Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Facebook: Masu amfani da shafin a kullum sun ragu karon farko cikin shekara 18
Katafaren shafin sada zumunta da muhawara Facebook, ya samu raguwar masu amfani da shi a kullum (DAUs) karon farko a tarihinsa na shekara 18 da kafuwa.
Ainahin babban kamfanin Meta Networks, ya ce yawan masu amfani da shafin a kullum ya ragu zuwa 1.929bn a cikin wata uku zuwa karshen watan Disamba, idan aka kwatanta da da yawan da yake da shi na 1.930bn a watanni uku na baya.
Kamfanin ya kuma yi gargadin samun raguwar kudinsa saboda hamayya da yake fuskanta daga sauran shafuka irin su TikTok da YouTube, yayin da masu tallata kayansu a shafin suma suke rage kudin da suke kashewa.
Darajar hannun jarin kamfanin na Meta ta ragu da sama da kashi 20 cikin dari a cinikayyar 'yan sa'o'i a kasuwar New York.
Faduwar darajar ta haifar da asarar kusan dala biliyan 200 (£147.5bn).
Haka kuma darajar hannun jarin sauran shafukan sada zumunta da muhawara da suka hada da Twitter da Snap da Pinterest, ita ta fadi sosai a kasuwar.
Shugaban kamafanin na Facebook ya ce cinikin da kamfanin yake yi ya ragu saboda masu amfani da shafin musamman ma matasa sun koma wasu shafukan, abokan gogayyar facebook din.
Kamfanin Meta, wanda ya mallaki kafar talla ta intanet mafi girma a duniya (Facebook) bayan Google, ya ce matsalar ba ta tsaya a nan ba, domin hatta dokar kare sirrin masu amfani da shafuka wadda kamfanin Apple ya yi ta shafe su.
Sauye-sauyen sun sa abu ne mai wuya ga kamfanonin kayayyaki su iya sa ido sosai tare da tantance tallansu a Facebook da Instagram, wanda kuma hakan zai sa kudin da kamfanin na Facebook ke samu ya ragu da dala biliyan 10 a wannan shekara, in ji babban jami'in kudi na kamfanin na Meta, Dave Wehner.
Jumullar kudaden da Meta ke samu wadanda yawanci daga tallace-tallace ne ta karu zuwa $33.67bn a cikin lokacin da ake magana, inda abin ya dan zarta hasashen da aka yi na kasuwa.
Haka kuma kamfanin ya yi hasashen samun kudin da ya kai tsakanin $27bn zuwa $29bn a wata uku na gaba, wanda hakan ya yi kasa da abin da masu hasashe suka ce zai samu.
Yayin da kamfanin ke zuba kudade domin bunkasa bangarensa na amfani da hotunan bidiyo domin gogayya da TikTok, wanda mallakin katafaren kamfanin fasaha na China ByteDance ne, kudin da kamfanin yake samu daga harkar bidiyon bai kai ainahin wanda yake samu ba a kafarsa ta Facebook da Instagram.
To amma duk da haka Mista Zuckerberg ya ce yana da kwarin guiwar cewa kudin da suke zubawa a fannin bidiyon kwalliya za ta biya kudin sabulu, kamar yadda a baya suka yi a fannin talla a wayoyin hannu da Instagram.
Sai dai shugaban ya yi waiwaye cewa a wancan lokacin kamfanin bai yi fama da gogayya da wasu manyan kamfanoni ko kafofi ba a tsare-tsarensa.
Ya ce jami'ansu sun dukufa suna aiki sosai kuma suna ganin amfanin hakan sosai, sai dai kuma shugaban na Facebook, ya ce, ''abin takaicin shi ne, abokin gogayyarmu TikTok yana da girma sosai kuma yana ci gaba da habaka da sauri.''
Meta na durkushewa?
Sharhi daga James Clayton
Facebook a kodayaushe kamfani ne da yake bunkasa.
A duk rukunin wata uku-uku na shekara yawan masu amfani da Facebook karuwa suke yi tun lokacin da aka kirkiro shi.
Amma duk da haka a 'yan shekarun da suka gabata, karuwar ta tsaya a Turai da Amurka. Sai dai yawan karuwar da ake samu kuma a sauran sassan duniya ta sa ba a ganin waccan matsalar.
A yanzu dai farin jinin Facebook ya ragu a wurin matasa. Kamar yadda kamfanin shafin da kansa ya bayyana cewa TikTok na dakusar da shi.
To amma akwai wasu dalilan kuma da masu zuba jari suka damu da su game da kamfanin na Meta.
facebook ya sauya sunansa zuwa Meta saboda yana son ya fadada tare da bunkasa abubuwan da yake yi, to amma wannan za a iya cewa fata ne kawai domin har yanzu bai kama hanya sosai ta zama abin da ce yana so ya zama ba.
Sai dai kawai dimbin kudade da yake ta zubawa na biliyoyin dala domin ya kai ga wannan buri nasa, ba don m komai ba sai don kawai Mark Zuckerberg yana ganin ana sha'awar hakan, saboda haka yake wannan kasada.
Ko a iya cewa watakila hanyar magance matsalar da Meta ke ciki a yanzu ta gasa, ita ce ya saye TikTok? To a nan hukumomin Amurka ba za su taba barin hakan ba saboda dokokin hana gogayya.
Kuma yanzu yawancin masu harkar fasaha da suka yi fice a Amurka, suna kallon Facebook a matsayin wani bataccen abu. Shakka babu ba wuri ne mai dadin aiki ba kamar yadda yake shekara goma baya ba.
Wannan ya sa abu ne mai wuya ga Facebook ya iya janyo hankalin kwararrun matasa masana fasaha su yi aiki da shi.
A takaice a iya cewa Meta yana da gagarumar matsala a gabansa, halin da yake ciki a yanzu ka iya kasancewa masomi ne kawai.