Emmanuel Macron da Marie Le Pen: Ana yin ta ta kare a zaben shugaban kasar Faransa

Bayan yakin neman zaben da ya janyo rarrabuwar kawuna, 'yan Faransa na yanke hukunci a yau Lahadi kan ko su bai wa Emmanuel Macron mai sassaucin ra'ayi karin shekaru biyar ko kuma su maye gurbinsa da shugabar 'yan adawa ta farko mai matsanancin ra'ayin rikau Marine Le Pen.

Da misalin karfe takwas (06:00 agogon GMT) aka bude rumfunan zabe inda masu kada kuri'a miliyan 48.7 za su zabi wanda zai shugabance su.

Ana sa rai sakamakon fark zai soma fitowa da misalin karfe takwas na dare a agogon kasar.

Domin samun nasara, dukkansu na bukatar jawo hankalin masu kada kuri'a wadanda suka goyi bayan sauran 'yan takara a zaben zagayen farko.

Amma alkaluma sun nuna cewa kawunan masu zabe a rabe suke, kuma babu tabbaci a kan ko wane ne zai yi nasara.

Masu adawa da Mista Macron na kiransa mai girman kai kuma shugaban masu hannu-da-shuni, yayin da ake zargin shugabar masu matsanancin ra'ayin rikau da alaka ta kut-da-kut da shugaban kasar Rasha.

Mista Macron ya hau karagar mulki ne da wata guguwar alƙawarin kawo sauyi amma mutane da dama na korafin ba su gani a kasa ba. Zanga-zanga da cutar korona da kuma hauhawar farashi sun mamaye shugabancinsa.

Ita kuwa Marine Le Pen, ta koyi darasi daga kura-kuran da ta tafka a lokacin da abokin hamayyarta ya yi mata kaca-kaca a zagaye na biyu a shekarar 2017.

Wannan ita ce takararta ta uku ta neman fadar shugaban kasa kuma idan ta gaza zai iya zama na karshe.

Babban abin da ba a sani ba a wannan zaben shi ne adadin masu kada kuri'a da za su ki mara wa ko wanne dan takara baya, ko ta hanyar jefa kuri'a mara kyau ko kuma ba za ta fito kwata-kwata ba.

Yawancin Faransawa suna hutu kuma watakila jama'a kalilan ne za su fito.

Gangamin yakin neman zaben na gajeren lokaci ne amma zabin masu kada kuri'a a fili yake, tsakanin shugaba mai ra'ayin Turai da 'yar takara mai kishin kasa da ke neman hana sanya hijabi da kuma takaita kwakwarar yan ci-rani cikin kasar.

Ko mene ne sakamakon, Mista Macron zai yi jawabi ga masu kada kuri'a a yammacin Lahadi daga wani mataki a karkashin hasumiyar Eiffel.

Bambancin da ke tsakaninsu

Matsananciyar tsadar rayuwa - wadda aka kwatanta a Faransa a matsayin pouvoir d'chatt ko kuma kashe kudi - ta zama batu na daya ga masu jefa kuri'a a kasar kuma Marine Le Pen ta yi wa masu kada kuri'a alkawarin kai dauki cikin gaggawa idan ta yi nasara.

Ta samu karbuwa sosai musamman a kananan garuruwa da yankunan karkara da suka yi fama da matsalar tattalin arziki a zamanin Macron.

Ta zo La Ferté-sous-Jouarre, wani gari a kan kogin Marne makonin biyu da suka gabata. Zaune a wajen mashaya, Cécile ta ce annobar korona ta yi kamari sosai yankin musamman ma: "Kafin korona akwai wata mashaya a nan da ake kira Avenue de Champagne, amma hakan ya sa an rufe kuma yanzu wurin ya mutu."

Ta ce za ta kada wa Marie Le pen kuri'a.

A duk faɗin Faransa Emmanuel Macron ya shahara musamman tare da matasa da tsofaffi masu jefa ƙuri'a, kuma haka lamarin yake a La Ferté ma

Séréna, 'yar shekara 18, ta damu da yakin Ukraine: "Ba mu san ainihin abin da Le Pen ke ji game da Putin ba. Canjin shugaban kasa zai dagula lamarin a yanzu."

Lokacin da Emmanuel Macron ya hau kan karagar mulki, ya kasance bisa alkawarin kawo sauyi. Amma maganar da ka ke ji a ko'ina ita ce, babu abin da ya canja sam.

Idan kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta kasance daidai kuma ya yi nasara, ba zai fuskanci wani wa'adi na biyu cikin sauki ba.