Covid 19: Dalilin da ya sa ake ci gaba da nuna damuwa kan Omicron

Binciken farko da aka wallafa a Birtaniya da Afrika ta Kudu ya nuna cewa yawan wadanda suka harbu da sabon nauin cutar korona na Omicron ba sa matsanancin lafiya

Shaidar farko ta nuna cewa mutane kalilan ne ke butar a kwantar da su a asibiti domin samun kulawa idan aka kwatanta da sauran nau'ikan korona inda an yi kiyasin samun raguwar daga kashi 70 zuwa 30

Sai dai duk da cewa Omicron ba ya haifar da matsanancin rashin lafiya amma ana nuna damuwa a kan yawan wadanda suka harbu da cutar zai iya fin karfin asibitoci.

Mutum sama da dubu dari suka harbu da cutar a Birtaniya a cikin kwana daya a karon farko .

Sai dai idan aka fahimci tasirin cutar kan marasa lafiya wannan zai taimaka wa kasashen duniya wajan sanin irin matakin da za su dauka.

Haka kuma wani binciken da aka yi a kasar Afrika ta kudu shi ma ya nuna cewa sabon nauin cutar korona ba ya haifar da matsanancin rashin lafiya.

Binciken ya nuna cewa mutane kalilan ne za su bukaci a yi mu su jinya a asibiti.

Sai dai ana ganin raguwar da aka samu a yawan masu matsanancin rashin lafiya na da alaka da yadda aka samu wasu da garkuwar jinkinsu ta inganta sakamakon alurar rigakafi da kuma wadanda suka warke daga cutar.

Wani binciken da kwalejin Imperial ta yi ya nuna cewa nau'in Omicron na sauyawa abinda kuma ya sa ba ya illa kamar Delta

Farfesa Neil Ferguson , daya daga cikin masu binciken ya ce " wannan labari ne mai dadin ji zuwa wani mataki".

Sai dai ya yi gargadin cewa raguwar da aka samu ba ta kai matakin da za sa a samu sauyi a tsarin ba kuma yadda nau'in Omicron ke yaduwa cikin sauri na nufin cewa za a iya samun karuwa a yawan marasa lafiya da za a kwantar a asibiti.

Farfesa Peter Openshaw likitan gakuwar jiki a kwalejin Imperial wanda baya cikin mawallafan rahoton ya ce alamun farko sun nuna cewa nauin cutar korona na Omicron ba shi da lahani amma ya ki amincewa da binciken da ya nuna cewa Omicron ya koma zuwa cutar mura.