwaso

New Nigeria Peoples Party (NNPP)

  • Shekaru: 66
  • Ministan Tsaro daga 2003 zuwa 2007
  • Gwamnan Jihar Kano daga 1999 zuwa 2003, da kuma 2011 zuwa 2015.
  • Ya wakilci Mazaɓar Madobi a Majalisar Wakilai a 1992 da kuma Mazaɓar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019.
  • Yana da digirin digirgir a injiniyanci daga jami'ar Sharda University da ke Indiya.
  • Ba da tallafin karatu da yunƙurin taimaka wa mutane.
  • Ƙara yawan ɗaliban firamare a 2011 daga miliyan ɗaya zuwa miliyan uku a 2015 lokacin da ya bar ofis.
  • Ya ƙaddamar da ciyar da ɗalibai 'yan firamare da ba su kayan makaranta kyauta.
  • Ya kafa Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil da kuma jami'ar Northwest, waɗanda su ne jami'o'in gwamnatin Kano kawai zuwa yanzu.
  • Samar da ayyuka ta hanyar zuba jari a ɓangaren noma.
  • Shawo kan matsalar tsaro.
  • Bin doka da ƙa'idar aiki.

Bola Tinubu (APC)

Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas ne da ke kudu maso yammaci.

Ya yi sanata na wani lokaci a farkon shekarun 1990, wannan ne karon farko da yake takarar shugaban ƙasa a jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC).

Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno ne ke yi masa mataimaki.

Atiku Abubakar (PDP)

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar yana wannan takarar ne a karo na shida.

Ya yi wa'adi biyu a matsayin mataimakin shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.

Gwamnan jihar Delta da ke yankin kudancin Najeriya Ifeanyi Okowa, shi ne ke yi masa mataimaki a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Rabiu Musa Kwankwaso (NNPP)

Rabiu Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano ne. Ya yi gwamna har sau byu, ya yi sanata tsakanin 2015 da 2019.

A baya an naɗa shi, a matsayin ministan tsaro.

Wannan ne karo na uku da yake neman babban ofishin. Takararsa biyu da ya yi a baya duka faduwa ya yi a zaɓen fidda gwani.

Yana takara ne da mataimakinsa Odiri Idahosa a jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Peter Obi (LP)

Tsohon gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabas, Peter Obi shi ne dan takarar shugaban ƙasar jam'iyyar Labour Party (LP).

Wannan ne karo na biyu da yake takara. Karon farko shi ne ya yi wa Atiku Abubakar mataimaki a 2019 karkashin jam'iyyar PDP.

Datti-Baba Ahmad ne yake yi masa mataimaki a takarar.