Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dakarun Amurka sun 'kashe shugaban kungiyar IS' a harin da suka kai Syria
Wasu dakarun Amurka na musamman sun kai hari a arewa maso yammacin Syria inda suka kashe shugaban kungiyar Islamic State (IS) da ke ikirarin jihar,a cewar shugaba Joe Biden.
"Muna godiya bisa basira da kwazon sojojimu, mun kawar da Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi," a cewar sanarwar da ya fitar.
Wani babban jami'in kasar Amurka ya shaida wa kafafen watsa labarann kasar cewa Qurayshi ya tayar da bam din da ke jikinsa inda ya kashe kansa da iyalansa.
Wasu 'yan Syria da suka soma zuwa wurin da lamarin ya faru sun ce sun ga gawarwaki 13 bayan harin.
Jiragen helikwafta da dama na Amurka sun sauka a wajen garin Atmeh da ke hannun 'yan tawaye, wanda yake lardin Idlib na arewacin kasar da ke kusa da kan iyakar kasar da Turkiyyas, da kusan tsakar daren Alhamis a agogon kasar.
Majiyoyi sun ce dakarun sun fuskanci turjiya sosai kuma an bude musu wuta da manyan bindigogi da aka girke a kan motoci.
An ji karar musayar wuta da kuma harba makamai tsawon awa biyu kafin jiragen masu saukar ungulu su bar wurin.
Jaridar New York Times ta rawaito cewa an bar wani jirgi mai saukar ungulu da ya lalace, amma daga bisani sojojin Amurka suka lalata shi . An sanya hotunan jirgin a shafukan intanet.
Shugaba Biden ya ce dukkan Amurkawan da suke da hannu wajen kai harin sun koma gida ba tare da ko kwarzane ba, wwanda ya ce an kai shi ne domin "kare Amurkawa da kawayenmu, sannan a raba duniya da miyagun mutane".
Wakilin kamfanin dillancin labaran AFP wanda ya ziyarci gidan da aka kai wa harin ya ce wurin ya yi kama da filin yaki - jini ya warwatsu a jikin bango, an yi kaca-kaca da tagogi, an lalata rufin gidan wanda ya rufta.
Rundunar tsaro ta Syria Civil Defence, mai suna White Helmets, ta fitar da sanarwar da ke cewa jami'anta da suka soma isa wurin da misalin karfe 03:15 kuma suka gano gawar mutum 13, ciki har da na kananan yara shida da mata hudu.
Sun kuma gano wata yarinya da aka jikkata wadda aka kashe iyayenta, a cewar rundunar. An dauke ta zuwa asibiti tare da wani mutum da aka jikkata lokacin da yake tsaye kusa da ginin yayin da aka yi ba-ta-kashin, in ji rundunar.
Wani babban jami'in gwamnatin Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "A farkon lokacin da aka kai harin dasn ta'addar ya tayar da bama-baman da suka kashe shi da iyalansa, ciki har da mata da kananan yara."
Shi ma Abu Bakr al-Baghdadi, wanda Qurayshi ya gada, ya kashe kansa tare da kananan yara uku a watan Oktoban 2019 ta hanyar tayar da rigar bam din da ke jikinsa lokacin da dakarun Amurka suka kai hari a maboyarsa da ke da nisan kilomita 16km daga Atmeh.