Kalubalen da ke gaban jam'iyyar APC gabanin babban taronta

APC

Asalin hoton, APC

Bayanan hoto, Jam'iyyar APC ta fada rikici ne a daidai lokacin da 'yan kasar suke dandana kudarsu game da tsadar rayuwa

A wannan makon ne ake sa ran jam`iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da babban taronta na zabar sabbin shugabanni da za a danka wa ragamar jam`iyyar.

Mutum takwas ne ke takarar shugabancin jam`iyyar, duk kuwa da rahotannin da ke cewa Shugaba Muhammadu Buhari na goyon bayan guda daga cikin su.

Masana dai na cewa babban taron yana da tasiri sosai a kan makomar jam`iyyar APC.

Duk da cewa shugaban riko na jam`iyyar APC, wato gwamnan jihar Yobe, Alhaji Maimala Buni da `yan kwamitinsa na cewa shiri ya yi nisa game da babban taron jam`iyyar na kasa, a bangaren masu neman takara za a iya cewa tana kasa tana dabo ganin cewa mutum takwas ne ke neman shugabancin jam`iyyar.

Bakwai daga cikin su, wato da Mallam Saliu Mustapha da da Mallam Mohammed Etsu da Senata Mohammed Sani Musa da Senata Tanko Al-Makura da Senata George Akume da Senata Abdullahi Adamu duka sun fito ne daga shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya.

Sai na takwas, shi ne tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari daga shiyyar arewa maso yamma.

Ko da yake akwai Senata Ali Modu Shariff, wanda ya ce ya koma gefe saboda rahotanni na cewa akwai wani shiri da ake yi don daidaitawa a bar kujerar ga wani dan takara, kuma a cewarsa shugaba Buhari na goyon bayan shirin maslaha ko daidaitawar.

Sai dai Senata Ali Modu Sharif ya gicciya sharadin cewa idan maganar ta sauya, to fa, yana nan kuma da shi za a yi zawarcin kujerar.

Rahotanni dai na cewa jiga-jigan APC a shiyyar arewa ta tsakiya, musamman ma gwamnoni da kuma Sanatoci daga bangarorin Najeriya daban-daban sun dukufa suna ta tuntuba don cimma maslaha ta yadda za a daidaita a kan mukamin shugaban jam`iyya da sauran mukamai.

Amma wasu rahotannin na cewa ana fuskantar turjiya.

Alal misali, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya ce maganar maslaha ba za ta hana shi jarraba irin nasa farin jinin ba.

Alhaji Ibrahim Dan Malikin Gidan Goga na cikin na hannun daman tsohon gwamnan kuma ya shaida wa BBC cewa "yana cikin wannan takara amma abin da muka sani shi ne an ce an kebe kujerar shugaban kasa ta koma kudu, kujerar shugaban jam'iyya ta dawo arewa.Wata magana a kebewa wani yanki mu duk ba mu san wannan ba".i

Sai dai inda za a fuskanci kalubale shi ne barazanar da bangaren Abdulaziz Yari a kan cewa za su iya ficewa daga jam'iyyar idan ba a yi mu su adalci ba.

Su ma masana kimiyyar siyasa na ganin cewa jam`iyyar APC za ta iya lallaba `ya`yanta su yi babban taro. Sai dai bayan taron ne wasu daga cikin `ya`yan nata za su nuna kalarsu.

Farfesa Husseini Tukur malami ne a jami`ar jihar Nasarawa, kuma ya ce "kowa yana kokari ne ya samu abin da yake bukata, a halin yanzu akwai 'yan takara da dama, akwai wadanda suka fito daga tsakiyyar Najeriya da arewa maso gabas da kuma arewa maso yamma. Wannan yana nuna cewa wajibi ne tunda tsarin mulkinsu bai nuna za a ware mukamin ba, toh a ba kowa dama ya yi takara".

Masanin ya ce a bayanne take cewa jam'iyyar tana cikin rudani saboda akwai bangarori da dama.

Shugabannin jam`iyyar APC dai sukan ce duk jam`iyyar da ta cika ta batse ta gaji hayaniya, ballantana APC mai mulkin kasa kuma suna daukar matakan daidaita kan `ya`yan jam`iyyar ta yadda za su samu mafita ga kowane irin rintsin da za su shiga.