Zamantakewa: Abubuwan da ke jawo mutuwar aure da yadda za a magance su

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na 34 ɗin, shirin ya yi duba ne a kan abubuwan da ke jawo mutuwar aure da yadda za a magance su

Yanzu da za a tambaye ku a ce aure nawa ne kuka sani da suka mutu a cikin shekara daya a unguwarku ko a garinku da watakila sai lissafi ya kufce muku saboda yawansa.

To Hajiya Aisha Ahly kuwa sai da ta shafe shakara uku cur tana bincike da bibiyar aurarrakin da suka mutu a yankinta, da zummar nemo mafita.

Kun san wani abu! Aure sama da 500 ta gano a karan kanta waɗanda suka mutu! Ban da waɗanda ta tattaro bayanansu a kotuna.

Tirkashi? Ku kalli bidiyon shirin na zamantakewa na wannan makon don warware bakin zaren.

Hajiya Aisha Ahly ta fadi abin da ya ja hankalin har ta kai gayin wannan gagarumin bincike na mace-macen aure

Kash, ba ma son mutuwar aure. Yana jawo koma baya a al.'umma, yana naƙasta rayuwar yara ta wajen tasowa ba a gaban duka iyayensu biyu ba, yana mummunan tasiri a kan ci gaban ginuwar al'umma.

Binciken na Hajiya Aisha ya nuna girman matsalar a ƙasar Hausa. Sannan ta fadi manyan abubuwa ne ke jawo yawan mace-macen aure, lamarin da ko ubangiji da KanSa da Ya halatta saki ba ya son a yi shi

A yanzu kusan an fi mayar da hankali kan kashe kudade wajen kawata bukukuwan maimakon mai da hankali wajen neman ilimin zaman auren.

Sannan kuma kai tsaye ba za a iya yin jam'un bai wa wani jinsi laifin jawo yawan mutuwar aure fiye da dayan ba, don idan ɓera da sata to daddawa ma na da wari.

Amma a dukkan tsanani akwai sauki. Haj Aisha ta bijiro da wasu matakai a binciken nata a matsayin mafita ga wannan lamari.

Wasu na baya da za ku so ku gani

Ciki ta ce musamman ma da a ce za a saka dokokin da idan ka yi saki to miji zai dinga warewa matar nan kudaden kula da ciyar da 'ya'yan da ya bar mata, ba wai a bar su kara zube ta yadda za su zame wa al'umma damuwa ba.

Idan kuma ba ka bar ta ta tafi da yaran ba, to hukuma ta sa ido kan yadda kai da sabuwar matarka za ku kula da dawainiyarsu ba tare da barinsu su a hannun duniya ba.

Ta kuma nanata cewa a guji zaben tumun dare.

Sannan kar a manta malama ta yi magnar kishi a can baya, gaskiya mummunan kishi daga dukkan bangarori musamman ta wajen mata yana jawo yawan mace-macen aure, sai mun yi hakuri mun dinga yayyafawa wutar kishinmu ruwan sanyi don a samu maslaha.

Sannan a dinga hukunta duk wacce mummunan kishi ya sa ta aikata wani abu marar daɗi.

Ku kuma maza, sakin nan a hannunku yake, dole sai kun takaita shi kar ku mai da shi kamar cin tuwo, gara a dinga yin sulhu maimakon rabuwar aure. Kuma ya kamata hukuma ta dinga sa ido kan wasu mazan masu zari da yawan auri saki.

A zama daya ba za a iya kawo dukkan hanyoyin warware matsalolin mutuwar aure ba, amma na tabbata idan kowa ya sa hannu a gyran to za a dace.