Yakin Ukraine: Girman bala'in harba makamin nukiliya a duniya

Nuclear

Barazanar makaman nukiliya da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi a matsayin shirin ko-ta-kwana na ci gaba da jan hankalin duniya a yaƙin da ƙasar ta ƙaddamar a Ukraine.

Tsawon mako guda kenan ana rikicin Ukraine bayan mamayar Rasha, kuma yaƙin na ci gaba da razana duniya saboda barazanar nukiliya.

Bala'in makamin nukiliya babba ne domin yana tattare da hatsari duk da ana amfani da shi wajen samar da makamashi, kamar yadda masanin nukiliya kuma shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Najeriya Farfesa Yusuf Aminu Ahmed ya shaida wa BBC.

A hirar da BBC ta yi da shi, Farfesa Yusuf Aminu ya bayyana tasiri da illolin amfani da makamin nukiliya.

Masanin wanda yana cikin kwamitin mutum 25 na Majalisar Ɗinkin Duniya kan yadda za a rage makaman nukiliya, ya ce harba nukiliya bala'i ne za a haifar a doron ƙasa.

Ba Rasha kawai take da makamin nukiliya ba, amma ita ce ta fi yawan makamin nukiliya a duniya. Ta mallaki makamin nukiliya kusan dubu shida.

Yawan makaman nukiliyar Rasha idan aka kwatanta da na sauran kasashen duniya
Bayanan hoto, Yawan makaman nukiliyar Rasha idan aka kwatanta da na sauran kasashen duniya

An samar da makaman nukiliya iri daban daban kuma idan an zo amfani da su yanayin yakin ne zai tantance yadda za a harba su, kamar yadda Farfesa Yusuf ya bayyana nau'in makaman.

Yadda ake amfani da makaman nukiliya

Ana iya amfani da su ta ƙarkashin ruwa kamar jirgi da ke tafiya kamar kifi a ruwa da za a harba ya fita ya yi ɓarna a duniya.

Akwai kuma nukiliya kamar makami mai linzame da za a iya harba wa ya tafi ya fita wata kasa ya yi ɓarna.

Akwai wadanda ake lodawa a jirgin sama sai an je kan wani gari sai a saki kamar yadda aka kai harin Hiroshima a Japan.

Tasirin harba makamin Nukiliya

Girman harbin makamin nukiliya zai iya shafar ƙasashe da ke kusa da inda aka harba makamin.

Farfesa Yusuf ya ce Rasha tana da makamin da ya lulluƙa girman wanda aka harba a Japan wanda ya lalata yankin gaba ɗaya.

"Tururin makamin da ya shiga iska zai iya kwarara ya shafi kasashe kamar Afirka duk da karfinsa zai ragu kafin ya kawo Afrika."

"Sakin makamin nukiliya babban hatsari ne ga duniya shi ya sa aka kira shi makamin ƙare dangi," in ji shi.

Ya kuma ce ko wane irin makami aka harba yana haifar da illoli kusan iri ɗaya.

Illar makamin nukiliya

Farfesa Yusuf Aminu Ahmed ya bayyana illolin makamin nukiliya ga bil'adama kamar haka:

  • Zai iya ƙona wuraren da ya sauka
  • Zai gurɓata yanayin wurin gaba ɗaya
  • Zai ɓata iskar da ake shaƙa
  • Girgizan da zai haddasa zai lalata abubuwa da yawa
  • Wurin da tokarsa ta sauka za a shafe shekaru wurin na fitar da tururin da zai yi wa mutane illa
  • Tururi zai shiga jikin mutum ya ƙona jijiyoyi ya canza fasalin jinin mutum da yanayin halittarsa idan ya shaƙi iska ko ya taɓa fatan jiki ko ya shiga abincin da aka ci
  • Turunin makamin nukiliya zai iya ɗaukar shekaru yana ci gaba da yin illa da gurɓata muhallin mutane.

Me zai sa Rasha ta iya harba nukiliya?

Kalamai na barazana daga ƙasashen yammacin duniya da ke cewa za su tura wa Ukraine da makamai, shi ya tayar da hankalin Rasha ita ma ta ce sojoji masu kula da makamin nukiliya su kasance cikin ɗamara.

Rasha na duba yiyuwar taron dangin da za a iya yi mata musamman Ingila da Faransa da Amurka duk suna da makaman nukiliya kuma idan suka haɗe makamansu sun fi na Rasha.

Akwai yarjejeniya ta duniya da aka amince a daina ƙirƙiro sabbin makaman nukiliya, waɗanda suke da su kuma ana son su rage waɗanda ba su da shi kuma kada su yi.

"Wasu sun yarda za su rage kuma an fara ragewa," in ji Farfesa Yusuf.

Don haka masanin yana ganin babu wanda ya taba Rasha da makami wanda har zai sa Rasha ta harba nata nukiliya.

Wani dai zai ce, shin yaushe za a kai lokacin da duniya babu makamin nukiliya?