Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sri Lanka: Fannin lafiyar kasar na dab da durkushewa saboda matsin tattalin arziki
- Marubuci, Daga Rajini Vaidyanathan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC South Asia correspondent, Colombo
Likitoci a Sri Lanka sun ce asibitoci na fama da karancin magunguna da sauran kayan aikin a daidai lokacin da kasar ta fada mummunan matsin tattalin arziki. Suna fargabar matukar cewa idan masu ba da agaji ba su kawo musu dauki ba, marasa lafiya za su fada halin rashin tabbas.
"A kowacce rana lamaru na kara dagulewa. Ba mu san halin da za a shiga ba idan muka kai matsayin da babu magani ko kadan," in ji Dr Gnanasekaram cikin tashin hankali.
Sakataren kungiyar kwararrun likitoci a Sri Lanka kuma likitan fida, ya damu matuka kan jerin magungunan da asibitocin birnin Colombo ke bukata, alhalin babu su kwata-kwata a kasar.
"Muna fuskantar karancin magunguna, allurar da ake yi wa marasa lafiya kafin a yi aikin fida ta kare, alluran kashe radadin ciwo, magungunan masu fama da ciwon hakori, kai abubuwan da muke bukata suna da tarin yawa.
"Matukar ba a samu taimako cikin dan tsakanin nan ba, fannin lafiyar kasarmu na gab da durkushewa kasa warwas," in ji shi.
Na hadu da Dr Gnanasekaram lokacin da yake tsaka da duba marasa lafiya, ya ce yana fatan wannan tattaunawar da muka yi da shi za ta zaburar da masu ba da tallafi na kasashen waje su kawo wa kasarsa dauki.
Likitocin sun ce matukar ba a dauki matakin gaggawa ba, za a fuskanci gagarumin kalubale.
"Idan haka ta faru, za a kai matsayin da ba za mu iya ceton rayukan marasa lafiya ba."
Tattalin arzikin Sri Lanka na cikin mawuyacin hali da ba a taba ganin irin shi a tarihi ba. Kasar na shigar da kusan kashi 85 cikin 100 na kayan da suka shafi fannin lafiya. Amma yayin da suke fuskantar karancin kudaden kasar waje, da kyar da sudin goshi suke iya sayen wasu daga cikin magunguna.
Mun ziyarci Dr Wijesuriya a ofishinsa da ke babban asibitin yara a Sri Lanka, ya nuna mana wata zungureriyar takarda da aka rubuta jerin magunguna da kayan aikin asibiti da ake bukata .
A jikin takardar da aka rubuta magungunan, akwai wani dan layi da aka ja na wasu tsirrun magungunan da ake da su.
Abubuwa kamar allurar da ake yi wa marasa lafiya kafin aikin fida, da iskar da suke shaka lokacin aikin, da ta kashe radadin ciwo, da magungunan kashe kwayoyin cuta, da na matsananciyar masassara, wadannan baki daya babu su a yawancin asibitocin kasar.
Shi kuwa maganin rage radadin ciwo za a fuskanci karancinsa nan da makonni biyu masu zuwa, yayin da wasu nau'o'i uku na maganin kashe kwayar cuta suka kare baki daya.
Dr Wijesuriya ya ce yana kokarin shawo kan matsalar karancin magungunan, inda yake amfani da wadanda ake da su a kasa. Yana kuma da kyakkyawan fatan gwamnati za ta yi kokarin ganin an wadata asibitin da magungunann da za a ceto rayuwar marasa lafiya.
Jami'an lafiyar da ke sahun gaba a sibitocin kasar na tsakamai-wuya. Yawanci sun ce gwamnati ta haramta musu magana da 'yan jarida kan halin da fannin lafiyar ke ciki, dole sai an samu jami'i guda da asibiti ya wakilta domin yin magana da mu.
A wata sanarwa da gwamnatin Sri Lanka ta aike wa manema labarai, ta musanta cewa kasar na fama da rashin magunguna da kayan aikin asibiti.
Kwana daya bayan wannan, ma'aikatar yada labaran gwamnati, ta amince akwai karancin maganin amma ba kamar yadda ake zuzutawa ba.
Bayanan da BBC ta gani, da tattaunawa da kungiyoyin likitoci, da bayanan likitocin da ke sahun gaba a fannin lafiya, sun nuna asibitoci a daukacin kasar na cikin halin rashin tabbas da durkushewa saboda rashin kayan aikin.
Ma'aikatan lafiya sun shaida wa BBC cewa rashin kayan aikin ya tilasta musu dai na wasu ayyukan musamman a fannin da ana gaggawa ba.
Dr Nishan (ba sunan shi na gaskiya ba ne) yana aiki a cibiyar masu cutar kansa ko daji da ke gabashin kasar.
"Nan da makonni biyu masu zuwa, ba lallai na ci gaba da yi wa marasa lafiya aiki ba, sai dai wadanda ke cikin mawuyacin hali," in ji shi, a lokacin da muke tattaunawa, ya kuma nuna min jerin kayan da suke bukata, ciki har da allurar jijiya, da sirinjinta, da wadada ake karin ruwa da ita har ma da shi kan shi ruwan.
"Akwai lokacin da dole za mu dakatar da kula da masu fama da cutar-daji."
Yankin da Dr Nishan ya fito, na daga cikin wadanda yakin basasa ya daidaita a Sri Lanka. Akwai tarin kalubale ga likitan da ke aiki a yankin da baya ga yaki tattalin arzikinsu ya durkushe.
"A lokacin da ake yakin, ba ma samun magunguna a kan lokaci, amma duk da haka akwai wadanda ba a rasa ba da ma'aikatar lafiya a Colombo ke aiko mana," in ji shi.
"Amma yanzu hatta ma'aikatar lafiyar ba ta da magungunan. Halin ni-'ya-sun da muke fuskanta a asibitocinmu ya wuce wanda muka fuskanta a lokacin yakin."
Sri Lanka na bin tsarin kiwon lafiya kyauta ga 'yan kasa, da miliyoyinsu da ke tsuburai suka dogara da shi.
Wani ma'aikacin asibiti a kudancin kasar mai suna Kasun (mun sauya sunan shi), ya ce nan da kwanaki kadan masu zuwa magunguna za su kare.
"An shaida mana mu yi taka tsantsan da amfani da abin da muke da shi a kasa, amma babu wani bayani kan yadda za a magance matsalar. Na damu matuka, ban san abin da za mu yi ba."
Babbar kungiyar likitocin tsuburin, da kungiyar likitocin gwamnati sun dora alhakin halin da ake ciki kan rashin kudade da almubazzaranci da dukiyar kasa da matsin tattalin arziki, da rashin masu bada agaji na kasashen waje.
Kungiyar ta lissafa kayan da suke tsananin bukata, ciki har da magungunan kashe radadin ciwo, da na zazzabi da ciwon kai, da maganin hawan jini da na tsananin damuwa da sauransu.
Zauren tattaunawa na likitocin Sri Lanka a fadin duniya a manhajar Whatsapp, sun dukufa wajen lalubo hanyoyin da za su taimakawa kasarsu da magunguna, a daidai wannan lokacin da fannin lafiya ke neman taimako ta kowacce fuska.
Dr Saman Kumara, shi ne shugaban kungiyar likitocin Sri Lanka mazauna kasar waje, ya dauki wani takaitaccen bidiyo da ya yi ta wadari a shafukan sada zumunta, inda ya ke rokon a taimaka wa kasar musamman jaridai sabuwar haihuwa da suke zuwa da lalura, musamman abin karin numfashi.
"Mun kusan kare duk kayan da muke da su na asibiti musamman bututun kara numfashi na jarirai da ba su abinci, kusan nan da makwanni biyu mau zuwa komai za kare," in ji shi. Dr Kumara ya ce ya bai wa ma'aikatan asibiti umarnin su wanke tare da tafasa bututan da aka yi wa jarirai amfani da su na kara numfashi da abinci, da sinadaran kashe cutuka, idan bukatar gaggawa ta taso da za a yi amfani da su.
Bayan wallafa sakon, likitoci a sassa daban-daban na duniya su ka bazama neman wannan abu, da kokarin taimakawa. Ya ce kafin awa 24 an samu tallafin bututun fiye da tsammaninsa.
Sai dai ya na cike da karin damuwa kan sauran kayan da ae bukata, ya na kuma aiki da kungiyar bada agaji da Save A Baby, domin fadada neman taimakon da tabbaar da sun isa kasar akan lokaci.
Dr Anver Hamdani, da aka nada shi ministan lafiya domin ya jagoranci shirin kokarin samar da kayan aiki da magunguna a asibitocin Sri Lanka, ya shaidawa BBC shi da abokan aikinsa na aiki babu dare babu rana domin magance matsalar.
Ya na kuma fatan roko da kiran da suka yi wa gwamnatocin kasashen ketare ciki har da Indiya da ke bin Sri Lanka bashin kudin magunguna da kayan aiki, da kungiyoyin agaji za su taimaka domin shwo kan matsalar kafin komai ya kare musu.
"Mun amince mu na cikin gagarumar matsala, mu na fuskantar kalubale mafi muni, mun amince tabbas akwai matsalar karanci har da rashin abubuwan da fannin lafiyar kasarmu ke fama da shi.
"An gagara shawo kan matsalar, fannin lafiyarmu na gab da durkushewa," ya ce duk da hakan ana bukatar magance matsalar cikin takaitaccen lokaci, da daukar mataki mai inganci domin kaucewa afkuwar hakan nan gaba.
Matsalar da fannin lafiyar na Sri Lanka ke fama da shi, ya janyo karin damuwa da takura ga ma'aikatan lafiya.
Kasun ya ce katsaham an shaikadawa ma'aikatan asibitin da ya ke aiki ba za a biya su alawus din da ake ba su idan sun yi aiki fiye da lokacinsu ba.
Kamar yadda ,iliyoyin 'yan kasar ke fadi tashi, su ma likitocin na cike da matsaloli. Yawancinsu su na daukar lokaci mai tsaho a gidajen mai kafin su samu na zuwa aiki a asibitin.
"Rayuwarmu na cike da kunci da tsauri, ba abiyan albashi kan lokaci, kuma albashin baya biyan bukatun yau da kullum kai lamuran dai ga su nan sai godiyar Allah," in ji shi.
Ya yin da miliyoyin 'yan Sri Lanka suka fantsa tituna don zanga-zanga kan tsdar kayan abinci da man fetur, likitoci da malaman jinya da dalibai 'yan makaranta su ma sun shiga zanga-zanar.
Da muka sake komawa ofishin Dr Gnanaksekaran, ya roki duniya ta taimaka mu su.
"Mu na bukatar magunguna daga kowacce kasa, mu na neman taimakon gwamnatoci, kai har da masu hannu da shuni.
"A matsayina na kwararren likita, na san halin da ake ciki, mun damu kan halin da marasa lafiya ke ciki.
"Abin da kawai muke bukata, shi ne taimaka musu, ba za mu so su mutu ba."