Yakin Ukraine: Abin da ya sa Putin ba zai iya bai wa mayaƙan Afirka horo ba

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Daga Peter Mwai
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check
- Lokacin karatu: Minti 3
Ana ta yada wani hoton karya mara kala a kafafen sada zumunta da ke nuna shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yana bai wa wasu 'yan Afrika Ta Kudu horo.
Wasu na ta amfani da wannan hoto wajen kafa hujjar da kasashen Afrika za su iya taimakawa Rasha a yakin da take da Ukraine.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Dan Shugaban Uganda Yoweri Museveni shi ma ya wallafa irin wannan hoton a shafinsa na Twitter.
Amma bai nuna shuga Putin ba a Afrika, kuma lokacin da mutane ke cewa an dauki hoton ba daidai ba ne.
Putin bai je Tanzania
An ta yada hotunan a kafafen sada zumunta bayan masu aiki da shafukan sada zumunta a Zimbabwe sun wallafa shi a karshen 2018.
Hotunan sun nuna Mista Putin a sansanin soji a Tanzania, inda ake horar da mayaka da ke nemaarwa kasashen kudancin Afrika 'yanci a 1973.
An kuma nuna shi a hoto, wanda ya nuna shugaban kasar Mozambique Samora Machel da shugaban Zimbabwe na yanzu Emmerson Mnangagwa.
"Putin ya zauna a domin horas da masu rajin samun 'yanci na tsawon shekara hudu daga 1973 zuwa 1977 kamar yadda mawallafa suka ce.

Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma babu wata hujja daga Shugaban Rasha ko Afrika kan cewa Putin da aka haifa a 1952 ya ziyarci Afrika a shekarun 1970.
Bayanan Putin da ke kan shafin fadar shugabanci ta Kremlin sun nuna cewa Putin na karatu a jami'ar Leningard a lokacin, kuma ya kammala karatu ne a 1975.
"Wannan ikirarin nasu kawai shirme ne," in ji Paul Fauvet, wani dan jarida da ya zauna a Mozambique na tsawon gwamman shekaru.
Horon da aka bai wa masu fafutukar neman 'yanci a Mozambique a sansanin sojin Tanzania, ya ce "China ce ta bayar da wannan horo ba Soviet ba".
Kuma Mista Mnangagwa baya Tanzania a 1973 sakamakon kama shi da aka yi a 1965 aka daure shi a gidan yari na tsawon shekara 10 lokacin gwamnatin nuna wariyar launin fata a kudancin Rhodesia a lokacin.

Asalin hoton, Getty Images
Shi Rasha ta aike da masu bayar da horo a Mozambique a shekarun 1980?
Wani marubuci Mozambique ya yi amfani da hotunan a 2018 a littafinsa, inda ya ce ya nuna Mista Machel da kuma wani mai ba da shawara kan harkokin sojin Soviet da ke bayar da horo ga sojoji a kusa da babban birnin kasar Maputo a tsakiyar shekarun 1980.
Amma ya ce a bayyane yake ba mista Putin ba ne a ciki.
Mista Putin yana aiki a matsayin jami'in KGB a gabashin Jamus tsakanin 1985 da 1990 inda yake a matsayin karamin jami'i, wanda ya nuna ba zai iya jagorantar wata tawaga ba.
Kuma babu inda sunansa ya fito cikin jerin wadanda suka je Mozambique da Kremlin ta fitar ko aka ambaci haka cikin tarihinsa.
Jose Milhazes wani dan jarida masanin tarihi, ya ce mutumin da aka gani a jikin hoto shi ma wani babban jami'in Soviet ne da yake aiki a kudancin Afrika.
"Akwai kamanceceniya tsakani, amma zan iya cewa kawai gam da katar aka yi," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Mutumin da ya bayyana a hoton na sanye ne da agogo a hannunsa na hagu yayin da shi kuma Putin yake sa agogonsa a hannun dama.










