Bazoum Mohamed: Yawan haihuwa ba tare da kulawa ba yana ban takaici

Shugaban Nijar Bazoum Mohamed

Asalin hoton, Gane Mani Hanya: Hira ta musamman da Shugaban Nija

Bayanan hoto, Shugaban na Jamhuriyar Nijar ya bayyana matsalar karancin abinci a matsayin ta biyu mafi muni

Shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya yi gargadin cewa yawan haihuwar 'ya'ya ba tare da kulawa da al'amuran da suka shafi jin dadin ruyuwarsu ba, na haifar da manyan matsaloli a kasar.

Shugaba Bazoum ya shaida wa BBC cewa wannan matsala da sa yanzu haka ake samun yawaitar kananan yaran da ke tafiya yawon barace-barace har zuwa wasu kasashen, wanda abinda ba za a lamunta ba ne.

"Babu abin da ya fi ci min tuwo a kwarya kamar yawan haihuwa da ake yi, za ka ga mutum ya auri mata har zuwa hudu, tare da haihuwar 'yaya masu tarin yawa, bai kula da su ba, har ma suna zuwa wata kasa su yi bara, wannan abin kunya ne da ba za mu yarda da shi ba," in ji shi.

Ya kuma ce galibi iyayen kan bayar da 'ya'yan nasu haya a tafi da su bara wasu kasashen ana aiko musu kudi, inda ya ce hakan ya saba wa addini da kuma 'yancin kananan yaran.

Shugaba Bazoum ya yi tambayar cewa: "Don me ya sa mutum yake ta aure-auren mata da yawa, ya kuma tara 'ya'yan da zai kasa kula da su? Hakan ba daidai ba ne."

Karancin abinci ne matsala ta biyu baya ga ta tsaro

Shugaban na Jamhuriyar Nijar ya bayyana matsalar karancin abinci a matsayin ta biyu mafi muni da ta fi damun talakan kasar baya ga rashin tsaron da ya addabi jama'a.

Ya kuma ce hakan ne ya kara haifar da tsadar kayan abinci a kasuwanni da ya zama dole gwamnati za ta dauki matakan samar wa talaka sassauci.

"Abinci kam tun da ba a noma shi ba, a kasuwa ya yi tsada, maganin irin wannan shi ne a karya farashi a sayarwa da talaka kan rahusa, ko a bayar da su kyauta a inda ya dace," a cewarsa.

Kan hake ne ya yi kira ga kasashen waje da su kawo wa kasarsa agaji, a tallafa wa mutane a fannin abinci.