Yadda kulle-kulle da kashe-kashen siyasa suke ci gaba da barazana ga zabukan Zimbabwe

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Daga Shingai Nyoka
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Harare
Duk da yake jagoran 'yan hamayyar Zimbabwe, Nelson Chamisa, ya kafa sabuwar jam'iyyar siyasa amma yana ci gaba da fuskantar kalubalen da a baya irin su yake fama da su wadanda wasu suka yi fatan ganin an kawo karshensu a 2017 bayan tumbuke tsohon shugaban kasa Robert Mugabe.
Ayayin da ake shirin gudanar da zabukan cike-gurbi ranar Asabar kan kusan kashi 10 na kujerun majalisun dokokin kasar, jam'iyyar the Citizens Coalition for Change party (CCC) ta ce ta fuskanci hare-hare. 'Yan sanda sun hana ta gudanar da wasu tarukan siyasa, sanna sun tarwatsa wasu tarukan yayin da kuma aka tsare magoya bayanta 37, a cewar kakakin jam'iyyar Fadzayi Mahere a hirar sa da BBC. Masu sharhi na ganin hakan a matsayin wani zakaran-gwajin-dafi na abion da zai faru a babban zaben kasar da za a gudanar a shekara mai zuwa.
A wani kauye da ke yankin Gweru, a tsakiyar Zimbabwe, Caiphas Ncube ya binne dansa a farkon watan nan, bayan an kashe shi a wani rikici na siyasa. Wani bayani da 'yan sanda suka rubuta game da kisan wanda kuma kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani ya nuna cewa wasu mambobin jam'iyyar Zanu-PF ne suka kai masa hari.
An soki Mboneni Ncube da mashi a yayuin da yake kan hanyarsa ta zuwa taron gangamin jam'iyyar CCC a Kwekwe, a cewar 'yan sanda. An tuhumi mutum biyar da laifin kisan kai da kuma tayar da zaune-tsaye. Mahaifinsa, wanda tsoho ne da ke tafiya da taimakon kwagiri, ya bukaci masu halartar jana'izar dansa da kada su sanya tufafi masu dauke da alamar jam'iyyun siyasa, inda yake fargabar abin da ka iya faruwa sai dai wasu sun sanya tufafin domin nuna goyon bayan su ga matashin da aka kashe.

"Abu guda kawai nake so yanzu a rayuwata - ina son sanin wanda ya kashe dana. Ina so na kalli idanunsa, na tambaye shi abin da ya yi musu har suka kashe shi," a cewar Mr Ncube a hirar sa da BBC, jim kadan bayan binne dan nasa.
Jam'iyyar Zanu-PF ta musanta hannu a kisan matashin, inda ta dora alhakin hakan a kan rashin jituwar da ake samu a tsakanin 'yan jam'iyyar hamayya.
A cikin kusan shekaru 32 da suka gabata, ana fuskantar zarge-zargen magudi zabe da rikice-rikicen siyasa a zabukan kasar Zimbabwe.
Kwanaki kadan kafin gudanar da zabukan cike-gurbi, wani babban jami'i a jam'iyyar CCC kuma dan takarar majalisar dokoki Tendai Biti ya ce har yanzu ba a ba shi jadawalin masu zaben ba wadanda za su
Kungiyar masu fafutika ta Zimbabwe ta ce an gano rashin daidaito a kundin masu zaben kasar.
Kungiyar ta Team Pachedu ta ce ta gano cewa an sauya mazabu da akwatunan zaben akalla mutum 165,000 zuwa wasu yankunan ba tare da sanar da su ba, lamarin da ya jawo rudani kuma wasu masu zabewn suka yi doguwar tafiya kafin kada kuri'unsu.

Asalin hoton, AFP
"Wane ne ya yi wannan aika-akai kuma mene ne dalilin yin hakan?" in ji Tafadzwa Sambiri, wani babban jami'i a Team Pachedu. "Akwai yiwuwar an yi karin sauye-sauye domin ba mu gama yin nazari kan kundin masu kada kuri'a," a cewar sa a hirar da ya yi da BBC.
Kungiyar ta yi zargin cewa wasu mutane da suke zaune a wurin da ke da adireshi iri daya yanzu sun yi rijista a wani wuri na daban.
Kazalika an cire sunayen mutum 40,000 daga jerin masu kada kuri'a ba tare da bin ka'ida ba.
Hukumar zaben kasar ta musanta zargin cuwa-cuwa tana mai cewa an sabunta kundin masu kada kuri'a.
Zabukan cike-gurbin suna daya daga cikin mafiya girma da za a gudanar a kasar don haka akwai hamayya sosai a kansu. Za a yi zaben ne kan kujeru ashirin da takwas da ke birane kuma wadanda 'yan hamayya ke rike da su, da kuma kujeru fiye da 100 na kananan hukumomi. Za a yi zabe a kan galibin kujerun ne bayan wadanda suke kansu sun sauka sakamakon rabuwar kawuna da ta faru a tsakanin 'yan jam'iyyar hamayya.
Masu sharhi sun yi amannar cewa zabukan za su tabbatar da Nelson Chamisa a matsayin halastaccen shugaban 'yan adawa. A shekarar 2020, an kore shi daga shugabancin babbar jam'iyyar hamayya ta Movement for Democratic Change (MDC), bayan fafutikar neman daunin iko a cikin jam'iyyar.
Duk da cewa ya lashe kashi 44 na kuri'u a zaben shugaban kasa na 2018, amma Kotun Kuli ta ce zaben da aka yi masa bai halatta ba bayan mutuwar shugaban da ya kafa jam'iyyar hamayya Morgan Tsvangirai a farkon shekarar.

Asalin hoton, AFP
Daga nan ne bangarensa na jam'iyyar MDC ya fuskanci kalubale, inda ya rasa kadarorinsa da alamomin jam'iyya da kuma kudin da yake samu daga gwamnati.
Thokozani Khupe, wadda ta zama shugabar 'yan hammaya, ta tuna yadda wasu 'yan majalisar dokoki da kansiloli suka hada baki da Mr Chamisa sannan suka maye gurbin su da mutanenta, ciki har da wadanda suka sha kashi a zabukan 2018.
Hakan ne ya sa a yanzu ake son gudanar da zaben cike-gurbi - dokokin Zimbabwea sun bukaci a gudanar da sabon zabe idan dan majalisa ya sauya shekara ko kuma aka kore shi daga kan mukaminsa.
Wannan ne ya sa Mr Chamisa ya kafa sabuwar jam'iyya.
A yayin da magoya bayan CCC suka zargi jam'iyya mai mulki da amfani da yaudara, babu shakka rarrabuwar kawuna ta kawo cikas a yunkurinta ta cire Zanu-PF, wadda take kan mulki tun shekarar 1980.
Shugaba Emmerson Mnangagwa ya musanta hannu a matsalolin da ake fuskanta a cikin jam'iyyar hamayya.

Asalin hoton, EPA











