Yadda mahaukaciyar guguwa tafe da ruwa ta share kauyuka a Madagascar

Akalla mutum goma ne suka mutu kusan 50,000 kuma suka rasa muhallansu bayan da wata mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwa mai suna Batsirai ta ratsa kasar Madagascar ranar Asabar da yamma.

Batsirai wadda ta kasance irin wannan mahaukaciyar guguwa ta biyu da ta fada wa kasar a cikin mako biyu, ta sauka ne a gabar gabashin tekun kasar inda take gudun kilomita 235 a cikin sa'a daya ta kuma haddasa torokon teku.

Rahotanni sun ce kusan dukkanin kauyukan da ke bakin gabar ruwan ta lalata su gaba daya.

Yanzu dai guguwar ta yi sauki in ji hukumar kula da yanayin kasar.

Daman Madagascar tana kokarin farfadowa ne daga wata mahaukaciyar guguwar mai suna Ana da ta afka wa kasar wadda tsibiri ce a tekun India, inda ta hallaka mutum 55 a watan da ya wuce.

Wannan mahaukaciyar guguwa Batsirai ta kara girman barnar, bayan da ta fada a birnin Mananjary wanda ke kudu maso gabashin kasar, da nisan kilomita 530 daga babban birnin kasar Antananarivo, da kusan karfe takwas na dare agogon kasar (17:00 GMT) ranar Asabar.

Wutar lantarki ta katse a Mananjary tsawon kawana biyu haka ruwan famfo ma an samu tankarda da shi, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

Wani mazaunin birnin ya sheda wa Reuters cewa hatta makarantu da coci-coci da aka tsara cewa za a yi amfani da su a matsayin cibiyoyin tsugunar da wadanda guguwar ta raba da muhallansu, rufinsu ya yaye.

A wasu wuraren kamar birnin Nosy Varika barnar ta yi tsanani inda kusan kashi 95 cikin dari na birnin ya lalace.

Ministan muhalli Vahinala Raharinirina ya gaya wa BBC cewa guguwa da ruwan kusan sun shafe kauyuka da dama.

Can a birnin Mahanoro, da ke gabar gabashi, ruwan teku ya yi toroko har ya wanke wata jigawa wadda bangare ce ta wata makabarta.

Marie Viviane Rasoanandrasana, wata mata mai shekara 54, wadda mijinta ya rasu ta zauna tana kallon yadda ruwa ya ci kabarin mijinta da sirikinta da kuma 'yarta, ana ganin gawarwakinsu.

Hukumar bayar da taimakon gaggawa ta kasar ta ce kusan mutane dubu 48 guguwa da ruwan suka raba da muhallansu.

Hukumar shirin samar da abinci na majalisar dinkin duniya ta yi kiyasin cewa kusan mutum dubu 150 ne bala'in zai sa su bar gidajensu.

Tuni daman aka tsugunar da wasu a inda aka ajiye wadanda mahaukaciyar guguwar Ana ta yi wa barna.

Duk da cewa karfin mahaukaciyar guguwar mai tafe da ruwa ya ragu yayin da take kutsawa cikin kasar inda take gudun kilomita 110, hukumar kula da yanayin kasar ta ce guguwar za ta yi illa sosai.

Kwararru na fargabar cewa guguwar ta Batsirai za ta iya yin illa fiye da Ana, wadda ita ma ta fada wa Mozambique da Malawi da kuma Zimbabwe, kuma tuni jami'ai na kira ga hukumomi da kasashen duniya da su kai musu dauki.

Hukumar shirin samar da abinci ta majalisar dinkin duniya tuni ta fara tsara taimakon abinci da za ta kai wa mabukata, yayin da tuni kuma an kwashe wasu mutanen.

Ita ma majalisar dinkin duniya tuni ta samar da jirgin sama da zai je inda aka samu barnar.

Ana dai sa ran mahaukaciyar guguwar ba za ta nufi doron nahiyar Afirka ba.

Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya ta ce yanayin yadda ake samun mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwa a yanzu sakamakon dumama da sauyin yanayi, abin ya sa damuna ba ta albarka, kayayyakin abinci sun yi tsada da kuma karuwar barazanar karancin abinci a yankin.

Al'ummar kudancin Afirka su ne matsalar sauyin yanayi ta fi addaba, tsawon shekaru, kuma a duk shekara matsalar na mayar musu da aiki baya in ji wata babbar jami'iar majalisar dinkin duniya, Margaret Malu.

Kwararru sun ce za a rika ganin matsalar tsananin sauyin yanayi kamar, irin mahaukaciyar guguwar da ake gani a yanzu sosai.

Madagascar ta samu kanta a cikin wannan mummunan yanayi ne bayan da take farfadowa daga illar fari wadda ita ma sauyin yanayi ya haifar.

Ministan muhalli ya gaya wa BBC cewa kasar ta mika wa babban taro na duniya kan sauyin yanayi, shirinta da ya nuna tana bukatar dala biliyan daya (fan miliyan 740) a duk shekara domin jure wa illar sauyin yanayi.