Gwamnan Abia zai ba da diyyar N2m ga Fulani da naira 150,000 ga shanun da aka kashe

Cattles wey dey Aba new market

Asalin hoton, S bin Abdallah

Gwamnatin Jihar Abiya ta fara biyan diyya ga mutanen da hari da aka kai a sabuwar kasuwar shanu ta Abia ya shafa a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Dr Okezie Victor Ikpeazu na jihar a ranar 20 ga watan Fabrairu ya gana da al'ummar Hausa-Fulani mazauna jihar kan harin.

Sarkin Hausawan Aba Shehu Bello ya shaida wa BBC Pidgin cewa "gwamnan ya fara da yin tir da harin da aka kai kafin ya tabo batun niyan diyyar."

Ya ce: "Abin da gwamnatin ta biya bayan taron na jiya (Lahadi) shi ne diyyar dabbobin da aka kashe, ina ganin kimanin shanu 56 da awaki 50 ne.

"A kan kowacce saniya, gwamnati za ta biya N150,000 kuma za ta biya N50,000 kan kowace akuya, kuma gwamnan ya yi alkawarin bayar da naira miliyan biyu na diyya ga kowane ran mutum daya da aka kashe kuma ranar Alhamis za mu karbo kudin," inji shi.

Pipo gada for di meeting on Sunday

Asalin hoton, Abia state goment

Bayanan hoto, Jama'a sun taru a wurin taron da aka yi ranar Lahadi

Shugaban al'ummar Hausawan ya kuma taɓo batun binne mutum takwas, wanda aka yi ranar Juma'a, inda ya ce mutum daya ne ya rage a dakin ajiyar gawa a wannan lokacin.

"Lallai mun binne dukkan mutanenmu, sai mutum daya da ya fito daga Jihar Filato."

Ya kuma yi magana kan bacewar wasu mutum biyu da har yau ba a san inda suka shiga ba.

"Tun bayan da lamarin ya auku, babu wanda ya iya yin barci cikin shugabannin al'umarmu saboda irin harin da aka kai da kokarin da muke yi na tabbatar da an yi mu su adalci. Har yau din nan akwai wasu mutum biyu da suka bace da ba mu san inda suke ba."

Muhammad Sulaiman

Asalin hoton, S bin Abdallah

Bayanan hoto, Muhammad Sulaiman na cikin mutanen da suka tsira da ransu bayan harin na Talata

'Yadda muka tsira da rayukanmu a daren da aka kai harin'

"Na yi sa'ar tsira da raina domin yawancin wadanda suka mutun sun fara barci."

Wadannan kalaman Muhamad Sulaiman ke nan, daya daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu a harin na Talata 15 ga watan Fabrairun wannan shekarar a kasuwar Shanu ta Aba.

Muhammad ya ce saboda shi da wasu abokan zamansa ba su yi barci ba shi ya sa suka tsira da rayukansu.

"Can kusan 12 na dare muna hira da wasu sai muka ji harbin bindiga, kuma mun ji wasu na cewa 'ku rike shi, ku rike shi'.

Rahotannin da BBC Pidgin ta samu na cewa wasu 'yan bindiga ne suka kai hari a sabuwar kasuwar Shanun a Omuma-Uzo da ke Ƙaramar Hukumar Ukwa West ta jihar.