Ikirarin cewa tsananin talauci ya sa mutane na sayar da yatsunsu a Zimbabwe ya ja hankali a Najeriya

yatsa

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Wani labari marar tushe game da mutanen da ke kokarin yaƙi da talauci a ƙasar Zimbabwe ta hanyar sayar da yatsunsu a kan kudi dala 40,000 ya zama abin ce-ce-ku-ce a Najeriya.

Sashen BBC mai bin diddigi ya bi diddigin labarin da ya samo asali daga shafin intanet na kafar Gambakwe a Zimbabwe.

A labarin da aka wallafa a ranar 28 ga watan Mayun 2022, kafar Gambakwe ta rubuta cewa "wasu da ake zargi ƴan Sangoma ne a Afirka ta Kudu ana zarginsu da bayar da kuɗi mai tsoka ga yatsun matasa marasa aikin yi a Harare."

Sangoma kalma ce ta Zulu da ke nufin masu maganin gargajiya ko kuma masu duba.

Kafar ta yaɗa rahotonta a WhatsApp wanda ya ja hankalin masu amfani da kafofin sada zumunta a Zimbabwe.

Kuma labarin ya bazu zuwa wasu ƙasashen Afirka yayin da ƴan Najeriya da Uganda suka dinga yaɗa labarin a Twitter.

Wani mai amfani da Twitter @joyie7star daga Kamfala a Uganda ya yaɗa labarin ga mabiyansa 6,881. Yana mai cewa tsadar rayuwa ta sa mutane na sayar da yatsunsu kan miliyoyin daloli.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

A Najeriya, @InnocentZikky shi ma ya yada labarin wanda kuma wasu suka yaɗa sau 2,668 a Twitter.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wannan saƙon a Twitter ya yi amfani da wasu hotuna na labarin Gambakwe a saƙonsa na Twitter.

Hotunan ne yawanci mutane suke yaɗawa a shafukan sada zumuna na Intanet domin ci gaba da yaɗa labarin.

Kafar Rediyo ta Kenya 933KFM ita ma ta yaɗa labarin, tare da tambayar mabiya wane ɓangare na jikinsu ne za su iya sayarwa.

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Jaridar Zimbabwe H-Metro ta wallafa hira da ƴan kasuwa a kantin Ximex Mall waɗanda suka ce mutane na zuwa suna tambayar yadda za su ci gajiyar cinikin.

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Wasu daga cikin ƴan kasuwar sun shaida wa H-Metro cewa waɗanda suka tuntuɓe su cewa labarin jita-jita ce kawai.

Sashen BBC da ke yaƙi da labaran ƙarya ya yi nazari kan wasu bidiyo guda biyu waɗanda aka ce sun sayar da yatsunsu ko kuma suna shirin sayarwa.

A bidiyo ɗaya wani mutum ya jirkitar da yatsunsa ya kuma rufe da filasta domin ya nuna cewa an datse masa yatsa.

A ɗaya bidiyon kuma an nuna mutum ana kamar ƙoƙarin cire masa yatsa, amma kuma babu wata alama da ke nuna cewa hanyoyin da aka bi da gaske ne, kamar yadda labarin ke bazuwa a Intanet, musamman ma yadda mutumin da aka datsewa kafa an nuna shi yana dariya a bidiyon.

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 5

Labarin ya yi kama da labarai irin waɗanda suka shafi sayar da sassan jikin mutum da ke jan hankali a sauran sassan Afirka.

Amma, waɗannan labaran wani lokaci suna da sarƙakiya domin wani lokaci ana yarda da su.

A watan Janairun 2022, wasu matasa biyu da kuma abokinsu ɗan shekara 20 an kama su a Najeriya kan zargin kisan wata yarinya domin yin tsafi.

Ɗaya daga cikinsu ya yi iƙirarin cewa wani labarin da aka yaɗa ne a kafofin sada zumunta ya ja hankalinsa.

A Malawi, ana sa ran kotu za ta yanke wa wasu mutum huɗu hukunci a ranar 27 ga Yuni kan kisan wani zabaya a 2018.

Ana alakanta kisan zabaya a Malawi da asiri musamman tunanin samun nasara da kuma arziki.