Zaben 2023: Shin sabuwar ƙungiyar siyasar da Kwankwaso ya ƙaddamar za ta iya barazana ga APC da PDP?

Matakin da tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da wasu gaggan 'yan siyasar Najeriya suka dauka na ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar siyasa ya jawo tsokaci daga bangarori da dama game da irin tasirin da hakan zai iya yi a zaben shekarar 2023.
A ranar Talata ne Sanata Kwankwaso ya jagoranci wani gagarumin taro na wasu manyan 'yan siyasar kasar karkashin wata kungiya mai suna The National Movement TNM.
Fitattun mutane da 'ƴan siyasa da suka halarci taron sun haɗa da Alhaji Tanko Yakasai da Capt Idris Wada, tsohon gwamnan Kogi da tsohon sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP Rufai Alkali da Aminu Ibrahim Ringim, tsohon dan takarar gwamna a jihar Jigawa da kuma Inijiniya Buba Galadima.
An gudanar da taron ne a babban dakin taro na International Conference Centre da ke Abuja, babban birnin tarayyar kasar.
A jawabin Kwankwaso, ya ce wasu 'ƴan Najeriya ne da suka damu da abin da ke faruwa a ƙasar suka haɗa kai don ceto ta daga mawuyacin halin da ta shiga.
Ya ce yunƙuri ne na 'ƴan Najeriya masu kishi da suke zaune a gida da kasashen waje.
Sanata Kwankwaso, wanda fitaccen dan siyasa ne da ke jam'iyyar hamayya ta PDP, ya dade yana kokawa kan matsalolin da ke addabar Najeriya da kuma abin da ya kira ''rashin mayar da hankali'' daga bangaren gwamnatin jam'iyyar APC na shawo kansu.
Kazalika, ya sha yin korafi kan wasu matsaloli da ke faruwa a cikin jam'iyyarsa ta PDP, wadanda ya ce shuwagabanninta sun kasa magancewa domin a tsayar da dan takarar da "zai iya kai jam'iyyar ga nasara" a zaben da ke tafe.
Hakan ne ya sa wasu suke ganin tsohon gwamnan na jihar Kano yake jagorantar yunkurin "kawo gyara" a harkokin siyasar Najeriya ta yadda 'yan kasar za su samu ci gaba.
Sai dai wasu na ganin idan ban da shi kansa Sanata Kwankwaso, wanda ke da dandazon magoya baya masu bin akidar kwankwasiyya, babu wani jigo a cikin sabuwar kungiyar siyasar da zai iya tabuka abin a zo a gani a lokutan zabe.

Hasalima wasu na ganin lokaci ya kure da za a samu wata kungiyar siyasa da za ta fafata da APC ko PDP kuma ta yi nasara, ko da yake shi kansa kwankwaso ya bayyana cewa kowanne daga cikin masu ruwa da tsaki a cikin kungiyar yana da tasa jam'iyyar, don haka ba su fita daga cikin jam'iyyunsu ba.
A nasa bangare, tsohon mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Rufai Alkali, ya shaida wa BBC cewa suna iya kwace iko daga jam'iyyar APC ko PDP a zabuka masu zuwa.
"Ai APC ma a shekarun da suka wuce ba a santa a Najeriya ba, a kankanen lokaci da Allah ya sa za su yi tasiri suka fito ana zaginsu ana kushe su ana cewa ba za su yi tasiri ba, amma a idon jama'a suka yi tasiri har suka yi mulkin Najeriya.
PDPn kanta lokacin da ta fito a zamanin mulkin soja, ai ana ganin ana ganin hatsari ne a ce za ka dubi shugaban kasa na soja ka ce za ka kwace mulki a hannunsa; amma PDP ta yi shugabanci. Sai dai yawanci bayan sun samu mulki kowa ya manta mafari, kuma ba a hangen gaba," in ji Farfesa Alkali.
Sai dai masana harkokin siyasa na ganin akwai gagarumin kalubale a gaban kungiyar siyasar idan tana so ta yi tasiri a zaben 2023.
Kabiru Sa'idu Sufi, Malami a fannin koyar da harkokin siyasa na Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a da ke jihar Kano, ya shaida wa BBC cewa sabuwar kungiyar siyasar ta aike da sako mai karfi ga manyan jam'iyyun siyasar kasar.
A cewarsa: "Tagomashin wannan kungiya ya dogara ne ga irin karfin da za ta kara yi nan gaba; kamar yadda muka gani yanzu, tuni wasu manyan 'yan siyasa suka shiga cikinta don haka idan aka samu karin 'yan siyasa suka shiga, za ta samu karin tagomashi da zai sa su yi tasiri."
Ya kara da cewa 'yan siyasa da dama da ke cikin APC da PDP ba sa jin dadin abubuwan da ke faruwa a cikin jam'iyyun, don haka za su iya mayar da hankali kan sabuwar kungiyar siyasar idan al'amura suka ci gaba da dagule musu.
Kawo yanzu dai manyan jam'iyyun na PDP da APC ba su bayyana matsayarsu ko yadda su ke kallon wannan sabuwar kungiya ta TMC a siyasarar Najeriya ba.
"Sannan kada ka manta 'yan siyasa da dama za su iya sauya sheka idan bukatunsu ba su biya ba a lokacin manyan tarukan wadannan manyan jam'iyyu [APC da PDP], don haka za su iya hada gwiwa da wannan sabuwar kungiya domin su yi taron-dangi ko kuma su zama wani ginshiki na uku da sai kowacce daga cikin manyan jam'iyyun ta nemi agajinsu kafin ta kai gaci," a cewar Malam Sufi.











